Idan aka ce sabulun wanki, an san ana nufin sabulun da ake amfani da shi wajen wanke tufafi, domin cire dauɗa, datti da wari da yake a jikin tufafi. Yana da kyau ya zama ingantacce, domin cire dauɗar da take a jiki kayan.
- A saka a rai cewa, akwai sabulai kaloli kuma iri daban-daban a kasuwanni, amma hadin nan da za a yi zai zama haɗi ne da za a iya shiga ko wani irin gasa ba tare da fargaba a rai ba.
- Wajen wannan haɗin a tabbata an yi amfani da turaren haɗin sabulu mai kamshi domin jan hankalin masu siya, turare mai daɗi sirri ne sosai wajen ɗaukar hankali.
- A yi amfani da Kala (colourant) mai kyau wajen haɗin, domin samun ingantaccen sabulu bayan an kamala hadin. Yin hakan zai taimaka wajen samun nasara a cikin abin da aka haɗa.
Na fara saka wannan gargaɗin ne domin a kula wajen haɗin da kokarin kare lafiyar kai, lafiya ita ce garkuwarmu, lafiya uwar jiki.
- A tabbatar an gane abin da yake a rubuce.
- Ya zama babu kuskure wajen awon kayan, ko adadin chemicals ɗin da za a yi amafani da su.
- Sannan a daidaita hadin chemicals ɗin a gwangwanayen su, domin samun abin da ake so.
- Abi shawarwarin koyarwar.
- Takunkumin hanci na da matukar amfani, domin gujewa shaƙar chemical ɗin da zai iya cutarwa.
- Takunkumin hannu wato (Rubber hand gloves) Shi ma yana da matukar amfani wajen haɗin kayayyakin chemicals din nan, domin gujewa afkuwar kuna a hanu ko a fata. Wasu chemicals din suna da matukar zafi a fata ko tafin hannu.
- Za a iya amfani da rigar Lab coat wato (laboratory coat) wajen haɗin domin gujewa fallatsar chemicals ɗin a kaya.
- Kar a taɓa gangancin gwada chemicals ɗin da hannu, ba tare da saka safar hannu ta rubber ba, yin hakan na da matuƙar hatsari.
- A yi nesa da ido wajen wannan haɗin domin kare lafiyar ido.
- A tabbatar ko wani kayan haɗin nan yana da ma’ajiya ta musamman domin yara, kuma da zarar an gama amfani da su, a mayar da su ma’ajiyar su a ɓoye.
- A karshe a tanadi (First-aid box) domin taimakon gaggawa a lokacin da abin da ba a fata ya afku wato fallatsar chemical mai zafi a fata, ko idan ya fallatsa a cikin baki a rashin sani. Domin haka sai a yi gaggawar wanke wajen da ruwan sanyi, idan kuma a baki ne sai anyi gaggawar kuskure baki, sannan a sha ruwan sanyi ko manja. Idan ba a samu sauƙin sa ba, sai a tuntubi likita.
- Ba za a taɓa cin arzikin wannan sana’ar ba, idan ba a jarraba ta ba. Mashinan, karafe / gwangwanayen aikin da sinaran haɗin duka suna da saukin samu. A fara jarrabawa da abin da ya sauwaka, babu shakka za a yi murmushi a gaba da ikon Allah(S.W.A). Kar a taɓa cewa sai an tara kuɗi da yawa za a yi sana’a.
- Hadin kayan nan yana tafiya ne wajen jarrabawa a koda yaushe, yin hakan ne kawai zai taimaka a ƙware.
- Kar a taɓa karaya ko a ji tsoro cewa, akwai ƙwararrun masu haɗin, su ma da sannu suka kai matsayin da suke.
- A sani kuma a saka a zuciya cewan kowane mutum da irin arzikin kasuwancinsa.
- Idan an gamsu da shawarata to, a fara jarraba wannan sana’ar a yau. A gaba ba iya ribar iya sana’ar za a ci ba, harda ribar koyawa wasu.
- Ina muku fatan Alkhairi.
Abubuwan Da Ake Bukata:
Sinadarai Adadi
- Caustic soda (Na OH) 1 kg
- Palm Kennel Oil ( P.K.O ) 6 Liters
- Soda ash ( light ) 0.25 kg
- Silicate 0.25 kg
- Sodium sulphate 3 kg
- kala Yadda ake so
- Ruwa 4.5 liters
- Turaren hadi Adadin da ake so
- Sinadarin kumfa 250 mls
Yadda Ake Hadawa:
A hade Caustic-soda din ta hanyar narkar da 1kg Caustic-soda a cikin 4.5 liters na ruwa. A tabbatar da cewa nauyin sa ya kai 1275kg/m3. A bar hadin ya kwana uku domin ya narke da kyau. A tabbatar ya yi wannan kwanakin domin samun nagartarsa, kuma domin gujewa samun matsala a fata ko a kan kaya.
- A zuba soda-ash ɗin a cikin wannan caustic soda ɗin da aka dama, aka bar shi ya yi kwanaki, sannan a yi ta motsa damun har sai ya yi yadda ake so, wato ya damu da kyau.
- sai ɗauko wannan Kalar ( colorant ) shi ma a zuba a cikin haɗin a ci gaba da damawa.
- Sannan kuma a ɗauko duka ( P.K.O ) wato Palm kennel oil a juye a cikin haɗin a juya ko na ce damawa ta tare da an mayar da hannu baya ba, kar a yi gaba ai baya nake nufi.
- Da kuma foaming agent wato ( sinadarin saka kumfa ) tare da Silicate a zuba su a ciki a ci gaba da motsawa.
- A ɗauko sinadarin kamshi wato turaren hadin sabulun, a zuba a cikin hadin. Sannan a zuba shi a cikin gwangwanayen sabulan,sai a bar shi na tsawan awa 24 ( 24hrs ) domin ya hade ya yi karfi.
- Bayan awa24 ( 24hrs ) nan kuma sai a yi tambari a kai, a yi masa fasali irin yadda ake so, sannan a yi pakajin su. Daga nan kuma sabulu ya kammala.
Domin Sanin yadda ake sabulun wanka danna koren rubutun nan