Abubuwan Da Ya Kamata Mu Kiyaye Don Inganta Lafiyarmu

0
34

MU DAINA AIKATA WAƊANNAN HALAYEN

Aikata waɗannan ɗabi’un marasa kyau ga mutum na iya jawo masa ciwon ƙoda (Nephritis) don haka in ka ji ko kin ji wani abu da kin san halinki ne to ki daina don Allah.

1. Riƙon fitsari: Jinkiri wajen yin fitsari cutar da kai ne mutum ya kasance yana jin fitsari amma ya ƙi zuwa ya yi yai ta riƙon sa yana takurewa, to ku sani duk sanda ƙoda ta tace fitsari ta turo shi ga mafitsara ba abinda da ake so irin a fitar da shi domin in kana riƙe shi to a hankali wani zai fara komawa ga ƙoda (kidney) wanda daga nan kuma matsala za ta fara afkuwa.

2. Ƙin shan ruwa: Rashin shan ruwa wadatacce yadda ya kamata nan ma matsala ne, ko mutum yana jin ƙishi sai ya sha kaɗan ko kuwa ma mutum ya gama cin abinci amma ya ƙi shan ruwan kwata-kwata musamman abinci mai nauyi da mai gina jiki irin su (carbohydrate & protein). Mai irin wannan hali ya kuka da kansa shi ruwa ana so ka dinga shan sa ba sai in kana jin ƙishi ba. Sannan in da hali in abinci ka gama ci to ka sha tea ko ruwan ɗumi ba ruwan sanyi ba.

3. Yawan shan gishiri akwai matsala ga ƙoda ba sai ga mai hawan jini ba, musamman mutanen da ke da irin ɗabi’ar nan ta ƙarawa abinci ko miya ɗanyen gishiri idan bai musu daidai ba, to su ma su kiyaye yana interfering da aikin cortex cikin ƙoda.

4. Rashin shan magunguna ga ƙananun cututtuka da ake ganin ko ba a sha ba za a warke kamar jin zafi ko murɗawar ciki, zafin fitsari ko ƙaiƙayin maƙogwaro.

5. Sannan kuma shan magunguna ba bisa ƙa’ida ba kuma ba bisa umarnin likita ba wato (self medication) wannan na cutar da ƙoda ƙwarai da gaske don haka duk mai irin wannan shi ma to ya sani ya miƙawa ciwon ƙoda takardar gayyata.

6. Yawan cin nama fiye da ƙa’ida: Su ma masu wannan al’adar su sani cewa ba burgewa ba ne a ce ka mayar da cin nama kullum kullum ko kuwa kwana 1 ko 2 kurum kake ɗaga ƙafa, hasali ma ƙila ba ka ko ba ki da ƙoƙarin motsa jiki, Sannan in kuka samu sai kun ji kun ci kun yi hani’an to mutum ya kiyayi kansa.

6. Rashin cin wadataccen abinci: Mutum ya riƙa ma kansa ƙwauro da gangan saboda tsurfa ko kuwa tunanin kar ya yi ƙiba, to masu irin wannan suma su kula.

SHAWARA TA A GAREKU

Shi fa jiki yana son service kamar mota ce in ana mata juye ta fi lafiya. Don haka jiki ma na buƙatar hutu, wanka, sanya tsaftataccen tufafi da kuma abinci mai kyau ba mai tsada ba. Yana da kyau kar ka mayar da cikin ka kodayaushe abinci iri guda, wato ka yi ta cin carbohydrate ko protein, jiki baya son haka shi yasa masu yawan cin carbohydrate kan yi fama da kitse a jika haka su ma masu cin protein kan yi ta fama da nauyin jiki.

Ki sani in kina cin waɗannan (masara, tuwo, dankali, doya, rogo, garin kwaki, flower,) ko da ba rana ɗaya kike haɗa su ba, abu ɗaya kike ci kullum domin duk carbohydrate ne, don haka ake gaurayawa da vitamins, lipids, water, protein, and minerals a yi tsari me kyau.

Da an ga alamun cuttukan sanyi wato ƙaiƙayin gaba, ko fitar ruwa a gaba ga mace ko namiji a nemi magani, ku daina yadda da zancen cewa ko ba magani yana tafiya ko ka ji wasu ma ana ce musu wai mataccen maniyyi ne, duk ƙarya ce ba wani mataccen maniyyi a likitan ce.

Karshe Da An Ji Alamun;

Yawan ciwon baya daga kasa ko sama wajen kafada, canzawar ɗanɗanon baki zuwa kalar kanwa ko ƙarfen da ya yi tsatsa, canzawar fitsari zuwa duhu-duhu kuma kaɗan-kaɗan in an je yi, yawan ganin jiri da kasa samun nutsuwa, yawan kasala, to a hanzarta zuwa a ga likita domin waɗannan alamun ciwon ne.

Allah ya kare mu! Ya ƙara mana lafiya da zama lafiya!!!

Karanta Yadda Ciwon Baki Yake
Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceIllolin iPhone Ga Tarbiyyar ‘Ya’yanmu
Labarin na GabaSunayen Wasu Kayan Abinci Da Itatuwa Da Turanci