Mijin Marigayiya Babi Na Goma

0
80
Karo na babu iyaka kenan da ta ɗauki wayarta ta buɗo whatsapp ta duba; har yanzu bai amsa messages ɗinta ba kuma bai biyo whatsapp call in da ta yi masa ba. To me yake faruwa ne? Allah dai yasa lafiya Mustapha yake da shi da yaran. Da farko da ta ga ta yi magana ta whatsapp bai kula ta ba kuma ta kirawo shi ta whatsapp ɗin bai ɗaga ba sai ta zata ko fushi ya yi, amma dai zuwa yau kwana uku abun ya fara ba ta tsoro kada ta je ko wani abu ne ya same shi.
Ta riga ta san babu credit a wayar don haka ko balance ma ba ta duba ba; shi ɗin ba mutum ne mai son saka mata credit ba, idan ma ta yi magana sai yace wa za ta kirawo ko kuma me za ta yi da data ɗin. Idan aka yi albashi dai idan ta yi magana yana saka mata naira ɗari biyar, shi ne za ta samu ta raba ta sa data sauran ta ɗan yi waya.
Don haka yanzun ma babu na wayar sai dai data ɗin da ta yi mata saura. Ta yi tsaki sannan ta sauka daga kan gadon Nabila inda take kwance ta wuce ɗakin Mommy.A parlor ta sami Mommy tana zaune tana kallon tafsiri a tashar Sunnah TV, ta zauna a kusa da ita bayan ta yi sallama ta amsa. Sai da suka ɗan yi jim kaɗan ta kula dai Mommy babu abinda za ta ce mata sannan tace ‘Mommy don Allah ki ɗan saka min 1k a waya mana.’
Ta kalle ta tana dariya tace ‘1k kuma? Ina Mustaphan ko kuma yau ba nashi kike so ba tunda kina gidana nawa kike so?’ Ita ma dariyar ta yi ta ƙara langaɓe kai ‘A a Mommy, don Allah dai ki taimaka, wallahi ya saka min ƙararwa na yi kuma dai kin san ba ni da kuɗi. Ke kenan kullum ba ki da kuɗi?’
‘Mommy bari dai na fara aiki. Uhm, shi Mustaphan ko ɗan na kashewa ba ya yaga miki balle ga ki ‘yar makaranta?’ Ta ɗan marairaice ‘To ai kin ga yanzu an yi hutu Mommy, duk ‘yan sauran canjin ma na kashe. Shi yasa kike maula kuma? To ɗauko min wayata a ɗaki na saka miki a cikin wanda mijina ya ba ni.’
Ta miƙe tana dariya tace ‘Mommy. Baffanta ba wai millionaire ba ne amma dai ta san yana da kyauta; duk da Mommy tana sayar da ‘yan kunnaye da sarƙoƙi amma duk wata sai ya tura mata kuɗin kashewa account ɗinta sai dai ko ya tura babu yawa amma fa sai ya tura.
Kuma idan dai ta buƙaci wani abu bayan wannan to yana iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya yi mata sai dai ko idan babu hali. Ta yi zaton haka za ta je ta samu a wajen Mustapha, musamman da yake yana yawan yi mata kyaututtuka da saka credit a waya lokacin da yana neman aurenta.
Sai dai bayan ta shiga gidan sai ta tarar ba haka ba ne; don wani lokacin a kan ya saka mata kati a waya ya gwammace ya ba ta aron wayarsa ta yi waya. Ko da ta koma makaranta ma ta yi zaton zai ɗan dinga ba ta kuɗin makaranta da kuɗin kashewa sai dai tun a ranar farko da gane ba zai jure ba.
Domin da farko bayan ta gama shiryawa ta yi zaton zai kai ta ne, amma sai dai suna fitowa da aka zo inda zai ɗauke hanya ya wuce office ɗinsu sai yace ta sauka a nan ta hau motar haya. Da ta yi maganar kuɗin mota kuma sai yace mata wai ya zata tana da kuɗi; ta dai samu ya ba ta naira dubu kamar ba da son ranshi ba.
Tun daga ranar ma sai ya zama ta daina damuwa ta yi sai ta shirya ta bi shi, yawanci sai ta jira idan ya fita sai ta kama hanya a motar haya. Kuɗin motar ma tana shirin ta tambayi Baffa ya dinga ba ta aka shiga lockdown; kuma har yanzu tana da niyyar kafin ta koma gida ta sanar da Baffanta kawai ya dinga tura mata kuɗin mota.
Tana ta wannan tunanin ta je taɗdauko wayar ta kawo wa Momy; ba tare da ɓata lokaci ba ta tura mara katin naira dubu kamar yanda ta buƙata. Nan da nan ta koma ɗaki ta sake hayewa kan gadon Nabila sannan ta danna masa kira. Sai da wayar ta kusa tsinkewa sannan ya ɗauka, cike da isa yana magana da ƙyar ya amsa sallamarta, haka ma gaisuwarta kamar ba zai amsa ba.
Wannan ya sa jikinta ya yi sanyi kuzarin da ta fara wayar da shi duk ya gushe. Cikin sanyi murya tace ‘Babe, ya na ji ka haka? Ko ba ka da lafiya ne?’ Sai da ya ɗan yi jinkiri sannan ya amsa ‘Umm, lafiyata ƙalau. Ke kin damu da lafiyata ne da kike wannan tambayar? Ba dole ki ji ni haka ba tunda kin zaɓi ki nesanta kanki da ni?’
Nan ta fahimci inda zancen ya dosa, amma da yake so take ta waske sai tace ‘Haba Babe ya za a yi na guje ka? Tunda da kuka tafi daga nan nake ta yi maka message ta whatsapp, ba ka gani ba ne? Kuma wallahi wayar ma ka san ba ni da credit, yanzun ma da ƙyar na samu Mommy ta saka min ɗari biyu shine nake kiranka fa. Haba Babe ya za a yi kace ban damu da kai ba?’
‘To idan kin damu da ni ya za a yi na zo har gidanku ga azumi kin sani kuma ga shi ana lockdown? Amma kina kallonmu ni da yarana duk muna ta murna za ki dawo amma kika ce ba za ki dawo ba sai bayan sallah. To ai na gaya maka wannan ba ni na tsara haka ba, Mommy ce. Kuma ka san dai idan mace ta haihu dai ana yin gyara da sauransu, sallar nan fa kuma saura bai fi kwana goma sha shida ba.
Haba Babe to meye na fushin?’ Shiru ya yi ba tare da yace mata komai ba suna sauraren numfashin juna. Ita ce ta gaji da sauraro tace ‘Ya na ji shiru ne? ina yara na?’ ‘Ai ba ki damu da su ba shi yasa suna ta cewa ki biyo su kika ƙi. ’Ta fara gajiya da wannan mitar tasa da duk abinda tace sai ya ce ba ta damu da su ba shi da ‘yayansa, to wai ita ba ta buƙatar a damu da ita ne ko me yake nufi?
Shi ba zai iya kula da ita ba kuma ya bar ta ma cikin natsuwa a inda za a kula da ita ta ɗan sami natsuwa yana nema ya hana? Ta ɗan yi murmushi mai sauti ta danne fushinta sannan ta saita muryarta tace ‘To don Allah ka yi haƙuri ka daina cewa ban damu da ku ba, kai ka san na damu daku. Kamar yau ne za ka ga lokacin ya yi ai na dawo, ko ba shikenan ba.’
‘Umm, amma dai da za ki dawo yanzu ai da ya fi ko? Haka kawai ni ba gwauro ba kin saka ni azumi babu mata. Kawai idan an buɗe gari na zo na ɗauke ki mu tafi, shi ne kawai zan san kin damu da ni. Ta dan ɗaga murya tace ‘Ah, Babe to me zan cewa Mommy, ni daɗi miji zan bi mijina kenan ko me?’
‘Ba wani daɗi miji, ai aure ne kuma ita ma ta sani. To gaskiya dai ka bari sai bayan sallar kawai.’ Haka dai suka ɗauki lokaci suna waya ba tare da ta amince za ta dawo ɗin ba, maimaita masa kawai take sai bayan sallar. Don haka kusan a fusace ya katse wayar ba tare da sun yi wata sallamar kirki ba.
Ta jefa wayar a kan gadon kusa da ita ta ja tsaki, sai kuma ta kifa kanta a kan pillow sai hawaye. Ta godewa Allah Nabila tana ɗakin Mommy tana bacci da sai ta gayawa Mommy tana kuka. Ta fara nadamar sakawa da ta yi Mommy tace ta zauna a gida har bayan sallah, yanzu gashi yana fushi da ita.
Ita ba ta zata wannan abun zai sa ya yi fushi ba don da ta san zai yi fushi ma da ko gidan ba za ta taho ba za ta haƙura ya je ya ɗauko ta. Bata sani ba ko za ta iya jure jinsa a cikin damuwa har na tsawon sati biyu ko uku, amma dai za ta gwada. Don da kunya tace a barta sai bayan sallah sannan yanzu kuma ta zo tace za ta koma.
Haka ta ƙarasa wunin ranar cike da damuwa da nadamar zaman da ta zaɓa za ta yi a gida. Haka ta cigaba da haƙuri tana buga masa waya wanda kullum idan ta buga gaisawa kawai suke yi babu wata magana mai daɗi, kamar ma shi dole take masa. Abun yana matuƙar damunta don haka ta fara rama wadda Mommy ta zata don ta cigaba da azumi ne tunda ta sami lafiya; idan ta yi zuru-zuru aka yi magana sai tace azumin ne da wahala.
Tun da ya kai su gidan Hajia bai sake zuwa ba tunda garin a rufe yake ba a fita, sai yau Asabar a lokacin saura sati ɗaya sallah. Yana fita ya tsaya a shagon telansa ya karɓar musu ɗinkunan kayan sallansu wanda tun kafin a fara azumi ya kai; wanda har da na Khadeeja a ciki, ya tsaya aka ba shi leda ya ware nata waɗanda ba shi da niyyar kai mata gidansu.
Ya dai yarda zai ajiye mata a ɗakinta duk lokacin da ta dawo ta gani. Yana karɓa kai tsaye ya wuce gidan Hajia cike da kewar yaransa. Tun daga nesa ya hango Habib a zaune a kofar gida tare da wani yaro, ba wasa suke yi ba a zaune suke kawai sun yi shiru kowa da abinda ya dame shi.
Kafin ya ƙarasa tsayar da motar ya taso da fara’arsa; ya gyara tsayuwar motar ya buɗe kofa yana sake ƙarewa Habib din kallo wanda ya yi zuru-zuru kamar wanda ya kwana da yunwa. ‘Abba sannu da zuwa.’ Muryar Habib ta katse shi. ‘Yauwa Habib, ya naganka kamar kana jin yunwa ko azumi kake ya fara ba ka wahala tun da safe haka?’
Idonsa ya ɗan yi rau-rau yace ‘Eh, azumi nake yi. To ba ka yi sahur ba ne?’ ‘Ba sosai ba, baƙin tuwo ne kuma ba na ci ga shi kuma babu wani abincin a gidan sai shi, na ɗan ci kaɗan dai. To ba sai ka fasa yin azumin ba? ɗa safe ka yi breakfast.’ ‘Hajia ma haka tace na fasa yin azumin amma ni nace zan yi, idan ma ban yi ba ba abinci zan samu ba sai an sha ruwa.
Tunda muka zo ma sau ɗaya na sha azumi.’ Cike da tsananin mamaki yace ‘Ban gane ba abincin kake samu ba sai kace wani almajiri? Ba a ba ka abinci ne a gidan? Ina Baito? Ai Baito sai da rana take zuwa, kuma safiya tana yi Hajia take cewa mu tafi gidan Anti Jidda mu yi wanka a can mu ci abinci a can. Kuma idan mun je sai Anti Jiddan tace babu abinci sai dai kawai wata ran ta ba mu baƙin shayi da ragowar ƙosai ko doya.
Idan kuma mutum ya dame ta sai ta yi masa faɗa, ita ma Shukra da Nasreen ragowar kunu ne kawai ko kuma idan an yi sa’a an rage abincin shan ruwa shi ne ake ba su.’ Mamakinsa ya ƙaru, yace ‘A a, ai na turowa Anti Jidda kuɗi a sayi indomie da cornflakes har da madara, ba a siya ba ko me ya faru da su.’
Ya ɗan zaro ido ‘Tab, tunda muka zo ba mu taɓa cin indomie ba ko cornfalkes. In an sha ruwa dai da yake muna gidan Hajia shi ne aka haɗa mana shayi da madara har da ƙwai ma ake soya mana da kaza, amma dai da rana babu wanda yake ba mu abinci. A wajen Hajia ma muke shan ruwa tare da ita da Alhaji.
Ya yi matuƙar mamaki kuma ya ji tausayin Habib; amma kuma yana matuƙar mamakin yanda za a yi a ce Yaya Jidda ta bar masa yara da yunwa. Ranar da ya kawo su bayan ya tafi ta kirawo shi tana tambayarsa kuɗi a sayi kayan shayi da indomie, kuma a take ya tura mata naira dubu goma don a siyo da wuri. To me ya faru da kuɗin da ake hora masa yara da yunwa?
Tare suka jero da Habib ɗin suka nufi cikin gidan, suna daf da shiga suka ci karo da Afaf tare da Shukra da Nasreen kowacce sanye da hijabinta, nan da nan suka faɗa jikinsa suna murna ‘Abba, Abba. Bayan ya amsa gaisuwarsu yace ‘Ina za ku je?’ Afaf tace ‘Gidan Anti Jidda za su je su yi breakfast.’
‘Ke kina azumin ne?’ ‘Eh ina yi.’ ‘To ku zo mu wuce ciki ku yi breakfast ɗin a nan.’ Nasreen ta yi dariya tace ‘Tab ai babu abincin, da an gama shan ruwa Baito take juye duk wani ragowar abinci ta tafi da shi. Kuma Hajia cewa take mu je gidan Anti Jidda a dafa mana indomie amma idan mun je ba a dafa bana, baƙin shayi ake ba mu da ragowar ƙosai ko kunu.’
Ya ɗauki shukra ya ja hannun Nasreen yana cewa ‘ku zo mu je. Bayan sun gaisa da Hajia tace ‘To ka bar su su je gidan Jidda ta dafa musu indomie ɗin su karya sai su dawo ko? Yunwa suke ji ga su nan.’ Nan suka yi wa Hajia bayanin abinda ake ba su idan suka je gidan yaya jidda; ita ma ta yi mamaki sosai. Tace ‘To me yasa ba ku taɓa faɗa ba?’
Nasreen ta zumɓuro baki tace ‘Yaya Meena ce tace duk wanda ya faɗa sai ta ci ubansa ta karta masa rashin mutunci don ta san mu da tsinin baki.’ Daga Hajiyan har Mustaphan mamaki ne ya kama su, Meena ita ce babbar ‘yar Yaya Jidda. To amma me zai sa ta yi haka bayan Jiddan da kanta ta gayawa Hajia ya turo kuɗin indomie da kayan karin kumallon yaran?
Tace ‘Lallai daga Aminan har Jiddan za su zo su same ni.’ Saboda tsabar takaici Mustapha kasa magana ya yi. A nan ya sake ba da kudi Habib ya fita kanti ya siyo musu indomie, yana kawowa Afaf ta dafa musu da ƙwai tunda dama da akwai ƙwai a gidan. Haka ya saka su a gaba duka sai da suka karya azumin suka ci suka ƙoshi.
Nan ya zauna suka cigaba da hira wajen Hajia tunda shi ma Alhaji ya fice; sai dai har la’asar ta  kawo jiki Yaya Jidda bata zo gidan ba saboda yaronta Abdallah ya shigo gidan lokacin suna cin indomie shi ma ya zauna aka ci da shi kuma yana gamawa ya koma gida ya gayawa uwarsu Abban Afaf ya zo har ma ya sa an dafa musu indomie da ƙwai.
Don haka tana sane ta ƙi zuwa saboda rashin gaskiya. Haka ya wuni a gidan ransa a ɓace yana tunanin mafita; tabbas duk Khadeeja ce ta janyo masa wannan wulaƙancin. To yanzu ya zai yi da yaran? Idan ya tafi da su ba za su bar shi ya zauna a nutse ba, kuma ma ya san Hajia ba za ta yarda ya tafi da su gida su zauna tare da shi ba.
Sai dai kamar yanda ta riga ta faɗa ya je ya siyo abubuwan da suke buƙata ya kawo ita sai ta dinga dafa musu kafin Baito ta zo; domin ita ma Baito ɗin mijinta ne ba shi da lafiya take jinyarsa shi yasa ba za ta iya zuwa da safe ba. La’asar tana matsowa ranshi ya sake ɓaci, kuma har lokacin Yaya Jidda ba ta iso ba.
Bayan ya idar da sallar la’asar yana zaune a kan dadduma yana tunanin mafita Habib ya shigo ya same shi. Bai daɗe da zama ba yace ‘Abba da ma ka kai mu gidan Mama, ka ga dama mun daɗe ba mu je ba tunda muka koma gida. Um, to ai da sallah za ku je ko? Ko ba kwa son zama a nan ɗin ne? Ai ka ga yanzu Hajia da kanta za ta dinga ba ku breakfast ɗin ko?’
‘Um, nan ɗin ma muna son zama amma can ɗin ma muna so, in ya so idan Anti Khadeeja ta dawo sai mu dawo.’ Nan sauran yaran suka shigo suka saka shi a gaba a kan su gidan Mama suke so su je; shi ɗin ma yana so ya kai su don ya san ba za a bar su da yunwa a can ba tunda ko babu mai aiki akwai ‘yan mata. To amma yanzu hakan yana nufin kenan ba za a iya riƙe masa yaransa a gidansu ba ko me?
Ita kuma Yaya Jidda me take nufi? Gashi ta ƙi zuwa, shi kuma ba zai je gidanta ba don ya fi so ta zo su yi a gaban Hajia. Haka dai yaran nan suka saka shi a gaba dole ya amsa zai wuce da su. Ita ma Hajia da ya gaya mata zai kai su sai da ta nuna ɓacin ranta don gani take kamar fushi ya yi da yanda ya sami yaran, sai da Alhaji ya sa baki kuma suka ga Nasreen tana nema ta saka musu kuka sannan suka bari ya kwashi yaran suka wuce gidan Maman su Ma’u.
Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Tara
labarin da ya wuceAbin Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Mafarki Mara Kyau
Labarin na GabaMijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Ɗaya
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.