khairatu.shehu
Bayan mun ji rabe-raben ƙwayoyi kamar yadda masana suka bayyana, sai kuma mu je ga bayanin nau’o’in magunguna da wasu abubuwan da matasa, musamman mata suke amfani da su don su yi maye.
Wasu magungunan da matasa suke amfani da su dan yin maye, akan bai wa mutum su a asibiti in ya sami wata matsala ta rashin barci ko zafin ciwo ko raɗaɗi ko na hana jin kasala ko ƙara kuzari da dai sauransu.
Amma idan mutum ya cigaba da shan waɗannan magunguna ba bisa umarnin likita ba, don son ransa da kuma ganin wancan karon ya sha ya yi masa magani, sai kuma ya ci gaba da sha ba bisa umarnin likita ba, to daga nan mutum ya zama ɗan ƙwaya wanda haka zai iya kai shi nakasa ko birkicewar ƙwaƙwalwa har ma ta kai da rashin hankali ko rasa rai baki ɗaya.
Wasu magungunan kuma masu wartsakarwa (stimulants) ne kamar hodar Iblis (cocaine) da nicotine (wanda ake samu a cikin taba sigari) da caffeine (wanda ake samu a cikin shayi/tea da kofi/coffee da goro).
Wasu kuma suna sanya gane-gane da jiye-jiye (hallucinogens), kamar tabar wiwi da kuma LSD. Akwai magunguna masu sa barci (sedatives), misali valium da diazepam da maganin mura ko tari. Wasu kuwa magungunan suna sa jiki ya natsu (depressants), kamar giya. Sai kuma magunguna masu rage zafin ciwo ko raɗaɗi (analgesics), da dai sauransu.
Amma su masu sha ko ci ko zuƙa ko yin suraci (rufe kai don tarar tururi) ko kuma yin allura don su yi maye suna yi ya zarce ƙa’idojin da masana suka shimfiɗa wa mai yin amfani da su, ko kuma a mayar da amfani da waɗannan abubuwa su zama jiki, wato na yau da kullum daga nan an shiga garari.
Magungunan sun kasu kashi-kashi. Akwai waɗanda ake sha na ƙwayoyi ko ake sha na ruwa, kamar magangunan mura da tari da giya ta gargajiya, kamar burkutu da kokino da bammi da kuma ta zamani, wato ‘yar kanti. Akwai waɗanda ake shaƙawa a hanci (inhalation/sniffing), kamar cocaine, da waɗanda ake tarba da shakar warinsu ta baki da hanci, kamar sholisho da sauransu.
Akwai waɗanda ake zuƙar hayaƙin da baki (smoking), kamar tabar wiwi da taba sigari. Akwai kuma waɗanda ake yin allurarsu ta hanyoyin jijiya (intravenous/iv injection), kamar heroine da coceine da sauran allurai kamar pentozocine da fortwine.
Yanzu za mu ware hanyoyi guda hudu da ake da su wajen sarrafa abubuwan da suke sa maye.
Domin karanta cikakakken littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina mafita? wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa danna nan
Danna nan don karanta Matsalolin da Shaye-Shayen Kayan Maye Ke Haifarwa Ga Al’umma
Edita@rumasau-kallamu