Tatsuniyar Cin Kasuwar Sama

0
5

Ga ta nan, ga ta nanku.

Da Zanzaro da Barangunda suka ƙulla abota. Wata rana suka je cin kasuwar sararin sama, da nufin su dawo da yamma. Da suka je suka dawo sai suka tarar Gizo ya fito ya zauna ya kame a kan kujera, yana shan iska. Da man hanyar ta bi ta ƙofar gidan Gizon ne.

Da Gizo ya gan su sai ya tashi ya yi musu maraba, suka amsa masa, har suka ba shi tsarabar kasuwa. Gizo da matarsa Koƙi suka ji daɗin tsarabar, sai Koƙi ta shawarci Gizo da ya bi su ko shi ma ya samo kayan daɗi. Gizo ya je da dare ya roƙe su, su taimake shi, su je tare.

Zanzaro yace: “Kai Gizo al’amarinka fa da wuya, ka cika fallasa.” Gizo ya tsaya da rantse-rantse, yana cewa: “Ai na bar halin da kuka san ni da shi a da.” Da ƙyar dai suka amince, suka ce gobe ya shirya za sutafi tare. Da tsakar dare Gizo ya je wurinsu, ya nemi ya tashe su daga barci, wai asuba ta yi. Suka far masa da faɗa cewa yaya zai zo musu da tsakar dare haka?

To idan haka zai yi musu su ba za su je tare da shi ba, domin ya fara halinsa na zumuɗi. Ya dai haƙura ya koma gida, amma ya kasa barci, ya laɓe a hanya har asuba ta yi. Sai suka ji ana kuwwa, ana cewa: “Wayyo Allah, na halaka.” Suka fito suka same shi, suka tambaye shi: “Gizo me ya faru?” Gizo yace: “Yunwa za ta halaka ni. “Sai Barangunda ta ce da shi, “Shiga hancina ka ci abinci”.

Da ya shiga sai ya tarar da wata babbar kasuwa, ya ci abinci har ya ƙoshi. Can bayan wani ɗan lokacin sai Barangunda ta ce da Gizo: “Fita mana, ai yanzu ka ƙoshi.” Sai Gizo ya ce: “Tukuna.” Ashe har Gizo ya ɗauki ƙosai, yana talla. Can dai Barangunda ya harzuƙa, ya yi atishawa sai Gizo ya faɗo tare da faifan tallar ƙosan. Sai Barangunda ya ce masa ya koma cikin hancin ya mayar da ƙosan.

Nan da nan Gizo ya shiga ya mayar, suka ci gaba da tafiya. Can kuma sai suka ji ihu, da aka tambayi Gizo ya ce ƙishirwa ke damun sa. Zanzaro ya ce ya shiga mararsa ya sha ruwa, ya shiga ya sha. Da ya ji sanyin wurin sai ya ƙi fitowa, ya ce sai ya yi wanka tukuna. Zanzaro kuwa bai ɓata lokaci ba, sai kawai ya matsa mararsa Gizo ya faɗo tim!

Haka dai suka yi ta tafiya. Da suka isa bakin kasuwar sama sai suka sami wani wuri suka ajiye kayansu, suka shiga kasuwa. Da Gizo ya ga sun ɓace masa cikin kasuwa sai ya tashi ya shiga kasuwa yana tara yara, yana gaya musu, su zo zai koya musu irin wasan garinsu.

Yara suka taru ya ce musu zai yi waƙa su kuma su amsa. Ya ƙara da cewa: “In kun ji na ce marmaron Zanzaro na sha ruwa, sai ku ce hancin Barangunda da kasuwa.

“Sai ya fara:

“Marmaron Zanzaro na sha ruwa,

hancinBarangunda da kasuwa”

Suka shiga tsakiyar kasuwa, Gizo yana ta rawa, yana tsalle. Zanzaro da Barangunda suka sami labari sai suka zo, suka saurari duk abin da Gizo yake faɗi, suka yi baƙinciki, suka rasa yadda za su yi, suka ma kasa isa wurin Gizo. Shi kuwa da ya gaji sai ya zo ya kwanta, barci ya kwashe shi. Da Zanzaro da Barangunda suka zo suka ga yana barci, sai suka ce madalla, abin nema ya samu, suka ciccire fukafukan da suka ba shi aro, suka sauƙo suka bar shi a sama.

Da Gizo ya farƙa ya ga ba fukafukai, sai ya fita ya yi ta yawace- yawace ko zai gan su, amma bai gan su ba, ya rasa yadda zai komo gidansa, sai ya fashe da kuka. Da yaran gari suka gan shi, sai suka tambaye shi abin da ya faru, ya yi musu bayani, suka ce za su taimake shi. Suka sami doguwar igiya da ganga da abin kiɗa. Suka ɗaura wa gangar igiyar suka ce da shi ya hau saman gangar.

Ya hau suka ba shi abin kiɗa, suka ce idan ya isa ƙasa sai ya kaɗa gangar don idan sun ji
muryarta sun san ya isa kenan, sai su saki shi. Suka fara zura shi. Da ya zo rabi sai ya tambaye su irin muryar da gangar take da ita wadda za su ji ta daga sama. Sai ya ce bari ma ya ji muryar, sai ya kaɗa gangar da abin kiɗa.

Da yaran suka ji muryar sai suka saki igiyar, Gizo ya surmiyo ƙasa, ya faɗi ya yi rugu-rugu. Da ƙyar aka tattara tarkacensa aka kai wa matarsa Koƙi ta shiga jinyarsa. Ya daɗe yana jinya kafin ya warke. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Kowa ya daka rawar wani, zai rasa turmin daka tasa.
  • Kwaɗayi mabuɗin wahala.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceLabari Mai Taken Fansar Hawayen Kakana
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.