Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana wasu ’yan matan ƙauye suka tafi rafi su, watau kamun kifi. Suka kuma yi sa’a suka kamo kifaye, suka kama hanya suka koma gida. A kan hanyarsu ta zuwa gida sai suka haɗu da wata tsohuwa sai ta tsayar da su, ta roƙi su sammata kifin da suka kamo, ko da mai ƙaya ne.
Sai suka hana ta. Amma sai wata budurwa daga cikinsu ta ɗeba mata kifin. Ta karɓa, ta gode mata suka tafi. Washe-gari da suka koma rafi don kamun kifi, da yawa daga cikin ’yan matan kuma sun kamo kifin mai yawa, ƙoransu cike maƙil. Da tsohuwar nan ta roƙe su, suka hana ta sai waccan budurwa da ta bai wa tsohuwa kifin jiya ta gaya mata cewa yau ba ta samu ba sai wasu ’yan ƙanana guda biyu kawai.
Ga shi kuma tana jin tausayin ’yar tsohuwar. Saboda haka sai ta ba ta ɗaya, ita kuma ta riƙe ɗaya. Kafin su rabu, sai tsohuwar ta gaya mata in ta je gida da wannan kifi guda ɗaya da ya rage a hannunta, kada ta dafa shi ta sanya shi a cikin randar gidansu. Bayan ta isa gida sai ta saka kifin a cikin randar kamar yadda tsohuwa ta ce ta yi. Sai ta shiga ɗaki ta kwanta.
Da gari ya waye sai ta buɗe randa don ta ɗauki ɗan kifinta, amma sai ta ga randa ta cika maƙil da manya- manyan kifaye. Ta yi ta ɗiba, amma kifayen nan ba sa ƙarewa. Bayan ’yan kwanaki ’yan mata suka koma rafi don su kamo kifi, amma wannan ranar ba su sami komai ba, sai suka koma gida babu kifi.
Washe-gari sai aka yi shela a gari cewa Sarki yana son ya ci kifi, kuma duk budurwar da ta kamo kifi ta dafa wa Sarki ta kai masa zai aure ta. Gaba ɗayan ’yan matan ƙauyen suka fita kamun kifi, amma ba wadda ta samo sai wannan budurwa da ta taimakawa tsohuwa da kifi. Yadda aka yi ta samo kifin nan kuwa shi ne, da ta kama hanyar rafi
sai ta haɗu da wannan tsohuwar.
Sai tsohuwa ta ce mata kada ta je babban rafi, ta nuna mata wata hanya da za ta kai ta har bakin wani ƙaramin gulbi. Sai tsohuwa ta ce ta yashe ruwan. Da budurwa marainiya ta fara yashewa sai ta fara ganin manyan kifaye, ta yi ta ɗiba har ƙwaryarta ta cika, ta koma gida. A duk faɗin garin budurwar nan kaɗai ce ta kamo kifi a wannan rana. Bayan ta dafa kifi ta sa a cikin akushi ta kai fada, mutanen gari da Sarki suka yi mamaki.
Nan take Sarki ya amince zai aure ta. Bayan ta koma gida sai aka gaya mata ta sanar da iyayenta, za a yi bikinta da Sarki. To da yake iyayenta duk sun rasu marainiya ce, ba ta da kowa, da ta koma gida dare ya yi ta kwanta, sai ta tashi tsakar dare tana kuka domin tana tunanin ba wanda zai yi mata kayan gara. Tana cikin wannan hali na damuwa, sai ta ga kwatsam tsohuwar nan ta ɓullo mata a tsakar ɗaki, kuma ta tambaye ta ko mene ne yake damun ta.
Sai marainiya ta yi mata bayanin dukkan abin da yake damun ta, har ya zamanto ba ta iya yin barci. Da’yar tsohuwa ta lallashe ta sai kuma ta gaya mata za ta iya yin dukkan abin da take buƙata. Yarinya ta yi ajiyar zuciya cikin murna, ta yi wa tsohuwa godiya. Tun kafin gari ya waye, sai ta ga ɗakinta cike da kayan gara fiye da yadda take zato za ta samu, ta yi ta murna.
Ta godewa Allah. Ana nan, ana nan, ranar bikinta ta zo, aka ɗaura musu aure ta yi ta murna. Tagode wa Allah aka yi gagarumin biki, aka kai amarya gidan Sarki. Da kayan gara ya ƙare sai tsohuwa ta sake ɓullo mata a ɗakinta, ta kuma kawo mata kayan alatu da na marmari. Tace mata kullum za ta rinka kawo mata kayan ɗadi ta rinka ba Sarki, amma kada ta gaya wa kowa.
Yarinya ta ce ba za ta gaya wakowa ba. Suka yi sallama tsohuwa ta tafi. Bayan ’yan kwanaki sai matan Sarki suka fara tsegumi cewa amarya ba ta da kowa, amma kullum Sarki yana ƙara son ta fiye da sauran matansa, kuma kayan alatu da take ba Sarki wa yake ba ta? Suka yi ta bincike, amma ba su gano bakin zaren ba, sai suka haƙura, suka bar ta.
To shi Sarkin bai taɓa haihuwa ba, duk sanda matansa suka ɗauki ciki, sai ya zube. Rannan bayan ’yan shekaru da auren marainiya da Sarki, sai ya tara matansa, bayan ya tabbatar kowacce tana da ciki. Ya ce da su kowacce ta tafi gidan iyayenta, kuma kada ta dawo sai ta haihu. Bayan kowacce ta kama hanyar gidansu, sai ita kuma amaryar
Sarki marainiya ta tafi gindin wata tsamiya ta zauna, ta kama kuka, tana waƙa tana cewa:
“Wa zai ba ni yaro a yau?
Wa zai amshi haihuwa a yau?
Ni ba ni da uwa, ni ba ni da uba?”
Tana cikin wannan hali sai tsohuwa ta zo ta sake tambayar ta abin da yake damun ta. Sai ta kwashe labarin yadda suka yi da Sarki ta gaya mata. Sai tsohuwa ta ɗauke ta, ta kai ta gidanta, ta cigaba da kula da ita, tana yi mata albishirin cewa in Allah ya yarda, za ta haihu, cikin ba zai zube ba.
Suna nan tare da tsohuwahar ranar haihuwa ta zo, ta haifi ɗanta lafiyayye, kowa ya gan shi ya ga ubansa. Amma sauran matan Sarki kuwa ba su sami haihuwa ba, sai ɗaya daga cikin kishiyoyinta ta sami labarin haihuwar amaryar Sarki marainiya. Sai ta fara bin ta a sace, har ranar da aka sa za su koma gidan Sarki. Rannan sai amaryar Sarki ta tafi bakin rafi donta yi wanka tare da ɗanta.
Da ta je bakin rafin sai ta ajiye jaririn, ta shiga wanka. Sai kishiyar nan tata ta zo ta sace yaron, ta gudu da shi.Da suka koma fada sai amaryar Sarki marainiya ta je ta gayawa Sarki cewa ta haihu, amma an sace abin da ta haifa. Sai aka ƙi yarda da wannan magana. Da kishiyarta wadda ta sace yaron ta zo, sai suka ce ita ce ta haifi yaron.
Ita kuwa matar Sarki marainiya sai aka sa fadawa da yaran Sarki suka kafa mata ɗaki irin na dawaki, aka ajiye ta a can, bisa cewa ta yi wa Sarki ƙarya. Da kishiyarta ta ba yaron nono sai ya ƙi kamawa. Aka yi juyin duniyar nan, jaririn nan ya ƙi shan nono, sai aka rinƙa ba shi madarar shanu, har ya girma. Ana nan, ana nan, wata rana sai ɗan duba watau Sarkin bokayen Sarki, ya gaya wa Sarki cewa wannan ɗan nasa matar da ta rene shi ba ita ce uwarsa ba.
Mamaki ya kama Sarki, sai ya nemi Sarkin bokaye da ya gaya masa ta yadda zai gane uwar yaron. Sai mai duba ya ce ya tara matansa ranar kasuwar garin, kuma a tara mutane a fada, sannan duk matansa su yi abinci, su kawo shi bainar jama’a, kuma su jeru a fada. Idan an yi haka, sai a ce da yaron ya zaɓi abincin da matan Sarki suka kai wurin, to duk abincin da yaron ya zo ya ci, tabbas mai wannan abinci ita ce uwarsa.
Ba tare da nuna wata shakka ba, Sarki ya ce a yi haka ɗin. Sarki ya umarci matansa a kan abin da ake so kowacce ta yi. Duk matan suka yi dafe-dafen kayan daɗi. Ranar kasuwa ta zo, mutane suka taru, fada ta cika ta batse. Amma ita amaryar Sarki marainiya, kuma uwar yaron ta gaskiya, ba ta da abin da za ta dafa.
Hasali ma tun ranar da aka kai ta ɗakin dawaki ba ta cin komai sai in an zuba wa doki dusa ta ɗiba, ta dama ta sha, ko ta yi tuwo da ita. Da aka ce har ita ma sai ta yi abinci, sai ta ɗebi dusar da aka kai wa dawaki kamar yadda ta saba, ta kama gafiya ta yanka, ta gyara ta da kyau, ta ɗauka ta kai fada.
Da ta isa fada sai ta tarar duk sauran matan Sarki sun jeru, suka shiga yi mata kallon reni da nuna mata ƙyama. Can da ɗan Sarki ya zo a kan doki aka ce ya zaɓi abincin wadda zai ci daga cikin matan Sarki, sai kawai ya ƙarya linzami ya doshi inda mahaifiyarsa marainiya take. Da zuwa sai ya kama cin abincin dusar nan da ke gabanta.
Da mutanen da suka yi cincirindo a fada suka ga haka, sai mamakin yadda al’amarin ya kasance ya kama su.Da Sarki ya ga alama lallai gaskiya ce ta yi halinta, sai yasa aka kama matar da ta sace yaron ta ce nata ne, aka fille mata kai. Ita kuwa mahaifiyar yaron ta gaskiya sai Sarki ya ba ta haƙuri, ya nemi ta gafarta masa.
Ba a daɗe da yin wannan abu ba, Sarki ya kamu da rashin lafiya, wadda ta zama ta ajalinsa. Bayan an gama zaman makokin rasuwar Sarki, sai aka naɗa shi ɗan marainiya a matsayin sabon Sarki. A cikin ikon Allah yaro ya hau karagar mulki. Ya ci gaba da tafiyar da harkar mulki kuma ’yar tsohuwar nan da uwarsa zumuncin da yake tsakaninsu ya ƙara ƙarfi. Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Alheri danko ne ba ya faɗuwa ƙasa banza.
- In Allah ya rufa maka asiri, ba mai tonawa.
- Karya fure take ba ta ’ya’ya.
Wannan tatsunya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Karanta Tatsuniyar Kurege Da Kura (Na Biyu)
Edita@rumasau-kallamu








