Tatsuniyar Dogarawa Uku

0
3

Ga ta nan, ga ta nanku.

Wasu dogarawa ne dai su uku masu suna Gi da Ɗa da kuma Ɗo. Aikinsu shi ne gadin gidan Sarki. To, akwai wani mutum kuma a garin sunansa Giɗaɗo. Shi ke nan, Sarki kuma yana da kaji da yawa a gidansa. Wadannan dogarai kuma su Gi da Ɗa da Ɗo kullum suna zuwa kamun fari.

Idan sun zo da su sai su zuba wa kajin Sarki. In kajin sun ga farin, sai su zo suna ci. Su kuma dogaran sai su kama guda uku, kowa da tasa. Sai su je su gasa, su ci. To, kullum a ƙofar gidan Giɗaɗo suke gasawa. Shi ke nan, yau da gobe, sai Sarki ya ga kaji suna ƙarewa. Sai aka soma bincike; in aka tambayi wannan, sai ya kalli wancan.

In aka tambayi wancan, sai ya kalli wannan. Sai Sarki ya ce in ba su faɗa ba, za a kashe su. To, akwai wani Bafulani da kan kai wa Sarki nono kullum. To, in ya tashi zuwa sai su haɗu da Gi, da Ɗa da Ɗo. To, ba ya iya bambanta sunayensu. In ya tashi kiran su, sai ya ce: “Giɗaɗo.” Kullum in sun haɗu, sai ya ce: “Giɗaɗo, ina za ka je?”

Sai su ce ai Sarki ne ya aike su, su kai kaji wani gida. Kullum haka. Shi ke nan, ana cikin yi musu tambayoyi game da ɓacewar kajin Sarki, sai ga Bafulanin nan ya zo. Da ya ji zancen da ake yi, sai ya ce ai ya san waɗanda suka ci kajin. Sai aka ce to, ya faɗa. Sai ya ce: “Ai Giɗaɗo ne.” Sai Sarki ya ce: “Kai ɗan Fulani, ka faɗi gaskiya.

Giɗaɗo ba zai zo ya kama kaji a gidana ya ci ba.”Jin haka ya sa Bafulani ya ce: “Wallahi Giɗaɗo ne yakan ci kaza kullum. Idan ina zuwa kawo nono mukan haɗu yana riƙe da kaza. Kuma idan na ce ina za shi da kaza, sai ya ce Sarki ya aike shi.” Sai Sarki ya ce a je gidan Giɗaɗo.

Da aka isa ƙofar gidansa, sai aka tarar da gashin kaji ya cika ƙofar gidan, saboda kusa da gidansa dogarawan Sarki kan je su fige kajin da suka sato daga gidan Sarki. Sai aka ce to a shiga a kamo shi. Sai aka shiga gidansa, aka kamo shi. To, da aka tambaye shi bayani a kan kaji, sai ya ce shi bai sani ba, don shi bai isa cin kaza ba, balle ya je gidan Sarki da masu gadi, har ya kama kaza, ya gasa, ya ci.

Sai Sarki ya ce: “To, in ba kai ba ne, sai ka gaya min wanda zai zo ƙofar gidanka da kaza, ya yanka, ya fige, kuma ya gasa, ba ka sani ba.” Giɗaɗo ya ce sam-sam, shi bai sani ba, kuma bai san wanda ya ci kaza ba. Sai Sarki ya kasa gane gaskiyar al’amari. Sai dogarawa suka ce tun da a ƙofar gidansa aka ga gashin kajin, ai sai a kashe shi.

Sai Sarki ya ce to a kama shi a kashe. Sai Gi da Ɗa da Ɗo suka ingiza ƙeyarsa waje, suka je suka kashe shi. Da yake da man ba su da gidajen kawunansu, sai suka mamaye gidansa, watau sun ci nasara, har da gadonsa. Sarki bai san maciya kajinsa ba. Kurunƙus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Kuskure ne a zartar da hukunci ba tare da yin kyakkyawan bincike ba.
  • Maciyin amana komai daɗewa sai ya ga mummunan sakamako.
  • Ba a yin azzalimin sarki, sai bafade.
  • Wata shari’ar sai a lahira.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Danna nan don karanta Tatsuniyar Ɗantsintuwa

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Ɗantsintuwa
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.