Wasu Daga Dalilan Shaye-shayen Ƙwayoyi

0
9

khairatu.shehu

Masu iya magana suna cewa, ruwa ba ya tsami a banza, kuma in ka ga zomo a kasuwa kai shi aka yi. Yadda iya bincike ya tabbatar daga majiya mai tushe shi ne, ‘yan mata masu shaye-shaye suna shan ƙwayoyi da wiwi da giya da hodar Iblis (cocaine) maganin mura ko na tari da sauran abubuwan sa maye don kawai su yi maye saboda wasu dalilai kamar haka:

1. Don a yi nishaɗi kawai

2. Saboda kawar da ɓacin rai, (wai don damuwarsu ta ragu)
3. Yawan kwaɗayi da ƙwalamar cewa sai an sha duk wani abu da aka ga wata kawa ko wani saurayi ko kuma aboki yana sha.

4. Idan suna so su yi wa wasu rashin albarka (wato rashin kunya ko tsageranci), domin in ba su sha ba kunya da tsoro suna iya hana su yin tsageranci.

5. Kwaikwayon ƙawaye da samari ko abokai don sun ga suna sha.

6. Wasu iyayensu suka gani suna sha, shi ya sa su ma suka shiga sha.

7. In suna so su yi fasiƙanci sai su sha.

8. Wasu don kawai su yi ta barci.

9. Don su yi duk abin da suka ƙudiri aniyar yi a ransu;

10. Kaɗaitaka da yawan tunane-tunane suna sa wasu su shiga shaye-shaye.

11. Sha’awar yadda mawaƙan ƙasashen Turawa da na yammacin duniya suke tafiyar da rayuwarsu ta fuskar shaye-shaye.

12. Saboda ba za su iya riƙe karatu ko haddace abin da aka koya musu a makaranta ba matuƙar ba su sha ba.
13. Saurayi yana bai wa budurwa ba tare da ta sani ba, don ya samu ya yi lalata da ita.

14. Akwai masu sha don su nuna cewa sun waye ko don su burge.

15. Saboda nuna isa, cewa za su iya yin abin da suke so, don babu wanda ya isa ya hana su.

16. Soyayya da mashayi ko ɗan maye ko ‘yar maye.
17. Rashin aikin yi.

18. Sakar wa yarinya budurwa kula da kanta da ɗaukar nauyin lamuran rayuwarta ta yau da kullum.

19. Gwasalewa da rashin yabawa ga matashiya a bisa abubuwan da take yi ga iyayenta ko mijinta.

20. Kariya daga tsoro ko fargaba.

21. Tsayawa a kan ra’ayi domin cimma wani buri.
22. Kora daga aiki ko makaranta.

23. Ƙyashi da hassada da kushe.

24. Zaman birni (ka zo na zo) babu ruwan kowa da kowa.

25. Rashin adalcin shugabanni wajen rabon arzikin ƙasa.
26. Cunkoso a gidaje musamman gidan haya.

27. Wuraren ayyukan gayya da kalankuwa da bukukuwan noma.

28. Bukukuwan salla da mauludi da kuma kirsimeti.
29. Son yin hutu ko barci a ƙarshen mako.

30. Gudun kada yarinya ta zama saniyar ware a cikin ƙawayenta masu sha.

31. Don tallata sana’ar su ta sayar da kayan maye da sauransu.

32. Don a sami ƙarfin ɗaukar kaya.

33. Akwai waɗanda ba su ma san dalilin da ya sa suke sha ba.

34. Bin ƙwaƙƙwafi (son a san yadda ake ji in an sha ƙwaya)

35. Son tafiya da zamani.

36. Rashin aikin yi.

37. Rashin kusantuwar ‘ya’ya da iyayensu.

38. Karance-karancen littattafai da mujallu da jaridu da ƙasidu da kallon finafinan baɗala.

39. Mummunan tunani a rayuwa.

40. Samun abubuwan maye barkatai a ckin al’umma, ba tare da wahala ba a cikin unguwanni da loko da sako da kan tituna da kuma kasuwanninmu, cikin farashi mai arha wanda kowa na iya sayensa.

41. ‘Yan siyasa da ɓata gari a cikin al’umma, suna amfani da wasu daga cikin dalilan da muka bayyana halaye da ɗabi’un matasa (a sama) su samar musu da kayan maye.

42, Rashin kwanciyar hankali a cikin iyali.

43, Rashin tarbiyya ta addini.

44. Sayarwa da tallatawa a kusa da makarantu da gidajen jama’a.

Da yawansu in mayen ya sake su sai kuma su ji haushin abubuwan da suka yi a lokacin da ba su da cikakkiyar natsuwa ko hankali, musamman idan an gaya musu ire-iren abubuwan da suka yi a lokacin da suke cikin mayen.

Kuma in ka ce wane daɗi suke ji in sun sha sai ka ji sun ce, ba wani daɗi illa dai kawai biya wa rai buƙata, kamar shan taba ne babu wani daɗi sai dai nishaɗi lokacin da kake busa hayaƙi sama.

Wannan bayani an ciro shi ne daga litttafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.

Don karanta Matakan Shiga Shaye-shayen Miyagun Ƙwayoyi danna nan

Edita@rumasau-kallamu

 

labarin da ya wuceMatakan Shiga Shaye-shayen Miyagun Ƙwayoyi
Labarin na GabaAyyukan Ta’addancin Matasa A Kano: Aure, Yawan Haihuwa Da Tarbiyya A Wata Mahanga
Ado Ahmad Gidan Dabino
Shahararren marubucin littattafan Hausa ne a Najeriya, sannan mai shiryawa da bayar da umarni sannan ɗan wasa ne a shirin finafinan Hausa kuma ɗan jarida. Tare da shi aka kafa wasu ƙungoyoyi na marubuta da masu shirya finafinai. Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta karrama shi da lambar yabo ta ƙasa mai taken, Member of the Order of the Niger (MON) bisa hidimta wa jama'a da yake yi a cikin ayyukansa.