Shirye-shiryen tafiya aikin Hajji sun kankama domin ana maganar saura sati uku alhazai su fara tashi. Duk wani abu da suke buƙata na kula da gida Mustapha ya tanada ya kawo musu, kuma ya yi mata bayanin abokinsa wanda dama ta san shi; shi ne zai kawo musu raguna kuma ya tsaya a yanka.
Yanzu kullum sai yamma ta yi sai ya ɗauki Najan a mota su fice wai sun tafi bita, haka ta zuba musu ido tana ta ba wa kanta haƙuri. Gaba ɗaya maganar tafiyar ta fita daga ran Khadeeja, kuma Mustaphan ma gaba ɗaya ya fice mata daga rai; ji take yi kamar matsayinta a wajensa bai wuce na mai aiki ba.
Zuwa yanzu ta san wanda ma bai san halin da suke ciki ba ya san Naja tana da ciki domin tara yawunta ya ƙaru kuma ta yi fari tas irin na masu ciki. Sai dai har yanzu ita Khadeejan ba ta sanar da Mustapha cewa ta san Najan tana da ciki ba. Sai shirye-shiryensa yake yi yana zuwa sallama da mutane domin Hajia ta gama gayawa kaf dangi Mustapha zai tafi Hajji da matarsa.
Danginsa da na Naja sai zuwa suke sallama, duk wanda ya zo sai ya cewa Khadeeja Allah ya kirawo ‘yan baya. Wannan kalmar ba ƙaramin ɓata mata rai take yi ba, amma haka ta share ta kawar da kai. Tun jiya ba ta jin daɗi sai dai ba ta gane me yake damunta ba, haka take ta fama. Da yake ba ita ce da aiki ba kuma Hammad baya nan haka ta wuni a kwance.
Daf da magriba ta fara gane abinda yake damunta; mararta ce take ciwo ga wani amai da yake taso mata amma ya ƙi fitowa. Haka ta sha panadol ta shige ɗakinta ta kwanta. Wajen 9pm Mustaphan ya shigo ɗakin domin sanar da ita ya dawo kamar yanda ya saba. Har ya juya zai fita ya ɗan tsaya yace ‘Wai ya na ganki a kwance ne? kamar ba ki da lafiya.’
‘Uhm, mara tace take ɗan ciwo.’ Ta amsa a gajiye. ‘Ok, Allah ya sauwaƙe. Ko kina buƙatar wani abu? Tace ‘No ina jin zai daina don na ma sha panadol. Ya sake yi mata sannu sannan ya juya ya fice. Can wajen 10:30pm ciwon ya matsa mata, tun tana daurewa har ta kasa. Ta lalubi wayarta ta kirawo shi, ba tare da ɓata lokaci ba ya shigo ɗakin nata.
Kafin ya shigo ma ta riga ta shige banɗaki saboda yanda take jin kamar za ta yi kashi, kafin ta ƙarasa toilet ɗin abinda yake shirin fitowa daga jikinta ya riga ya fito sai jini da ya biyo baya gaba ɗaya da aman da ya tokare mata ƙirji. A tsugune ya same ta a banɗakin, ya ƙarasa da sauri ya duba halin da take ciki. Ya kama ta ta miƙe sannan ta ƙarasa ta zauna a kan toilet.
Tace ya jira ta ta wanke jikinta sai su je asibiti. Nan da nan ta wanke jiki ta gyara sannan ta tattare zanin nata da bainda ya fita daga cikin nata gaba ɗaya ta saka a leda sannan ta fito ta shirya suka kama hanyar asibiti. Babu wanda ya yi magana sai shi da yake mata sannu lokaci zuwa lokaci; a haka har suka isa asibitin.
Ba tare da ɓata lokaci ba likita ya duba ta kuma ya tabbatar da cewa cikin jikinta ya fice gaba ɗaya, don ko wankin ciki ma ba sai an yi mata saboda komai ya fice. Aka rubuta mata magunguna aka sallame su. Tun a mota ta gane Mustapha bai ji daɗin zubewar cikin ba, duk da ita ta fi shishiga damuwa da zubewar cikin; amma dai ta kula ba haka ya yi ba wancan lokacin da ta yi ɓari.
Har yanzu tana jin ciwon mara don haka ba za ta iya surutu ba. Bayan sun dawo gida ta haye samanta ta sake yin wanka sannan ta sha magungunanta ta saka Hafsa ta haɗa mata indomie da shayi mai kauri ta zauna ta ci. Sai da ta ci ta ƙoshi sannan ta kirawo Mommy da Yaya Mama ta sanar da su.
A daren Momy ta so zuwa sai da Khadeejan ta hana ta ta sanar da ita cewa ta sami lafiya su bari da safe sa zo; don haka suka haƙura. Can wajen ɗaya saura ya same ta a ɗakin; tana kwance a gefen gado tana shirin yin bacci. Ya zauna a gefenta yace ‘Sannu. ‘Yauwa. Ta amsa tana daga kwance.
Suka yi shiru na ɗan lokaci, ta san da zance a bakinsa don haka ta yi kasaƙe tana jiran ta ji me zai ce. Jimawa kaɗan ya gyara zama kamar wani mara gaskiya yace ‘Um wai ni me ya faru ne? Me ya kawo wannan miscarriage ɗin? Ko wani abun kika sha ne? Ta yi ‘yar dariya tace ‘Babu abinda na sha, Allah ne dai ya kawo kamar yanda ya kawo wancan.’
Ya ɗan yi jim yace ‘Allah ya sauwaƙe. Ya sake yi mata sannu sannan bayan ya tabbatar babu abinda take buƙata sannan ya fice ya bar ta. Washe gari tun da safe Mommy da Yaya Mama suka zo, nan suka zauna suka zube mata kayan dubiyar da Baffa ya aiko mata. Mommy ta ji daɗi yanda ta ganta ta riga ta miƙe kamar ma ba daren jiya ta yi ɓari ba, sai kai wa da kawowarta take yi ana hira da ita.
Har sun fara shirin tafiya suna zaune Yaya Mama tace ‘Kin ga idan dai ciki ne zai sa a fasa tafiya da ke ai yanzu sai a ba ki kujerarki ko. Ta yi dariya tace ‘Dama kujera ba tawa ba ce, babu ruwan ciki niyyar ba ni ne ba a yi ba. Mommy ta dafa ta tana ɗan zare ido tace ‘Khadeeja in ce ko dai ba wani abu kika sha kika fitar da cikin nan ba saboda kujerar Makka.’
Ta ɗan zaro ido ta kalle ta suka haɗa ido tace ‘Mommy! Me ya yi min zafi? Wallahi babu abinda na sha, sai kace wata marar hankali? Ai na gaya miki fa ba ciki ne ya sa ba zai ba ni kujerar ba kawai haka ya yi niyya, yanzu kuma ɓarewar cikin ba za ta sa ya fasa tafiya da ita ba. Ni ce kawai ba za shi da ni ba. Yaya Mama tace ‘Haba Mommy, a kan wata kujera za ta ɓarar da ciki?
Ta gyara zama ‘To ai abun naku ne sai a hankali. Suka ƙarasa hirarrakinsu suka yi mata sallama suka kama hanya. Ta zauna tana tunanin dalilin da yasa Momy za ta yi wannan tunanin; to ko tunanin da Mustapha ma ya yi kenan yake tambayarta me ya faru bayan sun dawo daga asibiti? Allah ya gani babu abinda ta sha, cikin nan ma ba ta taɓa kawo masa zubewa ba kuma ko da wasa ba ta so hakan ba.
Kawai dai Allah ya yi ikonsa ne kamar yanda ya yi a wancan karon, kuma ta san shi ne zai fitar da ita daga duk wani zargi da zai iya tasowa. Kujerar Makka ma idan dai Mustapha ne zai ba ta kam ba ta so ta san Allah zai hore mata ta je tunda ita ma tana kan neman kudinta.
Can da yamma su Hajia suka shigo ita da Yaya Jidda da ‘yan matanta. Ba ta san da Hajia suka shigo ba don haka ta yi banza da su tunda ta jiyo su a wajen Naja. Jimawa kaɗan suka hawo saman gaba ɗaya; ta sauke su a nan parlor ɗinta ta kawo musu ruwa da lemo, suka zauna suka yi mata dubiya da jaje. Suna cikin hirarrakinsu Mustaphan shi ma ya shigo ya zauna aka cigaba da hirar yana sa musu baki lokaci zuwa lokaci.
Yaya Jidda ta dube ta tace ‘Alhazai dai sun kusa tashi balle ma a ce za a canza a ba ki kujera tunda cikin da ya hana ya fice, ko ka canza ne Mustapha? Ya kalle ta sannan ya kalli Khadeejan yace ‘A a ai an gama wannan maganar, ita za ta zauna da yara idan Allah ya kai mu shekara mai zuwa sai a je da ita. Hajia tace ‘E ai an gama wannan maganar.
Allah ya ba ki lafiya ya kawo wasu yaran masu albarka. Ita Najan sai su je kamar yanda aka tsara. Ita dai tana zaune a tsakiyarsu amma ba ta iya ce musu komai ba; to kenan su ma zarginta suke yi da zubar da cikin ko me? To me Mustaphan ya gaya musu har suke mata wannan zargin? Sai da suka gama hirarrakinsu sannan suka yi mata sallama suka tashi suka fice.
Bayan sallar Magriba Mustaphan ya same ta a ɗakinta tana zaune a gefen gado, bayan ta amsa sallamarsa ya karasa ya zauna a gefenta. Ta yi masa sannu da zuwa ya amsa suka zauna suka ɗan yi shiru, jimawa kaɗan ya kirawo sunanta. Bayan ta amsa ya kakkafe ta da ido sannan yace ‘Wai ni me kika yi ne cikin nan ya zube, ko wani abun kika sha saboda ya zube mu tafi da ke aikin Hajji.’
Ta yi ‘yar dariyar takaici sannan tace ‘Mustapha ban zubar da ciki ba, domin kujerarka ta maka ba ta isa ta saka ni na zubar da ciki ba. Kamar yanda Allah ya kawo wancan cikin ya zube ba tare da na yi wani abu ba wannan ɗinma hakan ce ta kasance. Yace ‘To ai kin ce wancan wahala ce da aiyuka suka yi miki yawa ya sa ya zube, ko ba haka kika ce ba? Wanna kuma na ga babu wannan ko?
Ta gyara zama ita ma ta kakkafe shi da ido tace cikin zafin rai tace ‘Mustapha wai ba ka ji me nace ba; ban zubar da ciki ba kuma kujerar Makka ba ta isa ta sa ni na aikata hakan ba. Na riga na san ba ka yi niyyar zuwa da ni Hajj ba domin lokacin da kake cewa ina da ciki ba za ka je da ni ba ita ma Najan cikin ne da ita. Ka dai zaɓi matarka wadda kake so ka tafi da ita ni kuma ‘yar aikin gidanka ka bar ni na kular maka da gida da yara kamar yanda ka saba.
Idan ma kai ne ka gayawa ‘yan uwanka wannan maganar har suke yar min da magana to ka koma ka gaya musu ƙarya ne. Ya miƙe a fusace ‘Daga an tambaye ki kuma shi ne za ki yi min rashi kunya kamar yanda kika saba saboda ke ba a gaya miki gaskiya ko? Wannene rashin kunyar a ciki; ganewa da na yi cewa ka yi rashin adalci wajen zaɓar matar da za ka je da ita hajji ko kuwa gaskiyar da na gaya maka?’
‘Mtsewwwww!’ Ya ja dogon tsaki ya miƙe a fusace ya fice daga ɗakin. Ta zuba fuskarta a tafukan hannayenta, so take hawayenta ya fita ko za ta samu ta ji sanyi a ranta amma hawayen ya bushe ƙyamas. Ƙirjinta har zafi yake saboda yanda zuciyarta take turiri; Mommy ce ta fara yi mata wannan zargin ga shi yanzu Mustaphan ma da shi da ‘yanuwansa suna zargin ta zubar da cikin ne don ya je da ita Hajji.
Tabbas Allah sai ya bi mata haƙƙinta. Haka ta kwanta zuciyarta na mata zafi saboda takaici; ta so ta kirawo Mommy ta gaya mata ko za ta sami salama a ranta, to amma hakan ba zai yi mata wani amfani ba. Tunda Mommy ɗin ce ta fara yi mata wannan zargin. Ta sake fashewa da kukan takaici ta gyara kwanciyarta; yau ita ce da kwana amma ta san yanda Mustapha ya fice daga ɗakin nan wataƙila sai dai idan ya dawo daga aikin hajji sannan ya waiwaye ta.
Ranar Laraba aka kirawo su Mustapha, jirginsu zai tashi ƙarfe biyar na yamma don haka aka ba su shawara su kasance a cikin airport ɗin tun kafin azahar. Sun gama haɗa kayansu shi da Najan kuma ya riga ya sanar da Khadeeja, ya danƙa mata duk wani abu da take buƙata don kula da gidan. Wajen ƙarfe sha ɗaya yana zaune a parlor ɗinsa shi da yara Khadeeja ta fito daga ɗakinta ta shige kitcen don ɗora abincin rana.
Ya tsallake yaran ya bi bayanta ya tsaya daga ƙofar kitchen ɗin ya rungume hannuwansa a ƙirji sannan yace ‘Kada fa ki dafa abincin da ni yanzu za mu wuce airport, ki dafa ke da yara kawai. ‘To.’ Ta amsa murya ƙasa-ƙasa. Ya kula tunda suka yi maganar zubewar cikinta take son ta-da masa fitina shi kuma ba zai saurare ta ba, fata yake kawai Naja ta gama haɗa kayanta su fice su bar mata gidan kafin ta takalo rigima. Don haka ya juya ya koma cikin yara ya zauna.
Har ta ɗauko tukunya za ta ɗora shinkafa sai kuma ta fasa, ta ajiye tukunyar ta fito daga kitchen ɗin ta koma ɗakinta. Tana shiga ta wuce gaban mudubi ta ja kujerar ta zauna; ba ta san me ya sa ta fasa ɗora girkin ta zo ta zauna ba. Kamar dai tana buƙatar wani wanda za su yi magana ne amma ta rasa wanda za ta gayawa damuwarta ya fahimce ta.
Ta ɗaga fuskarta ta kalli kanta a cikin mudubin, ta yi wa kanta murmushi sannan ta sake sunkuyar da idanuwanta. Yanzu haka za ta cigaba da rayuwa a gidan nan a matsayin ‘yar aiki? Tunda matsayinta bai wuce hakan ba, duk wasu alamu sun nuna. Mustapha ya tabbatar mata ba zai taɓa iya yi mata adalci ba tun ma tana ita kaɗai matarsa balle yanzu da ya haɗata da wadda yake ƙauna.
Ta sake daga ido ta kalli kanta a mudubin; to wai zaman me take a gidan Mustapha ne? Shi dai ya gama nuna mata ba zai taɓa canzawaba; duk wani abu da yake yi mata a halin yanzu za ta iya yi wa kanta. Buƙatar aure ce kawai wadda dama sai ya gama dama yake zuwa wajenta tunda ta daina bin shi ɗakinsa. Ta yanke ƙauna daga samun adalci a wajen Mustapha komai yawan ƙaunar da za ta nuna masa da kulawarta ga ‘yayansa.
Ta tabbatar shi ba zai iya nuna mata ƙauna da kulawa ba; wataƙila sai dai idan ana ƙwatan soyayya ta ƙwata ta ƙarfin tsiya daga wajen Mustapha; to idan sai an ƙwata kuma ya koma ba so ba. Ta ja gwauron numfashi, ta zuba fuskarta a tafukan hannayenta, ɗumin hawayenta ne ya sa ta ɗaga fuskar tata ta kalli hawayen da ya ɗiga a hannuwanta.
Ta jijjiga kai tana murmushi a lokacin da hawaye yake gangarewa a kumatunta; ta gaji, ba za ta iya ba, ta gaji da wannan kokawar, ta gaji da kokawar ƙwatowa kanta mutunci da so a wajen Mustapha, ta gaji ba za ta iya cigaba ba. Ta miƙe kamar wadda aka tsikara ta nufi gaban wardrobe, ta sauke akwati ta fara zuba kayanta. Ba za ta iya cigaba da wannan rayuwar ba, gara kawai a yi ta ta ƙare.
A hankali ya turo ƙofar ɗakin ya shigo da sallama, fuskarta fayau kamar ma farinciki take. Ta dube shi ta amsa sallamarsa ta cigaba da jera kayanta a cikin akwatin. Ya dube ta da mamaki yace ‘Ya na ga kina haɗa kaya, ko wardrobe ɗin kike gyarawa? Ta ɗan tsaya da zuba kayan ta kalle shi tace ‘No ba gyarawa zan yi ba, gidan mu zan tafi.’
Mamakinsa ya ƙaru, ya kasa matsawa kusa da ita ‘Ban gane gidanku za ki tafi ba bayan yanzu za mu tafi, shigowa ma na yi na gaya miki ki fito ku yi sallama da Naja za mu wuce. Ta rufe akwatin ta zuge sannan ta juya cikin wardrobe ɗin ta ɗauko jakarta ta sake ajiyewa a kan gadon. Ta kalle shi tace ‘Ka ba ni minti biyar na ƙarasa haɗa kayana na fita sai ka rufe gidan gaba ɗaya don ni ma gidanmu zan tafi.’
Ya ɗan fara fusata ya matsa ya sha gabanta yana cewa ‘Ba na son wulaƙanci Khadeeja, wai ke me yasa ne duk lokacin da mutum yake cikin uzuri yake so ki yi masa wani abu sai kin yi fitina ne? An gama magana da ke amma yanzu saboda kina so ki sa mu yi missing flight za ki fara maganar za ki tafi gida. Ta yi murmushi ta ɗaga kai ta kalle shi tana cewa ‘In sha Allahu wannan ita ce fitina ta ƙarshe da zan yi maka Mustapha, daga ita ba zan sake ba.
Gidanmu zan tafi Mustapha saboda na gaji da aurenka, kuma na gama aurenka daga yau. Za ka iya sakina yanzu ko kuma duk lokacin da ka sami natsuwa ka rubuta min takardar sakin ka aiko gida; amma ba zan sake zama a matsayin matarka ba. Gaba ɗaya yawun bakinsa ƙafewa ya yi saboda bai taɓa zaton Khadeeja za ta iya faɗa masa haka ba.
Ya sake ta! Kuma a wannan lokacin; ya kalle ta ya sunkuyar da kai, jimawa kaɗan ya sake kallonta sannan yace ‘Saboda kujerar Makka kike so ki kashe aurenki Khadeeja? Kujerar da na gaya miki next year da ke za a tafi. Tukunna ma kin san hukuncin matar da ta nemi saki a wajen maigidanta ba tare da wani dalili ba?
Ta jijjiga kai tana murmushi a daidai lokacin da ƙwalla ta faɗo daga idonta, ta share ƙwallar sannan tace ‘Ko ɗaya, kujerarka ba ta kai ta ɗaga min hankali ba tunda dai ƙasar Makka ta Allah ce ba taka ba. Alhamdulillahi ma kace wadda ta nemi saki ba tare da dalili ba; don ni ina da dalili kuma Allan da ya halicce ni ya fi ni sanin dalilin. Amma tabbas yau zan bar gidanka da aurenka Mustapha.
Ya ja baya ya sake ƙare mata kallo, yace ‘Kin san me kike faɗa kuwa Khadeeja? Please idan wasa kike ki bari kada ki saka mu yi missing flight. Ta yi ‘yar dariya yayin da ta ware hijabinta ta saka tana cewa ‘Ba wasa nake ba, amma dai kana da zaɓi. Ka sake ni yanzu ko kuma ka tafi idan ka dawo ka rubuta min takardar ka aiko min gida.’
Ta kewaye shi ta ɗauko jakarta daga kan gadon ta nufi gaban mudubi. Yana tsaye mamaki ya hana shi magana. Yana ɗaga kai idonsa ya sauka a kan agogon bangon yake kafe a saman ɗakin; 12:52pm agogon ya nuna; shi da aka cewa su zama suna cikin airport kafin azahar. ‘Mtseww!’ ya ja ɗan gajeran tsaki sannan ya fesar da iska daga bakinsa.
‘Khadeeja yanzu ya kike so na yi da yaran bayan mun gama magana da ke? Kuma me na yi miki da har za ki riƙe a matsayin hujjar da ta saka za ki ce na sake ki? Yara kam ai yanzu ba matsalata ba ne, duk yanda ka yi da su daidai ne. Ni dai zan tafi, yanzu in sha Allah. Ta sauke akwatinta ta fara ja tana nufin ƙofar ɗakin. Ya bi bayanta da kallo; to me ya yi mata da har za ta ce ya sake ta a wannan lokacin?
Anya kuwa ta san menene zawarci? Kawai saboda baƙin cikin ba da ita zai fara tafiya aikin Hajji ba? Ko ma me take nufi ya kamata ya cika mata burinta, wataƙila kafin ya dawo ta dawo hayyacinta kuma ta gane mahimmancin aure a rayuwarta. In ya so idan ya dawo da ita sai ta haƙura ta zauna tunda dai shi bai ga wani abu da ya yi mata ba.
Tana daf da ƙarasawa bakin ƙofar yace ‘Khadeeja. Ta juyo ta ɗan tsaya ‘Ki je na sake ki saki ɗaya. Ta yi sauri ta juya fuskarta saboda kaucewa haɗa ido da shi; duk da ita nema kuma da yaƙinin zai aikata haka amma sai da fitar kalmar ta yi mata ciwo. Ta sake juyowa cikin murya ƙasa-ƙasa tace ‘Nagode.’
‘Za ki yi nadamar rabuwa da ni Khadeeja.’ Ya faɗa a gajarce. Ta kalle shi ta yi murmushi sannan ta kawar da kanta ta faki idonsa ta goge ƙwallar da ta taru a kwarmin idonta. Bugun ƙofa ne ya katse su da Shukra tana cewa ‘Abba Anti tace za ku makara fa. ‘Um, gani nan zuwa.’ Ya amsa daga cikin ɗakin.
Ya wuce Khadeejan ya buɗe ƙofar ya fice. Ta bi bayansa janye da akwatinta. Shukra ta tsaya a gefenta tace ‘Anti ke ma har da ke za a tafi? Ta kama hannunta tace ‘A a ni gidanmu zan tafi ba da ni za a tafi ba. Gidan Mommy? To da mu za ki tafi? Ta tambaya da mamaki.‘Eh, gidan Mommy zan tafi amma ba da ku zan tafi ba. Abbanku zai gaya muku wadda zata zauna da ku.’
Gaba ɗaya yaran suka zuba mata ido suna ƙoƙarin gane me take faɗa. Ta ƙwalawa Hafsa kira ta ba ta umarni ta haɗa kayanta su tafi gida. Ba tare da ɓata lokaci ba ta juya. Ta dubi Naja wadda take zaune tana binsu da kallon mamaki tace ‘Maman Rukayya sai kun dawo, Allah ya amsa ibada Alah ya maimaita mana. ‘Amin.’ Ta amsa a gajarce sannan ta dubi Mustapha tace ‘Ban fa gane ba, me yake faruwa ne?’
Kafin ya ba ta amsa tuni Khadeeja ta ja akwatinta ta fice daga parlor ɗin. Shukra wadda ta ƙarasa ta faɗa jikin Abbanta ta rushe da kuka; saboda ta kasa fahimtar me yake faruwa su da aka ce za a yi tafiya har Abbansu a bar su da Anti kuma Antin ta fara tafiya. Ya dubi Naja yace ‘Cewa ta yi na sake ta kuma na sake ta, tunda ita ta nema.’
Ta ɗan firgita ta dafe ƙirji, ba ta san lokacin da yawun da yake bakinta ya wuce ba tace Saboda me? Kai kuma ka biye mata? Saboda baƙin cikin zan tafi dake Hajji ban tafi da ita ba.’ Ya faɗa cike da ɗacin rai. Ya ƙarasa ya zauna a kan kujera a jigace kamar wanda aka tura. Sukayi cirko cirko suna kallon shi. Habib ya shigo a guje ko sallama bai yi ba, yana cewa ‘Abba na ga Anti tafi. Me yake faruwa ne? Waye zai zauna da mu?’
Ya miƙe a jigace yana cewa ‘Maza kowa ya ɗebo kaya ko kala ɗaya ne mu wuce, sai na ajiyeku gidan Hajia. In ya so ko gobe sai ku dawo da Yaya Jidda ku ɗebi kaya. Antin ta tafi. Ya fice ba tare da ya saurare su ba Naja ta rufa masa baya. Nasreen ta kalli Habib ta kare gefen bakinta kamar me raɗa tace ‘Ya sake ta. Ya zaro ido zai yi magana suka jiyo muryar Abbansu daga ƙafar bene yana cewa ‘Maza fa ku sauko. Suka miƙe gaba ɗaya suka shirya suka fice.
Danna nan don karanta Mijin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Takwas
Edita@rumasau-kallamu










