Labari Mai Taken Wata Sabuwa

0
6

Taƙaitaccen labari ne duba da yanayin rayuwa da ake ciki don yin hannunka mai sanda ga alʼumma daga taskar uwar muminai💐💐💐💐. 07033941914.

Yau ma kamar kullum na tashi raina a cunkushe kallon kowa nake kamar maƙiyi, nai ƙoƙari na jawo hisnulmuslim don yin azkar ɗin safiya. Duk halin da nake ciki ba ya hana ni yi, na gama na jawo wayata misalin 6am akwai Online classes na islamiya da nake bi duk safiya ina buɗe data telegram na shiga, inda na lalubo ajin da nake bi haka nan nake jin rai duk a ɓace cikin saʼa na samu Malam ya fara, na ci gaba da sauraro ina jotting some important points.

Haka yanai min daɗi nakan ji sauƙi raɗaɗi da yake damuna wanda ban san ta inda ya samu ba, ban san dalilin da yasa na tsinci kaina ciki ba, na furza huci mai zafi daga baki na. 6:30am na bugawa na tashi yara don shirin makaranta ba na iya fita don taya su shiri kowa tasa ta fisshe shi kowa yay sabgar sa. Yarana biyar biyun farko mata ne babbar ita ce ‘ƴar shekara sha biyar me bi mata sha uku sai ƙannansu maza da ɗan shekara goma da takwas autan  kuwa shekara shidda yake.

Gida ya kacame ‘ƴan matan ɗaya na gyara gida ɗayar na shirya musu abun kari su kuwa ‘ƴan mazan ba abun da suke sai dambe da ƙiriniya ni kuwa ko a jikina an tsikari kakkausa, Abbansu ne ya dawo daga masallaci ya same ni ɗaki yace kina jin yaran nan ba za ki musu magana ba? Ko ɗaga kai ban yi ba, domin ni yanzu ba na so yana shiga harka ta, cikin ɗaga murya yace ko ba ki ji ba, nai masa kallon hadirin kaji tare da figar wayata na bar ɗakin.

A raina nace kan ka ake ji tun da na shiga wannan halin na fita harkar kowa, Kawai abun da na Sani Wani ɓangare na zuciyata Yana gaya min “ba ke ba ce ba halimatun nan mai ƙwazo da kazar kazar mai kula da komai da kowa, ni kai na ya shiga duhu na kasa gane komai kawai ina cikin ruɗani da taraddadi cikin raina.  Ina da haƙuri da kai zuciya nesa amma in aka ɓata min, ina da riƙo da sauƙin mantawa.

Saboda haka yanzu ta shafi kowa ba na so kowa ya raɓo ni ko yara suka yi min abin da bai kai ya kawo ba za su sha duka. Kawai abun da na Sani yanzu na zama ba ni da haƙuri ga saurin harziƙa ba na ganin kowa da gemu kana yi min zan rama har in wuce makaɗi da rawa wanda hakan ba ɗabiʼa ta ba ce. Ba ni da abokin hira sai waya, wani lokaci ba wani abun kirki sai ɓata lokaci ban jin daɗin hira da kowa.

Cikin ikon Allah ban faɗa hannun yan sharholiyar social media ba ina yawo na daga wannan class Sai wanna kuma duk Qur’an ake koyarwa ko abin da ya shafi addini amma wannan ƙunci ya hana ni kataɓus da zaizayar ruhi kullum fuskata kamar na kurɓi maɗaci, idan na ji sallamar Abban su sai in ji kamar an watsa min ruwan zafi, idan ina tsakar gida zan shiga ɗaki kafin ya zo na kwanta in kuwa ina ɗakin ne zan kwanta in rufe ido ni mai bacci, duk halin da nake ciki bai taɓa tambayata ko lafiya?

Babban ɗan I don’t care ne Idan yana da abin faɗa ya faɗa in na ga dama na amsa wani lokacin ko ci kanka ba zan ce ba in ɗago in kalle shi ma zan ji kamar ana caka min wuka a ƙahon zuciya. Na kai sati cikin wannan hali na uƙubar rai da ruhi kawai abin da na sani bayan karatuna na online to in nai addu’a nakan ji sauƙi saboda haka ba na wasa da addu’a da roƙon Allah ya ba ni yarda da abinda ya ƙadarta mini kuma ya sa min albarka a cikin sa.

Duk wannan halin da nake ciki gidan mu ba wanda ya sani, Ni yanzu wani abu da ke  damu na ma kawai sai in ji kamar ana ihu a maƙota cikin kiɗima da razana zan leƙo tsakar gida sai in ga kowa yana harkar sa kuma wani ɓangaren zuciya yana gayamin,  in kika koma ɗakin nan kama ki za a yi haka zan ta yi, zuciya ta cika da tsoro na rasa inda zan sa kaina ban yarda da kowa ba adduʼar ma yanzu so take ta gagare ni, da na fara sai in ji kamar an ƙwalla ihu, haka dai duk halin ko in kula na megida na ya fara karɓo turaren miyagu da na jinnu, wani lokacin har da rubutu amma kullum abu ƙaruwa yake don har na haƙura da zuwa aiki .

Cikin dare misalin ƙarfe 3:30 ko makamancin haka kamar an tashe ina bacci, cikin firgici da razana wani tsoro ya kama ni ba dalili, na ji jikina na rawa domin wata ƙara na ji kamar aradu ban san sada na fara faɗin innalillahi waʼinnan ilaihirrajin cikin rawar muryaba, ji nake kamar ana wujijjiga ni tare da jin rugugin muryoyin mutane a ciki, na kasa gane komai, amma kamar an jefa ni cikin durum ban fasa kiran sunan Allah da neman agajinsa ba.

Cikin ikon Allah na ji na fara dawowa hayyaci na jiki na dai na rawa zuciya ta cike da tsoro  na tashi na yo alwala daman ɗabiʼata ce na tada sallah sai a lokacin na ji idona ya ƙwararo ruwan hawaye, na gagara karanta komai ina tsaye zuciya tana ba ni tabbacin a nan ne maganin matsalar take tsahon lokaci ina tsaye can na fara karatu a hankali wata irin nutsuwa ta fara ɗiga cikin ruhina, na cigaba da sallah rakaʼa huɗu na gabatar  ɗaga hannu nai zuwa sama, nai godiya ga Allah tare da salati Manzon Allah sannan na fara kai kukana ga Allah nace, “ya Allah ba ni da kowa ba ni da komai ba ni da wayo ba ni da dabara.

Allah kai kaɗai nake bautawa kuma kai kaɗai nake neman taimako, Allah ina cikin wani hali ban san shi ba, ya Allah ban san dalilin sa ba,  Allah ka kawo min ɗauki da agaji ka sauƙaƙa min ya Allah ka amintar da ni da abun da yake ba ni tsoro ka kawo min mafita, ya Allah” na rufe adduʼa ta da salatin Annabi, na miƙe na cika da wutri ina zaune ina jan istigfari kawai shawarar in ɗau azumi ta faɗo min nai niyya da sahur na jira fitowar Afiji dan sauke faralli.

Alhamdulilla wunin ranar rai na sakayau  lokacin buɗe baki da adduʼoʼi na neman ɗauki daga Allah bayan na idar da sallar ishaʼi na ji kamar an fito da ni daga cikin buhu mai duhun da aka yi wa ɗaurin huhun goro iska ta koʼina na ratsa ni, raina yay fari kamar audiga na cigaba da jan carbi ina kai gaisuwata ga farin jakada Annabi ɗan gatan Allah a haka har bacci yay awon gaba da ni.

Cikin farin ciki na wayi gari da ƙwarin gwiwa na ji ya kamata yau in yi wa ɗakina kwalema na daɗe ban yi shara ba kowani abu gyaran gwado ina miƙewa zanin gado da net na cire sai wanki sannan na dawo ɗaki na fara ɗaga saƙo da loko, in sakato shara yara suna taya ni, cikin ɗan lokaci komai ya koma hayyacinsa, wanda hakan ya yi daidai da lokacin walaha. Na shiga bayi nai wanka nan ɗauro alwala cikin  nishaɗi na gabatar da sallah na jawo wayata don lalubo ko cikin class ɗin da nake bi online zan samu masu gabatar da karatu.

Na ci saʼa kuwa suna karatu nai joining layi na ya zo ni ma na karatu shafi guda cikin suratul hashar, ustaza tai min gyara inda na kasa aka gama karatu na ɗau carbi nai salatin Annabi dan ni shi ne madogarata. Na ɗora da adduʼoʼin godewa Allah tare da yin alƙawarin gyara alaƙa ta tsakani da mijina da ‘ƴa’ƴa da sauran alʼumma kai lokacin da na shiga wannan halin har kaina na zalinta, dan ina jin yunwa in ƙi cin abinci ko in ƙi gyaran jiki ko gyaran muhalli.

Ni da yara ba walwala bare kuma mai gidana da nake masa kallon kanwa uwar gami. A hankali abubuwa sun dawo min na dawo cikin hayyacina na ƙara yarda Adduʼa takobin mumini ce tare da yarda da abin da Allah ya rubuta maka a rayuwa Bahaushe yace kowanne icce akwai bakin hayaƙin sa, in ka yarda da hakan ka zauna lafiya a wannan Rayuwa…….

Danna nan don karantaLabari Mai Taken Ayar Allah

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceYadda Ake Addu’ar Nema Wa ‘Ya’ya Tsari
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.