Yadda Ake Pancake

pancake

A yau za mu koyi yadda ake Pancake

Abubuwan da ake buƙata

flour kofi ɗaya
•Sugar cokali 2
•Baking powder babban 1
•Ƙwai ɗaya
•Madara ta ruwa ɗaya (ko ta gari ne za a iya saka 2-3 table spoon a dama da ruwa cikin gwangwanin madara ƙarami)
•Butter/oil
•Gishiri kaɗan

  1. Yadda ake haɗawa
    Cikin kwano mai faɗi, a haɗa tankaɗaɗɗen flour, sugar, bakin powder da gishiri.
  2. A fasa ƙwai cikin madara da cokali ɗaya na mai, a kaɗa a juye cikin flour, sai a dama shi.
  3. Idan ya yi ruwa sosai, sai a ƙara flour kaɗan, ana son kwaɓin ya fi na wainar fulawa/kalallaɓa kauri kaɗan.
  4. A saka cokali ɗaya na bota, a frying pan, in ya yi zafi, sai a ɗebe kwaɓin daidai misali a zuba, a yi faɗi da shi, kamar za a soya ƙwai, idan ya yi, sai a juya ɗayan ɓangaren.
  5. Haka za a yi ta ɗiba har ya ƙare.

Domin sannin yadda ake danbun nama danna nan