Abubuwan da ake buƙata
- Fulawa
- Yis
- Kantu/riɗi
- Sikari
- Gishiri
Yadda ake haɗawa
- A sami fulawa a tankaɗe a zuba mata yis, sai a zuba ruwa a kwaɓa,
- Kada a kwaɓa ta yi ruwa, a kwaɓa ta da ɗan tauri.
- Idan ana son Gurasa mai sikari, sai a zuba sikari a cikin kwaɓin , idan kuma mai gishiri ce, sai a zuba gishiri a cikin kwaɓin.
- Idan lokacin zafi ne za ta yi saurin tashi saboda dama yis zafi yake so, awa uku zuwa huɗu ya ishe shi ya tashi.
- Amma idan lokacin sanyi ne yakan daɗe bai tashi ba. Idan ana so a yi gurasa da safe, to sai a kwaɓa fulawar tun da daddare,
- Idan an tabbatar kwaɓin ya tashi , sai a zuba karare a cikin tanderu, a kunna wuta domin tanderun ya yi zafi.
- Idan an tabbatar tanderun ya yi zafi sosai kuma karan ya cinye sai a yayyafa ruwan kanwa a ciki.
- A saka tsintsiya a share toka-tokar da ta maƙale a cikin tanderun.
- Sai a kawo kwaɓin a cura shi ya yi faɗi, a faɗaɗa da hannu, yadda dai a ke son faɗinta ya kasance.
- Idan kina son kantu/riɗi sai a zuba ɗan kaɗan a kan gurasar a tsakiya, idan kuma ba a so shi kenan sai kawai a saka curin da a ka yi a cikin tanderun.
- Idan an gama sakawa sai a kawo tire a rufe tanderun, takan ɗau kamar minti ashirin zuwa minti ashirn da biyar kafin ta yi.
- Ba ma sai an kalli agogo ba, da ta yi za a ji ƙamshi ya turare ko ina a gidan.
- Sai a kawo wuƙa da tire, a ringa saka wuƙa ana ɓamɓaro ta tana faɗawa kan tiren. Amma sai an yi a hankali saboda zafi kada a ƙone domin tanderu yana da zafi sosai.
Domin karanta Yadda Ake Faten Wake Da Doya danna nan
Edita:@rumasau-kallamu