Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana Ɗankucaka ya fita kiwon ragonsa a bayan gari. Ya yi wa rago talala don kada ya shiga gonakin mutane ya yi ɓarna. Bayan la’asar sai ya koma ya kunce ragon, ya hau ya kama tafiya. Da ya isa kusa da gidan Kura, sai rago ya yi kuka. Da Kura ta ji kukan rago sai ta fito da gudu ta kira Ɗankucaka. Da ya je sai tace: “Yaya sunanka ne?” To daman kuwa Ɗankucaka wani hatsabibin yaro ne.
Wasu ma kan yi masa ganin aljani. Sai ya ce da Kura: “Sunana Ɗankucaka.” Kura ta tambaye shi: “To, Ragon na sayarwa ne?” Sai Ɗankucaka ya ce: “E, na sayarwa ne.” Sai Kura ta ce: “Nawa ne kuɗinsa?” Sai Ɗankucaka ya ce: “Ba da kuɗi za a saya ba; sai dai a yi kokowar kwana bakwai.
Kuma kokowar a kan dutse nake yinta.” Jin haka sai Kura ta yi dariya ta ce: “Mutanen ƙwarai ma ba su ce za su yi kokowa ba, sai kai Ɗankucaka!” Tana gama faɗin haka sai kawai ta kama Rago ta kashe, ta ɗauki gangar jikinsa ta kai gida suka sha gara ita da ’ya’yanta.
Washe-gari sai Ɗankucaka ya je wurin Kura suka tafi kokowa. Suka kama kokowa; can Kura ta kayar da Ɗankucaka. Lokacin da za su rabu kowa ya tafi gida, sai Kura ta ce: “Banda wawa, maimakon ka karɓi kuɗi sai ka zaɓi duka?” Ɗankucaka dai bai ce da ita uffan ba. Washe-gari ya sami Kura suka tafi dutsen da suke yin kokowa.
Gaga-gaga, Kura ta sake kada Ɗankucaka. Da za su rabu kowa ya tafi gidansa sai Kura ta kalli Ɗankucaka ta ce: “Gara ka haƙura da kokowar nan haka, don za ka rasa ranka.” Ɗankucaka dai bai ce komai ba. A ranar kokowarsu ta ukun ma Kura ta kayar da shi. Amma a rana ta huɗu, sai Ɗankucaka ya ɗaga Kura ya doka ta a kan dutse.
Kayen kuwa ya kiɗima ta. Sai ta ce da shi: “Kai aboki menene haka?” Ɗankucaka ya ce mata: “A lokacin da kika ƙwala ni da ƙasa na yi magana ne?” Kura ta ce: “A a, a gaskiya ba ka yi magana ba.” Da Kura ta isa gida daga fagen kokowarta da Ɗankucaka, sai tace da ’ya’yanta: “Duk wanda ya zo nema na gobe ku ce na yi tafiya, ba zan dawo ba sai bayan kwana biyar.”
Washe-gari Ɗankucaka ya je gidan Kura domin ta fito su tafi kokowa. Ashe ta shiga rumbu ta ɓuya, amma ’ya’yanta suka ce tayi tafiya. Ɗankucaka ya ce: “Na ji ta yi tafiya; amma daman tace idan na zo in ɗauki rumbu in tafi da shi.” Sai ’ya’yan suka ce: “To, ɗauki mana.” Ba tare da ɓata lokaci ba, sai ya ɗauki rumbu.
Sa’adda ya je bakin ƙofa, sai ya yi wurgi da rumbun. Kura ta buge ƙugunta; ba ta san sanda ta ce: “Wayyo!! Mene ne haka aboki?” ba. Da Ɗankucaka ya ji haka sai ya ce: “Na gaji ne saboda nauyinki; ina hutawa ne. Ashe kina nan, kika ƙi fitowa mu je kokowa?” Tun da an gane, kan dole ta yarda suka je fagen kokowar.
Da suka kama kokowa kici-kici, sai ya ɗaga Kura sama, ya yi juyi da ita, sannan ya maka ta a kan doron dutsen nan. Kayen ya kai kaye, kuma jikinta ya yi tsami fiye da kullum. A rana ta shida sai Kura ta ɓuya a cikin zana. Da Ɗankucaka ya biya mata domin su tafi fagen fama, sai ya ce ya je ne ya ɗauki zana.
Ba tare da wani musu ba ’ya’yan Kura suka ba shi zanar da uwarsu ta maƙe a ciki. Da ta lura ya je bakin ƙofa, sai ta ji tsoron kada ya yi jifa da ita. Sai tace: “Abokina daure ka ajiye ni a hankali, kada ka yi jifa da ni irin na jiya.”Da Ɗankucaka ya ji maganarta sai ya ce: “Ashe kina nan?” Ba su zame ba sai a wurin kokowarsu.
Ɗankucaka ya sake yi wa Kura mummunan kayen da bai taɓa yi mata kamarsa ba; duk kanta ya farfashe. Da ta isa gida, sai ta gudu daga gidanta, ta tafi gidan kawunta. Tana isa sai ta tarar da ɗan kawunta mai suna Goshi. Ta tambaye shi: “Goshi, ina babanka?” Sai yaron ya ce: “Babana yana nan, amma kin san ba a tashinsa daga barci sai da wani babban dalili, kuma idan ana son ya tashi sai an nemi zugazugai an sa a ƙarƙashinsa, an haɗa wuta kamar ta maƙera.
Zafin wannan wuta ne zai tayar da shi.” Yana gama yi mata bayani ta ce: “Goshi, abin da ya kawo ni fa babban abu ne.” Goshi ya dubi Kura ya ce: “Wane abu ne kuwa wannan?” Sai Kura ta gaya masa yadda suka yi da Ɗankucaka, kuma ta nuna masa kanta, duk ta ji ciwo. Sai Goshi ya ce: “Ai idan dai wannan ne, ai ko ni zan yi miki maganinsa.”
Shiga gida a shafa miki magani.” Goshi ya koma bakin ƙofa ya zauna, yana jiran ya ga wanda zai zo. Washe-gari Ɗankucaka ya je gidan Kura, ya tambayi ’ya’yanta inda take; suka ce masa ta yi tafiya. Sai ya fita ya fara bin sawun Kura, har sawunta ya kai shi gidan kawunta.
Da ya isa, sai ya tarar da Goshi a kofar gida. Sai ya tambaye shi: “Kura tana nan ne?” Goshi ya sanar da shi Kura tana nan, kuma ya tambaye shi: “Me ya faru ne?” Ɗankucaka ya ce masa: “Ina son ta zo mu je mu ƙarasa kokowarmu ne.” Ba tare da tunani ba, Goshi ya ce: “Na sayi kokowar. Mu je ka yi da ni.”
Sai Ɗankucaka ya ce: “A kan dutse muke yi fa.” A cikin fushi Goshi ya ce da Ɗankucaka: “Ko a kan ƙarfe ne na karɓa.” Suka tafi. Da fara kokowa Ɗankucaka ya Ɗaga Goshi ya danƙara da ƙasa. Goshi ya ji zafin kayen nan ƙwarai. Shi ma ya zabura, ya ɗaga
Ɗankucaka, ya maka shi da ƙasa kan dutsen nan. Kayen ya razana Ɗankucaka.
To amma sai suka ci gaba da fafatawa. Can Ɗankucaka ya sake kayar da Goshi. Da ya ga Goshi a ƙasa, sai yace: “Dutse buɗe.” Dutse ya tsage, Goshi ya faɗa ciki.” Goshi ya yi wa dutse magana, wani hayaƙi ya turnuƙe, sai ga Goshi ya fito. Suka sake kama kokowa. Da Goshi ya yi wani gwauron numfashi, ya cicciɓi Ɗankucaka, ya yi sama da shi ya maka shi da ƙasa a kan dutsen nan, bai ko shura ba ya mutu.
Goshi ya ɗauki Ɗankucaka ya je gida, ya feɗe shi, ya dafa suka cinye namansa, amma ya shanya fatarsa. Ba a ba Kura naman Ɗankucaka ba, saboda yaminsa ya fi nata ƙarfi. Bayan ’yan kwanaki sai kitsen fatar Ɗankucaka da ke rataye ya fara narkewa yana ɗiga ƙasa.
Aka gaya wa Kura duk kwaɗayin da zai kama ta, kada ta kuskura ta taɓa fatar. Kwanci-tashi, wata rana Kura ta zo wucewa sai ta ga mai yana ɗiga daga jikin fatar nan, sai ta ce: “Ga daɗi, amma an ce kada in ci. Amma bari in taɓa kaɗan.” Sai ta sa harshe ta lashi man. Nan da nan wasu dogayen farata masu kaifi da tsini suka bayyana a jikin fatar, suka datse harshen Kura.
Zafi ya kama ta. Sai ta ƙwala ihu. Da Goshi ya ji haka, sai ya fito ya ce: “Me ya faru?” Sai ta ce: “Fatar nan ce ta yi farata, ta kama ni za ta kashe.”Da ya ji haka sai ya gane Kura dai ta taɓa man da ke ɗiga ne. Daga baya sai Goshi ya ɗinka jaka da fatar Ɗankucaka.
Wata rana zai fita farauta sai ya ba Kura jakar ta rataya domin ta raka shi. Suna cikin tafiya sai jaka ta yi farata. Faratan suka kama Kura. Sai ta ƙwala ihu. Sai Goshi ya karɓi abinsa ya riƙe, suka shiga daji. A cikin dajin, sai Goshi ya ce: “Wuta, wuta daji!” Daji ya kama da wuta.
Ɓeraye da gafiyoyi da sauran ƙananan dabbobi suka fito. Sai Goshi ya dube su ya ce: “Duk ku gasu.” Nan da nan suka gasu. Ya ce: “Tuwo fito.” Sai ga tuwo masaki-masaki. Sai Goshi ya ce da Kura: “Fara ci.” Kura ta ce: “A a, kai dai fara. Ai kai ne babba.”
Sai Goshi ya fara cin naman nan da tuwo. Kafin a ƙifta idanu, ya cinye komai. Mamaki ya kama Kura.
Sai ta tambaye shi: “Yaya ka cinye duka ba ka rage mini ba?” Sai ya ce: “Ai ke ce ba ki yi magana ba.” Daga ƙarshe dai haka suka kama hanyar gida. Shi a ƙoshe, Kura na jin yunwa. A kan hanya ne suka je bakin wani rafi. Sai Goshi ya dubi ruwan ya ce: “Kifaye ku zo ku taru in kama.” Nan take kifaye suka taru.
Ya ba Kura dama ta kwashi kifaye ta ci. Ta ƙi, wai shi ne babba. Shi kuwa sai ya kama kifayen ya cinye su baki ɗaya, ko ƙaya bai bari ba. Haka suka ci gaba da tafiya. Sannu a hankali suka isa daidai wata kuka mai ’ya’ya da yawa, amma ba abin kaɗo su. Sai Goshi ya ce da Kura ta ba shi cinyarta ɗaya ya kaɗo ’ya’yan kukar da ita.
Tun kafin ta yi magana sai ya fizge mata cinya ɗaya, ya jefa, ’ya’yan kuka suka zubo birjik. Ya sha kukar nan ta yi masa karo. Ya ɗauki cinyar Kura ya maƙala mata, ta zauna kamar ba a taɓa cire ta ba. Mamaki da tsoro suka rufe Kura. Da haka dai suka isa gida. Washe-gari sai Kura ta je ta sami abokinta Kurege, ta ce da shi: “Yau za mu je farauta, amma kar ka ɗauki gayan tuwo.”
Amma Kurege da wayonsa ya ɗauki gayan tuwo ya jefa a jakarsa. Sai Kura ta ce kar ya ɗauki fartanya. Amma sai Kurege yasa ƙaramin magirbi a cikin jakarsa. Ta ce ko dutsen hura wuta kada ya ɗauka. Amma duk abin da ta ce kada ya aikata, sai da ya yi. Suna isa daji Kura ta ce: “Wuta, wuta daji. Daji bai kama da wuta ba. Da ta yi ta gaji, sai ta ce da Kurege, “Mene ne abin da za mu yi?”
Sai ya ce da ita: “Ko da yake kin hana in zo da dutsen wuta, na zo da wani da na gani a jakarki.” Ta yi murna. Suka yi ƙyastu da dutse, wuta ta tashi a daji. Kura ta ce da ɓeraye su fito, amma ko gashi ba su gani ba. Ta nemi shawarar Kurege. Shi kuwa ya tuna mata: “Ai kin ce kada in zo da magirbi.” Kura ta ce: “Je ka ɗauko mana.”
Don kada ya wahala, sai ya fito da wanda ke cikin jakarsa. Kura ta amsa, ta yi ta tonon ramukan ɓeraye, amma ba su samu da yawa ba. Ta ce da ɓeraye su gasu, amma ba abin da ya faru. Ta rasa yadda za ta yi. Amma sai Kurege ya taƙaita musu wahala, ya fito da dutsen ƙyastu, ya buga shi, wuta ta kama. Da haka dai har duk abubuwan da ta ce kada ya ɗauko daga gida suka yi amfani.
Ba tare da wata-wata ba, Kura ta kama nama da ci. Kurege dai bai ce komai ba. Amma idan ya faki idonta, sai ya ɗauki gasasshen ɓera ya jefa cikin jakarsa. Da haka ya tara abinda zai je gida da shi, ko da yake ba ta bari ya ci ba. Duka abubuwan da Goshi ya yi sanda ya fita farauta da Kura, sai da ta yi irinsu tare da Kurege. Amma shi yana fakar idonta ya ɓoye irin abubuwan da ta riƙa ci tana hana shi, har suka isa bishiyar kuka.
Da suka je bishiyar kuka, sai Kura ta ce wa Kurege: “Ka kwanta in cire cinyarka in jeho mana kuka da ita.” Sai Kurege ya ce: “Haba Kura. Haka bai dace ba.” Sai Kura ta fusata ta ce: “Ka yarda da abin da na ce, in ka ƙi kuwa in kashe ka, in ciri cinyar in yi abin da nake so da ita.” A kan dole Kurege ya kwanta, ta tuge cinyarsa, ta jefi kuka da ita.
Sai cinyar ta maƙale. Da Kurege ya ga haka sai ya fara ƙaraji, yana hargowa. Can dai ya yi sa’a, iska ta kaɗa cinyar ta faɗo. Kura ta ɗauko cinya wai za ta maƙala wa Kurege. Idan ta sa nan, sai ta ƙi zama, ta ce ta yi yawa ne. Sai ta riƙa cin naman cinyar da nufin rage mata girma, domin ta yi daidai.
Da haka har cinyar tarage saura kaɗan; sai ga Goshi. Kukan Kurege ne ya jawo shi. Sai
ya tambayi abin da ya sa Kurege kuka. Kurege ya yi masa bayani. Goshi ya tambayi Kura nata bayanin. Kura ta ce Kurege ya faɗi gaskiya. Sai Goshi ya yi wuf ya cafke Kura, ya kashe ya cinye. Daga nan kuma ya nemo wata cinya ya maƙala wa Kurege, ta zauna. Da
aka sa wa Kurege cinya, sai ya tashi, ya ruga a guje bai sake komowa kusa da inda ya saba haɗuwa da Kura ba. Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Kwaɗayi mabuɗin wahala.
- Azzalumi a ƙarshensa jin kunya ko wahala.
- Kura dirungu sha duka.
- Kowa ya daka rawar wani, zai rasa turmin daka tasa.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Edita@rumasau-kallamu









