Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana wata mata mai juna biyu ta je ɗibar ruwa a bakin rafi. Bayan ta cika tulunta da ruwa, sai ta kasa ɗauka saboda cikinta ya girma sai nishi take yi, abin tausayi. Kuma ga shi ita kaɗai ce ƙwal a wurin.
Haka ta haƙura ta zauna. Can sai ga wani mutum ya taho, sai ta dube shi ta ce: “Malam don girman Allah ka ɗora ni mana.” Sai yace shi ba zai ɗora ta ba sai dai idan za ta yi masa wani alkawari. Mai ciki ta dube shi ta ce: “Na mene ne?” Shi ko ya kaɗa baki yace: “Idan kin haihu, in namiji ne to abokina ne, idan kuma mace ce, to matar ɗana ce.
” Da jin wannan sharaɗi sai ta yarda. Ya ɗauki tulu ya ɗora mata ta kama hanya ta tafi gida. Da ta je gida sai ta yi wa mijinta bayanin yadda suka yi da mutumin. Da yake mijinta mai sauƙin kai ne, sai ya ce: “To shi ke nan, Allah ya sauke ki lafiya.
”Bayan ’yan kwanaki sai mutumin ya zagayo gidan matar, suka gaisa. Ya nuna mata ɗansa suka yi sallama ya koma gida. Bayan wata ɗaya sai matar ta haifi ’ya mace, amma jikinta na jaki ne. Da mutumin ya ga haka sai ya yi halin dattaku ya ce: “To shi kenan tun da an yi alƙawari ai sai an cika.
”Sai ya kira ɗansa aka ɗaura musu aure da yarinyar ya kai ta gidansu. Yaro ya zauna da mace mai jikin jaki, ya ɗaure ta a gida. Amma duk sanda ya tafi gona idan ya dawo gida sai ya tarar an yi masa shara, an dafa masa abinci an kuma kai masa ruwan wanka bayan ɗaki.
Kullum haka, sai abin ya fara ba shi tsoro tun da ba kowa a gidan. Rannan sai ya je ya sami babansa ya gaya masa, amma sai baban ya ƙi kula shi sai ya kore shi. To da ma yaron yana mutunci da wata tsohuwa maƙwabciyarsa dangarsu ɗaya. Sai wata rana ya zauna a gindin bishiya, yana tunanin abin mamakin da ke samunsa.
Da tsohuwar ta gan shi a zaune haka, sai ta kira shi ta ce: “Ɗanyaro me ke damunka ne?” Shi ko sai ya kwashe labari ya bai wa wannan tsohuwa. To da ma ashe tsohuwa tana ganin duk abin da yarinya take yi idan ya tafi gona. Watau rikiɗa take yi ta koma kyakkyawar budurwa, ta shiga yi masa waƙa, ta yi shara, ta yi wanke-wanke, ta dafa abinci, ta ɗebo ruwa a rijiya ta kai masa banɗaki.
Duk bayanta gama kafin ya dawo sai ta mayar da jikinta na jaka, ta ɗaure kanta a turke.
Da tsohuwa ta gama bai wa yaron labarin abin da take gani sai ta shawarce shi da cewa gobe ya kwashi kayan aiki kamar zai tafi gona, idan ya kama hanya sai ya ratse a hanya, ya zagayo gidanta.
Bayan sun gama shirya zancensu, sai ya koma gida yana mamaki, ya shiga ɗaki ya kwanta. Da gari ya waye sai ya saka kayan aiki ya ɗauki fartanyarsa ya kama hanyar gona. Bayan ya tafi ya yi nisa sai ya ratse cikin ciyawa, ya zagayo ta gidan tsohuwa, ya same ta a ɗaki.
Daga nan sai suka ɓuya suka shiga leƙen yarinyar. Jim kaɗan sai suka ga ta rikiɗa ta koma kyakkyawar mace, ta fara waƙa ta kama shara da sauran ayyukan gida, ta shirya miya, ta dafa abinci, ta zuba nasa, ta kai masa ruwan wanka banɗaki. A daidai lokacin da ta fito daga bayan gida sai mijinta ya tsallaka danga ya dira a gabanta.
Sai kawai ta razana za ta rikiɗa sai ya kama hannunta ya fara yi mata waƙa yana roƙon ta. Da ta ji waƙarsa sai ta fara kuka tana roƙon ya yafe mata. Shi kenan suka yi zamansu cikin daɗi suka ci gaba da more rayuwarsu cikin ƙauna da farin ciki. Dan kan ɓarya, ba domin Gizo ba da na sheƙa muku ƙarya. Ƙurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Alkawari kaya ne, in an sauke sai a huta.
- Tsintar dami a kala.
- Rabon kwaɗo ba ya hawa sama.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Cilakowa Da Kodokodo
Edita@rumasau-kallamu








