Ga ta nan, ga ta nanku.
Wani mutum ne yana zaune da matarsa a cikin talauci a wani ɗan ƙauye, babu cin yau balle na gobe. Wata rana sai ya je gona ya ga wata busasshiyar bishiya, ya hau ya fara sara da gatarinsa domin neman abin zaman gari. To akwai wani dutse mai kogo kusa da gonar.
Sai kwatsam, ga wasu mutane su goma sha biyu riƙe da kwari da baka sun fito daga ciki. Da fitowarsu sai suka zauna suka ci abinci, suka tafi. Amma kafin su bar wurin sai da suka faɗi wani abu kamar haka: “Kalja sum sum, Kalja sum sum, Kalja sum sum.” Da faɗin haka sai mutumin ya ga ƙofar kogon dutsen ta rufe.
Sai dai ya ga kamar ɗaya daga cikinsu ya manta da wani abu sai yace: “Buɗe sum sum, Buɗe sum sum, Buɗe sum sum.” Sai ƙofar kogon ta buɗe, ya shiga ya ɗauko wata batta daga ciki; ya fita, suka kama hanyarsu. Bayan sun tafi, sai mutumin ya matsa kusa da dutsen domin ya kashe kwarkwatar idonsa.
To, tun da ya ji abin da suka faɗa, sai shi ma ya faɗa, ƙofar kogon kuma ta buɗe, sai ga ruwa. Ya sake cewa: “Kalja sum sum,” wata ƙofar ta buɗe, sai ga wuta. Bai fasa ba dai, ya sake faɗa, wata ƙofar ta buɗe, amma a wannan wuri sai kawai ya ga ƙyalƙyali irin na zinariya. Ga kuma tarin zinariyar mai ɗinbin yawa, abin gwanin ban mamaki, har ma da tsoro.
Can gefe kuma tarin azurfa ne kamar ba iyaka, ga kuma kuɗi a wani ɓangaren kamar duk kuɗin duniya baki ɗaya aka tara a can saboda yawansu. Mutumin nan ya shiga ya ɗebi dukiya iya yadda zai iya ɗauka, ya ɗora a ka, yana riƙe da gatarinsa ya kama hanyar gida, amma fa duk sai da ya tabbata ya rufe duk ƙofofin kogon nan da ya buɗe.
Yana isa gida matarsa ta tarye shi da murna kamar dai yadda takan yi kullum idan ya je neman abinci ya dawo. Mutumin da gaggawa kuma a cikin murna ya nuna wa matarsa zinare da kuɗi da azurfar da ya samo. Matar kuma a guje ta je ta aro ma’auni a wajen maƙwabta suka auna zinaren.
Ba da saninsu ba ashe akwai ɗan guntun zinaren ya maƙale a ma’aunin da suka mayar masu. Masu ma’auni suka ajiye, har dare ya yi. Sai ga wani abu ya haske musu ɗaki, suka yi ta mamaki. Da gari ya waye suka shiga bincike, suka gano ashe zinare ne a jikin ma’auni da maƙwabta suka ara da maraice.
Daga nan suka aiki ɗayansu ya je ya tambayi mutumin inda ya samo zinariya. Ya dai matsawa mutumin sai ya nuna masa inda ya samo domin shi ma ya je ya ɗebo. A kan tilas mutumin nan ya tasa ƙeyarsa suka tafi. Da suka isa, sai mutumin ya gaya wa maƙwabcinsa abinda ake cewa ƙofofin kogon dutsen nan su buɗe.
Daga nan fa sai ya tafi gida abinsa. Maƙwabci ya faɗi abin da mutumin ya gaya masa, sai nan da nan ƙofofin suka buɗe. Sai ga dukiya, kamar ta fi wadda mutumin farko ya fara gani jiya. Maƙwabci ya lafci dukiya iyakar son ransa, to amma da ya zo fita sai ya rikice, ya rasa abinda zai faɗa ƙofar kogo ta buɗe.
Jim kaɗan sai mutanen nan goma sha biyu suka dawo daga inda suka je. Suka shiga kogon, sai kawai suka tarar da maƙwabci. Ganin ya kwashi dukiya ba tare da izininsu ba, sai suka kama shi suka yanka, suka ajiye gawarsa a gefe. Washe-gari da mutumin ya ji ana cewa maƙwabcinsa bai dawo gida ba, sai ya koma dajin nan, ya jira sai da mutanen nan suka fito suka tafi, ya je ya buɗe kogo, ya shiga.
Da shigarsa sai ya tarar da gawar maƙwabcinsa a gefe, mutanen nan sun yanka ta gunduwa-gunduwa. Ya tattara gaɓobin, ya zuba a mangala, ya kama hanyar gida. Sai ya ɗebi zinariya, ya je wurin shugaban dogarai ya ce da shi ɓarayi sun tare su, har suka kashe mishi ɗan’uwa, saboda haka ya ce masa: “Don Allah ga ladan zinariya nan ka sake haɗe min shi, domin a rufe shi a haɗe.”
Sarkin Dogarai ya haɗa mutum, amma tun kafin a ɗauke shi a tafi da shi wurin binnewa ra, sai mutanen kogo suka je gidan Mai Gari suka ce wani mutum ya sayi saniyarsu bai biya ba, amma ya mutu an kawo gawarsa gidan Sarkin Dogarai. Sarki ya bincika aka tabbatar da haka; aka kawo gawar, suka ce a ba su.
To, dama suna so a ba su gawar ne domin su cinye, Sarki ya hana. Yasa Sarkin Dogarai ya ba mutumin nan gawar maƙwabcinsa, aka binne ta bisa al’adar garinsu. Mutanen kogo suka haƙura, shi kuwa matalaucin nan da ya sami dukiya a dare ɗaya, ya yi ta cin
duniyarsa shi da matarsa. Amma kuma duk sanda ya ga matalauta yakan taimake su da kuɗi da abinci da jari domin su yi sana’a. Sai mutan ƙauyen suka sa masa suna Mai sa’a. Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Mahaƙurci mawadaci.
- Wanda ya daka rawar wani zai rasa turmin daka tasa.
- Kuɗi masu gidan rana.
- Duk wanda ya haƙura da kaɗan Allah zai wadata shi.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Jika Da Kaka
Edita@rumasau-kallamu









