Labari Mai Taken Ayar Allah

0
33

Shara nake a babban tsakar gidan mu. Mijina ne ƙarami aikina kenan safe da yamma, ban aune ba na tsinkayi Uwani a gabana tsaye wanda ya yi daidai da watsa sharar kan ƙafar ta, kamar me jiran ƙaɗan ta kuwa haske fuskata da wawan mari kwanyar kai na tai wuuuuu kamar katantanwa kafin na ankara ta ƙara ɗora min wani a ɗaya kunnen take nai ƙasa wanwar faɗuwar ‘ƴan bori da ba dan ina jiyo hayaniya ba sai in ce suma na yi, can cikin iskar da take guguwa a samaniya na jiyo muryarta tana cewa ” Idan  gidan ku ba a koya miki saurarawa manya zan koya miki”

Gidan mu uku ne facaloli amma ko tari ba wacce ta yi, na fi minti biyar ina ji kamar ana yin sukuwar dawakai a ka. Haka ya faɗo ɗaki kamar wanda aka wurgo yana zare ido,  jiki na ya yi nauyi kamar dutse saboda ɗazu na maru ban iya ɗago kai na dube shi ba, bai ko damu da halin da nake ciki ba cikin gadara ya ke magana “shi fa matsiyaci ko an sa shi a tandun mai haka zai fito ƙandas, ya ja tsaki,  rai na ya dugunzuma amma na haɗiye.

A rai na ce wannan cin zarafi ya ishe ni ba ya ganin kima ta ko ƙis! ballanta na facaloli na, gaskiya da sake an ba wa me kaza kai,  na yunƙura cikin ƙarfin hali da sanyi murya na ce kai na ke ciwo ko ido in na buɗe jiri nake ji ya taɓe baki ya ce “damuwar ki” sai na ji kamar an watsa min wuta a zuciya na nemi jirin na rasa nai masa duban hadirin kaji “nace anya Haruna ƙirjinka da zuciya? Anya akwai sofanen tausayi na a ranka? Shin har rashin darajar tawa a gunka ya kai haka?

Ko ba komai ni ce uwar ‘ƴa’ƴan ka! Idan ba ka buƙata ta ka sawwaƙe min” kamar wani fusataccen kure ya taso kaina yana huci, na san halin sa dukan mace a gun sa shan ruwa ya fi shi wuya kamar walƙiya cikin zafi nama nai waje a miliyan, na faɗa wanda ka yi da ya isa amma yanzu ɗan ba ƙara.

Rayuwar ba daɗi Rana zafi inuwa ƙuna, tsugune nake a gaban malallauta ina wanke-wanke ina ta saƙa da warwa cikin zuciya ta ba zan yarda in zama karkataciyar kukar kowa ba ni da ‘ƴa’ƴana mun zama kamar mujiya, kawai!!! Na ji an watso min ruwan datti,  a fusace na ɗago muka yi ido huɗu da Rakiya ɗaya daga cikin faccalata nai saroro da son fahimtar tana sane ne ko kuskure ne sai na hango rainin wayo a ƙwayar idon ta  lallai gidan nan suna son warware min zaren tunani na, lallai yau an kai haƙurina ƙarshe cikin himma na taso don rama abinda tai min.

Amma wani ƙululun takaici ya tokare min maƙoshi na kamar an tusa min dusa nai ƙoƙarin yin magana ruwan hawaye ya riga yin awan gaba take fuskata tai sharkaf kamar an kunna famfo  don  gudun kar in kurma ihu gaban mutane na toshe baki  na shige ɗaki da sauri . Duk wani aikin tsakar gida a ɗaki nake yi, ko banɗaki za ni sai na faki ido a tsakar gida, duk facalolina sun haɗe min kai ban taka musu ba bare in zubar ba wacce muke shiri da ita a tunaninsu ni ‘ƴa boko ce kar in raina su,” ƙaramin sani ƙuƙumi”.

Ba mai shiga sabga ta haka tasa ni yin leƙe ƙofar gida, cikin saʼa muka yi kacibus da megidana shi ma ya kawo kai ya ja da baya cikin shan mamaki kamar ya ga miciji yace ashe in na fita ke ma fitowa ki ke yi?   Inda yake shiga ba ta nan yake fita ba kamar ya ari baki Ni dai da na ga ya gagara fahimta sai nayo cikin gida nan fa Uwani ta ara ta yafa me neman kuka an jefe shi da kashi tumakai ai kai yau kagani amma ta saba haka take cika ɗaki da samari sai dai ka jiyo shewa, daga ɗaki na ke jiyo ta nasan ƙarshen zance,  amma  kunci Amna kuma zan ɗau mataki kawai yace.

Wannan karon sun zo min da makircin da na kasa fita, misalin ƙarfe takwas bayan idar da sallar isha na ji shigowar sa kamar kullum ba  sallama  gurin abincin sa ya nufa na ji ya ɓude ya fara ci kawai sai na ji ya danna wata Ashar tare da ƙwalla kiran sunana  cikin ƙaraji kamar saukar Aradu bai saurara ba ya ɗora”  ban yi zaton har kina tunani kashe ni ba munafuka fito nan, ƙirjina yay  tass!!!

Wani gumi ya yanko min kamar an fisan ruwan zafi jikina ya hau bari kamar mazari ƙafafuwa sun kasa ɗauka ta na ja jiki zuwa inda yake muka yi arba ya ƙara zaburowa tuni jikina ya daskare saboda tsoro ya shaƙo ni idona ya fito jawur kamar an taka ƙwaɗo a ka yace “yau sai kin gayan dalilin da yasa ki ke so ki kashe ni, guba a abinci?  Bokon naki har ya kai haka?  Zaman ki ya ƙare a gidan nan,  daga wannan ban ƙara sanin  komai ba ko suma na yi oho?

Buɗe ido na yi na ga jamaʼa cikin ɗaki sun zagaye ni ƙwalla ce ko gumi ne ya  jiƙe ni sharɓan ban sani ba. Wasu na sannu wasu na za ta aikata, mai ya faru? Dole in bar gidan nan kafin a ɗau gawata ba na iya gane fuskokin su don jiri ne ke ɗauka ta amma da yawa suna tofin Allah tsine wai na yi yunƙurin kashe mijina. Shurun da na ji ya ban damar yunƙurawa domin tabbatar da abun da yace, Ni Hajara ta ina na samu guba?  Loma ɗaya na sa a baki na na ji kamar an kunna min wuta na kasa juya abincin haka tasa na furzo shi waje.

Ɗanɗanon darbejiya da uban gishiri ne ya kaure bakin kamar an mare ni ta waje cikin kuma kamar ana  datsa min harshe, na nace na shiga uku!!! Waɗannan bayin Allah yau ta nan suka biyo,  ba ni da mafita gurin alʼumma, ‘ƴa’ƴa sun samu tabo me muni uwar su ta yi nufin kashe uban su. Ban san lokaci da na kurma ihun mai ratsa zuciya na rasa ta ina zan sa kaina.

Yau ba ni da mafuta ba mai goyan bayana daman ba na tunani samun furucin da zai ƙwantar min da rai cikin mutanen da suke tare da ni, abu ɗaya da na sani shi ne ba zan yafewa wanda ya aikata min wannan ba, cikin duhun dare tafiyar ƙafa me nisa na ɗau ‘ƴa’ƴa na muka bar gari don tsira da mutunci.

Sunana Hajara Isah ‘ƴa ɗaya gun iyaye na babana babban malami addini ne a ƙauyen mu yana da buri in yi karatu boko duk da mutanen mu suna ƙyamar karatun musamman ga mata amma malam yakan ce” Ilimi gishirin rayuwa idan mutum ba shi da shi komai ɗaci yake masa”. Hawayen da ba na farin ciki ba ne ya zo lokacin da na karɓi takardar kammala firamare na domin mutuwa ta yi awon gaba da malam.

Sitiyarin rayuwata ya koma gurin kawuna shi kuma ya ce “Karatu gadon maza ne ita mace a gida aka santa” hakan tasa aka aurar da ni a ƙanana shekaru ga Haruna ɗan abokin sa. Na shiga gidan aure ban shirya ba na samu rayuwar gidan mai cike da duhu da ruɗani. Allah ya azurta ni da yara biyu Isa mai sunan malam da Aminatu yau Aure na ya ƙare na nufi garin da a kan ‘ƴa ta ƙi zaman aure gara a kawo musu gawar ta, tsugune ba ta ƙare min ba Ni Hajjo.

Na fahimci za muyi mutuwar kasko ni da ‘ƴa’ƴana dangina sun juyan baya na ƙi zaman aure hakan tasa na yunƙura dan tallafar rayuwar mu, gidan masu kuɗin garin mu nake aikatau ko mai ya samu yi nake  har ɗinki hula, na lashi takobin ‘ƴa’ƴana sai sun samu ingantaciyar rayuwa.

Alhamdulillah ban so jiki na ba ina samun abun tasarifin Rayuwa, na sa yara na makarantar boko da ta islamiya ni ma na samu damar komawa yaƙi da jahilci. Lokaci ya shuɗe na kuma fuskanci ƙalubalen rayuwa wasu na ka-da su wasu sun kayar ni, yanzu takardar N C E  ce da ni kuma ina koyarwa a makarantar ‘ƴan mata ta ƙauyen mu, ina ba su ƙwarin gwiwa a kan su yi karatu ƙalubalen rayuwa ba ya hana cikar buri sai dai in ba manufa. A ko ina ilimi haske ne duhu ba zai hana shi haskawa ba.

Wata uku masu zuwa za a yi bikin Aminatu Haruna mai goro da Dr. Husain Mukhtar, likita ne a asibitin da suka je yin practical bayan gama karatun ta da ta yi na zama cikakkiyar unguwar zoma, yanzu haka tana aiki a Asibitin garin mu, shi kuma Isha Haruna mai goro yana karatu a babbar jamiʼar ƙasar mu domin zama cikakken mai shariʼa yana aji huɗu…….

Danna nan don karanta Tatsuniyar Kurege Da Kura

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceYadda Ake Ittikafi
Labarin na GabaTatsuniyar Zomo Da Damo
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.