Ga ta nan, ga ta nanku.
A can ƙasar Mazarƙwaila an yi wani yaro ɗan Sarkin Zaƙi, mai suna Nasiru. Yana da wani aboki wai shi Nisiru. Ana kiran baban Nasiru Sarkin Zaƙi ne, domin ya fi kowa yin kayan zaƙi a garinsu. Shi Nisiru yakan je ya sami Nasiru su tafi cin zuma, watau su ƙona itace hayaƙi ya kori ƙudan zuma, su kuma su kwaso saƙarta da ruwan.
Haka suke yi kullum. Ana nan, ana nan, sai mahaifiyar Nasiru ta rasu. Rasuwarta ke da wuya sai kishiyarta ta shiga ba Nasiru wuya. To amma ɗan kishiyar uwar mai suna Aliyu yana son Nasiru sosai; ba ya nuna masa ƙiyayya ko kaɗan. Wata rana sai Aliyu ya ce wa Nasiru da abokinsa: “Yau zan raka ku cin zuma.”
Da Nasiru ya ji haka sai ya ce da shi: “Ni fa ina tsoro kada mahaifiyarka ta yi faɗa.” Sai Aliyu ya ce: “Ba komai, ba za ta yi faɗa ba sam-sam.” Daga ƙarshe dai Nasiru ya haƙura, ya amince zai je da Aliyu. Lokacin da Nasiru da Aliyu suke wannan maganar, ashe wata mata magulmaciya ta ji su, sai ta je ta sami uwar Aliyu ta ce da ita: “Kin ga Nasiru da abokinsa Nisiru za su ja ɗanki daji su halaka shi.”
Uwar na jin haka sai ta ce da matar nan: “Yanzu yaya za mu yi?” Da ’yar zugar ta sami gangara, kawai sai ta ce: “Akwai wani hatsabibin boka wanda za mu je ya ba mu maganin da zai kashe Nasiru kawai mu huta.” Wannan shawara ta tsorata uwar Aliyu, sai ta ce: “A a, ni fa ina tsoron kashe mutum.”
Sai matar nan mai ingiza kantu ruwa ta ce: “Idan ba ki kashe yaron nan ba sai ya fi ɗanki arziki domin yana da ƙashin arziki.” Uwar Aliyu na jin wannan gurguwar shawara, sai ta ce: “To, shi ke nan mu je.” Uwar Aliyu da mai zuga ta suka je gidan boka suka yi masa bayani. Nan take kuwa ya kawo magani ya ba su, ya ce su zuba a nono.
Ya tabbatar musu idan Nasiru ya sha maganin to zai mutu. Suka dawo gida, uwar Aliyu ta dama fura da nonon da aka zuba wa magani, ta ajiye wa Nasiru ita a gindin randa, ta danta Aliyu kuma ta ɗora a kan randar. Nasiru da Aliyu suka shiga gida, aka nuna wa kowa furarsa.
Nasiru ya ɗauko tasa daga gindin randa zai fara sha, sai ya ga uwar Aliyu ta sa shi a gaba tana yi masa fara’a, har da wasa da dariya. Ganin haka ya sa shi shan jinin jikinsa. Sai ya ce da ita zai koma waje ya sha. Da ya fita waje, sai ya sami wani ɗan akuya ya ba shi furar ’yar kaɗan. Shan ta ke da wuya sai nan take ɗan akuyan ya faɗi matacce.
Nasiru na ganin haka, sai ya yi rami ya binne ragowar furar, ya kwanta nashe-nashe, kamar ya mutu. Jim kaɗan sai ga mahaifiyar Aliyu ta leƙo sai ta ga Nasiru a kwance kamar ya mutu. Ba ta san sanda ta yi subur da baka ba cikin murna ta ce: “Yawwa, madalla. Tun da aka haifi yaron nan nake neman yadda zan gama da shi, ban sami nasara ba sai yanzu.
Ba shakka wannan boka hatsabibi ne, na gode masa.” Tana cikin wannan murna, idanunta a rufe, ta ɗauki Nasiru ta kai shi bayan gari ta jefar; ko tunanin a rufe gawarsa ba ta yi ba saboda tsananin ƙiyayya. Shi kuma Aliyu ɗan’uwan Nasiru sai ya nemi uwar ta gaya masa inda yake.
Da ƙyar dai ta yi masa bayanin da ya gane cewa yana bayan gari, sai ya fita nemansa, ya ci sa’a kuma ya rera wata waƙa a kusa da inda aka jefar da shi:
Nasiru, Nasiru, Nasiru,
Nasiru ɗan Sarkin Zaƙi,
Nasiru tashi mu je shan zaƙi.
Nasiru ya bar duniya,
Nasiru ya tafi lahira.”
Duk da cewa Nasiru yana kusa da Aliyu, bai mayar masa da wannan waƙa ba. Sai Aliyu ya koma gida a cikin matsanancin tashin hankali. Har ma dai ya ce da uwar shi fa ba zai ji daɗin zaman duniya ba, muddin ba ya ganin Nasiru. Can kuma, abokin Nasiru shi ma ya shiga tashin hankali rashin ganin abokinsa.
Shi kuma sai ya sami uwar Aliyu ya ce:
“Mamayo, mamayo, mamayo,
Nasiru ya bar duniya,
Nasiru ya tafi lahira.
Nasiru ya bar duniya,
Ni mazantafi lahira.”
Da uwar Aliyu ta ji wannan waƙa, sai ta ce da Nisiru: “Ina ruwana ka tafi gaba da lahira ma, duk ɗaya ne.” Zuciyarsa cike da baƙin ciki ya kama hanyar daji. Yana cikin tafiya sai ya ga wani mutum a zaune ya gama kai da gwiwa; sai ya matsa kusa da shi ya ce: “Bawan Allah me ya same ka haka?” Yana ɗago kansa, sai abokin nan nasa ya gane ashe wanda ya fito nema ne sai ya tsorata.
Amma abokin nasa sai ya ce da shi: “Haba mutumina, kada ka ji tsoron komai. Ni ne Nasiru.” Hankalin Nisiru ya kwanta, suka sami wuri suka zauna. Bayan sun yi ’yar hira, sai suka yanke shawarar barin garin don gudun mugun halin uwar Aliyu. Sai suka koma wani gari mai babbar kasuwa da karkara mai dausayi, ga filayen noma nan sai an zaɓa.
Da yake su duka muzakkarai ne, sai halin zaƙaƙurancinsu ya sa suka shiga neman abin kansu. Kafin shekara ta dawo kowannensu ya mallaki dukiyar da an jima ba a ga masu kamarta ba. Wata rana bayan kamar shekara biyar Nasiru da abokinsa suna cikin halin baƙunta a wani gari, sai suka yanke shawarar cewa ya kamata su je ganin gida.
Nan da nan ko suka yi laftun dukiya suka ɗora wa raƙuma, suka tafi da ita garinsu. Nasiru ya tarar da uwar Aliyu tana cikin mummunan talauci, ga tsufa ya kama ta, ƙanensa Aliyu kuwa ba ya komai, sai baranta a gidan wani tajiri. Nan take Nasiru ya ba ta dukiya mai tarin yawa.
Ta shiga cin daɗi, ba da daɗewa ba ta murmure. Ya kawo jari mai kauri ya ba ƙanensa Aliyu. Shi da abokinsa kuma suka shirya suka koma wurin sana’arsu. Duk sanda uwar Aliyu ta zauna, sai ta shiga tunanin ƙetar da ta shirya wa Nasiru, da kuma irin alherin da ya saka mata da shi, ta yi da-na-sani. Ta roƙi gafararsa, ya yafe mata. Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Ba a rama alheri da mugunta.
- Duk wanda ya daka ta magulmaci zai tsinci kansa a cikin nadama da dana-sani.
- Mai hankali ba ya rama mugunta da sharri sai da alheri.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Marowata
Edita@rumasau-kallamu










