Dokokin Suturar Musulma

0
674

Amana ce akan miji duk suturar da zai yi wa matarsa ta zama daga halaliyar abin da yake da shi. Sannan kuma kada ya kuskura yayiwa matarsa sutura data sha bamban da wadda musulunci ya yarda musulma tasa.

Don haka:
(1) Haramun ne miji ya sayowa matarsa koya dinkawa mata irin kayan kafirai:

An karbo daga Abdullahi ɗan Amru ɗan Ass ya ce, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) ya ganni sanye da wasu kaya biyu masu ruwan ɗorawa, sai yace: “Haƙiƙa, waɗannan kayan suna daga cikin irin kayan kafirai, kada ka ƙara sasu”. (Muslim da Nasa’i da Hakim da wasunsu ne suka rawaito shi).
Kuma Abu Dawud ya rawaito hadisi da aka karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya yarda shi) yace, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yace: “Wanda ya kwaikwayi wasu mutane ya zama ɗan cikinsu”.

(2) Haramun ne miji ya sayowa koya ɗinka wa matarsa kayan maza:

Saboda hadisin da Abu Dawud da wasunsu suka rawaito cewa, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) ya tsinewa mutumin da yake sa kayan mata, haka kuma ya tsinewa matar da take sa kayan maza.

(3) Baya halatta miji ya sayawa ko ya ɗinkawa matarsa kayan neman suna, saboda Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yace:

“Wanda ya sanya kayan shuhura (neman suna) a duniya, Allah zai sanya masa tufafin ƙasƙanci ranar alkiyama, sannan kuma Allah ya balbala shi a wuta”. (Abu Dawud ne ya rawaito shi daga Abdullahi ɗan Umar( Allah ya yarda dasu).
Tufar neman suna, ita ce tufar da aka yi ta domin yin fice da kuma son zama daban cikin mutane, imma dai ta zama mafi wulaƙantar tufa da in aka sata za a jawo hankalin mutane, ko dai da sunan gudun duniya, ko son yin daban da sauran mutane.

(4) Haramun ne miji yabawa matarsa damar sa matsattsun tufafi masu kama jikinta, su kuma siffatashi, ballantana kumashi ya sayo mata matsattsun ko ya ɗinka mata su:

Saboda hadisin da aka karɓo daga Usamatu ɗan zaid (Allah ya yarda da shi) cewa, Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yana tsoron mace ta sanya tufar da zata riƙa siffata kasusuwan jikinta. (Diya’ul Maksidi ne ya rawaito shi).

(5) Sannan dai kuma bai halatta miji ya sayawa matarsa suturar da take shara-shara ba, saboda faɗar Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) cewa:

“A ƙarshen Al’umma ta za a samu wasu mata da zasu zama sanye da tufa, amma kuma suna tsirara, kansu kuwa kamar tozon rakumi (In kun gansu ) ku tsine musu, tsinannu ne su”. A wani hadisin ya ƙara da cewa: Baza su shiga Aljanna ba, kuma baza suji ƙanshinta ba, ga shi kuwa haƙiƙa ana iya jiyo ƙanshinta daga tafiya mai nisan kaza da kaza”. (wato mai nisan gaske ). (Ɗabarani ne ya rawaito shi).

(6) Lallai ne miji ya tabbatar cewa, suturar da zai yiwa matarsa, ta zama wadda zata rufe mata baki ɗayan jikinta.

(e) Bata Izinin Fita Yayin Buƙata:

Yana daga cikin haƙƙoƙin da mace take da su akan miji, yaba ta izinin fita domin zuwa ta biya buƙatar data same ta, wadda bata saɓawa shari’a ba, kamar zuwa gaisuwar mutuwa, ko duba mara lafiya, ko jajantawa wani Musulmi da wata musiba data same shi, ko sada zumuntar ‘yan’uwa da dai sauransu.
Bukhari da Muslim da wasunsu ne suka rawaito shi daga Aisha (Allah ya yarda da ita) wanda a cikinsa Annabi (tsira da amincin Allah sutabbata agare shi) Yace: “Allah yabawa mata damar fita domin biyan buƙatunsu”. Amma fa kuma lallai ne miji ya kula wajen ganin matarsa tabi ƙa’idojin da Musulunci ya shimfiɗawa mata; a yayin fita unguwa, kamar rashin cin ado da sanya turare, bin gefen hanya, rashin ɗaga murya da shewa akan hanya, da dai sauran su.
An karɓo daga Abi Masal Ash’ari (Allah ya yarda da shi) yace, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yace: “Duk matar da ta sa turare ta kuma gifta wasu mutane domin suji ƙanshinta, to ita karuwa ce”. (Nisa’I da wasunsu ne suka rawaito shi).
Sannan kuma baya halatta mabayyaniyar suturar mace ta zama mai ado caɓa-caɓa, a yayin da zata fita unguwa, saboda faɗar Allah Maɗaukaki: “Ku mata ku tabbata cikin ɗakunanku, (ko gidajenku) kada ku bayyanar da adonku irin bayyanar da ado (lokacin maguzancin farko)”.
Kuma Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yace da Umaimatu ‘yar Ruƙaika a lokacin data yi caffar karɓar Musulunci: “Zan yi caffa dake akan… ba zaki bayyanar da adonki ba, irin bayyanar da adon (lokacin) maguzancin farko”. (Ɗabarani ne ya rawaito shi daga Abdullahi ɗan Abbas Allah ya yarda da shi).
Bayan haka kuma, bai kamata mace ta riƙa tashin hankalin kanta dana mijinta ba, a daliln ta nemi izinin fita a wajensa bai barta ba, a nan haƙuri shi ne mafi dacewar abin daya kamata mace tayi, sannan kuma ta tuna faɗar Allah Maɗaukaki: “Ba komai da kuke so kuke samu ba, sai Allah ya so”.

(f) Adalci, a zamantakewar miji da matarsa:

Adalci, shi ne yin abu bisa cancanta da kamala.
Haƙƙin mace ne akan miji ya riƙa yin hulɗa da ita bisa cancanta da kamala, a cikin maganganunsa da ayyukansa, kamar irin yadda yake son matarsa ta yi hulɗa da shi bisa cancanta da kamala (wato ya zauna da ita batare da ya nuna sakaci ko zalunci ba, musamman idan mai auren fiye da mace ɗaya ne).
An karbo daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Ass, Allah ya yarda da su yace: Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yace: “Dukkan wanda ke son a nesanta shi daga wuta, kuma a shigar da shi Aljanna, sannan mutuwarsa tazo masa yana mai ba da gaskiya da Allah da ranar lahira, to ya rinƙa yiwa mutane irin abin da yake so suyi masa”. (Muslim ne ya rawaito shi).
Kuma an karɓo daga Aisha (Allah ya yarda da ita) tace: “Manzon Allah (tsira da Amincin Allah su tabbata agare shi) ya kasance baya fifita wasunmu akan wasu wajen raba mana kwana da zaman da yake yi a wajenmu….”. (Abu Dawud ne ya rawaito shi).
Sai dai shari’ar Musulunci ta shar’antawa mutumin daya ƙara aure, yayi sati ɗaya (kwana bakwai) tare da amaryarsa idan budurwa ce, idan kuma bazawara ce, ya kwana uku a wajenta, bayan haka, sai ya raba musu kwana daidai wa daidai, ba tare da wani fifiko ba.
Anas, sahabin Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) Allah ya yarda da shi yace: “Yin hakan shi ne koyarwar Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi).Amma fa raba musu kwana baya hana miji wasa ko zantawa da wadda ba ranar kwananta ba, ko shiga dakinta, matuƙar dai ba zai sadu da ita ba. Domin kuwa Aisha (Allah ya yarda da ita) tace: “Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) ya kasance yana shiga wajena a ranar kwanan wata, sai yayi abinda yaso dani sai dai ban da jima’i. Duba littafin Irwa’ul Galil na Malam Muhammad Nasiruddin (7/87).
Sannan kuma idan tafiya ta sami mai auren fiye da mace ɗaya yana iya yin ƙuri’a a tsakaninsu don warar wadda zai yi tafiyar da ita. Kamar yadda Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yake yi a tsakanin matansa.
Imamul Bukhari da Muslim sun rawaici hadisi da aka karɓo daga Aisha (Allah ya yarda da ita) tace: “Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) ya kasance idan zai yi tafiya yana yin ƙuri’a a tsakanin matansa wadda kuri’arta ta fito, sai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) ya tafi da ita”.
Waɗannan abubuwa da muka ji, su ne tsarin da Musulunci ya buƙaci magidanta su bi shi a gudanar da zamantakewarsu da matansu.
Idan kuwa abu ya zama ya fita daga cikin ikon mazaje, to ba a ce su ɗorawa kansu yin abin da ba zasu iya yin saba, sannan kuma ba daidai bane, a zarge su da rashin yin adalci, akan abin da aka san cewa basu da iko a kansa.
Bisa ga misali, shari’ar Musulunci bata ɗorawa miji daidaita son da yake yiwa matansa a cikin zuciyarsa ba, saboda sanin cewa yin hakan wani abune da ya fita daga ƙarƙashin ikonsa. Don haka Allah Maɗaukaki yace: “Bazaku iya yin adalci (na soyayya) ba a tsakanin mata, ko da kuwa kuna kwaɗayin yin haka. Saboda haka, kada ku karkata dukkan karkata, har ku bar ta kamar wadda aka rataye”.
Sai dai ako yaushe abin da ba a so, bayyanar da karkatar zuciyar a fili, ta yadda har za a iya fahimtar miji yana fifita matarsa wance akan wance, ko kuma wane yana yin biris da haƙƙoƙin matarsa wance, banda wance. Babu shakka yin hakan ne babba, tun bama ace miji ya mayar da ɗaya daga cikin matansa tamkar mara miji (wato bora) wanda a saboda girman wannan laifi, har sai da aka tanadar wa da mai yinsa azaba ranar lahira.
An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya yarda da shi) daga Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yace: “Wanda yake da mata biyu, sai ya karkata wajen ɗaya, to zai zo ranar alkiyama tsagin jikinsa a shanye” (Ahmad da Abu Dawud da Tirmizi da Nisa’I da Ibn Majah ne suka rawaito shi).

A nan nake cewa, wannan shi ne abin da ya sauwaka na haƙƙoƙin mace akan mijinta, saura kuma haƙƙoƙin miji akan matarsa.
Kamar yadda mace take da haƙƙoƙi na dole akan miji, to haka shima miji yake da haƙƙoƙi na dole akan matarsa.

Ga jerinsu kamar haka:

1. Biyayya.
2. Zaman gidan miji.
3. Ayyukan cikin gida.
4. Kula da abubuwa mallakar miji.
5. Hana wanin miji damar shiga gidan miji.
6. Neman izinin miji don yin Azumin nafila.
7. Neman izinin miji a lokacin buƙatar fita.
8. Godiya da yabawa miji.

Haƙƙin Biyayya:

Haƙƙin biyayya ga miji shi ne mafi girman haƙƙoƙin da miji yake da su akan matarsa, saboda faɗar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) cewa: “Da zan umarci wani yayi sujada ga wani (ba Allah ba), to dana umarci mace tayi sujjada ga mijinta (don biyayya gare shi). Tirmizi,Ibn Hibbana da wasunsu ne suka rawaito shi, kuma an karɓo shi daga ayarin sahabbai Allah ya yarda da su.
Don haka, yi- na-yi, bari-na-bari,dole ne akan mace a zamantakewar da mijinta.

Domin karanta cikakken bayani akan Abubuwan Da Suke Hana Mace Bin Mijinta Danna nan.

labarin da ya wuceAbubuwan Da Suke Hana Mace Bin Miji
Labarin na GabaJiga-jigan Magunguna