Duk halittu sukan faro ne mataki bayan mataki har zuwa cikar halitta. Haka abin yake ko a mu mutane! Matakin farko shine bayan shigar ciki muna farawa da matakin “Ɗan tayi” wato ’embryo’ wanda a karshe wannan embryo din ne zai girma a sami dukkan sassan jiki dake nuna cikar halitta walau na jinsin Mace ko Namiji.
Wasu muhimman sassa da ke rarrabe Namiji da Mace shi ne zubin al’aurarsu da bayyanar nonuwa a ƙirji in an cimma lokacin balaga.
Sashin halittar al’aura, mazantaka da iya yi wa Mace juna biyu a namiji shi ake kira da “Mel rifurodoktib sistem” yayin da sashin zubin halittar mace, haila, da goyon ciki ake kiransa da “Fimel Rifurodoktib Sistem”
Shi wannan sashi na FIMEL RIFURODOKTIB ya ƙunshi sassa irin su: Ƙwayayen haihuwa, mahaifa wato uterus, bakin mahaifa, bututun wucewar ƙwai da kuma can cikin farji…. Wannan sassa suke haɗuwa su samar da ɗa a gaba.
Toh sai dai ina son mu sani wannan sashin yakan zamto an sami tangarɗar halitta tun sanda mace take jaririya a ciki amma sam ba a san da matsalar ba sai bayan da ta girma ko kuwa ta yi aure ma.
KU SANI:
- Akwai macen da ke zamtowa tana da mahaifa wato uterus amma sam ba ta da ovaries. Sashin da ke samar da su bai tsiro ba, ta waje za ka ga kyakkyawar mace da nonuwa da komai to amma fa ta ciki tana da wannan naƙasun, don haka wannan macen ba za ta taɓa iya haihuwa ba. Shi yasa galibi sai bayan aure an ji ba labari an zo gwaji ake ganowa.
2. Akwai macen da ke kasancewa maimakon kwanson ƙwayayen haihuwa guda biyu na hagu da dama…ita ɗaya gareta, Amma ba ta da mahaifa, ko kuwa mahaifar wani yanki ne ba complete ba ce… Wannan ma komi kyanta ta waje ba za ta taɓa iya haihuwa ba sai haƙuri.
3. Akwai macen da akan haife ta da mahaifa ƙwaya biyu wato Biconuate. Wanda hakan ke nuna ko an sami ciki to aljihu ɗaya zai shiga kuma akwai hatsarin cewa cikin ba lallai ya zauna zuwa haihuwa ba, akwai hatsarurrukan da ka iya sa a rasa shi.
4. Akwai macen da akan haife ta da rabin mahaifa, ita ma wannan sai can gaba ta gane ba za ta iya ciki ba ballantana ta haihu.
5. Akwai me ƙofar farji biyu.
6. Akwai macen da ba ta da farji, Eh ga shape da komi amma gajere ne, babu zurfi, ba hanya. Irin wannan in miji ya matsa mace ta hau kuka saboda azaba ya zaci ko a matse take tunda mutanen mu akwai wawan tunani wani lokacin. Bai san “Blind ended” vagina gareta ba.
Mace ga nonuwa ga komi amma babu hanyar farji, musamman wannan na daga abinda ke janyo ciwo ko azaba yayin saduwa a mace me sabon aure. Sai daga baya a gane ba hanya ne kuma ba ta da cikakkiyar mahaifa don haka ba za ta iya ɗaukar ciki a haihu da ita ba, wanda galibi wasu Mace ba ta iya faɗawa miji wannan don ba lallai auren ya ɗore ba. Sai dai irin wannan mukan yi aiki Vaginoplasty mu ƙirƙiri hanyar farjin da za a ji daɗi da ita, amma dai ba batun haihuwa.
Wannan matsalolin duk ta waje ba za ka iya sanin akwai su ba. Domin ta waje za ka sami mace cikakkiya a tsaye, a dire, nonuwa, hips, da kuma farjin in ka kalla da ido. Abin ta can ciki ne. Illa iyaka sai dai wasu da akan samu duk da ga Nonuwa ga cikar sura ta mace amma sam za su zo nema akan ba su taɓa ganin haila ba.
Sun kai shekaru 17, 18, ko 20 amma mace tace har yau ba ta fara haila ba, ko kuwa ga alamu tana ji duk wata a keɓantattun kwanaki kamar haila amma babu jinin. Galibi wannan daga nan ne sai mun bincike sai mu gano ba ta da uterus. Infact wasu a nan muke tantance ta waje mata ne amma ta ciki maza ne.
Wannan matsalar na ga ana ɗan samunta kwanan nan, gwanin ban tausayi, mutum yana ganin ya auri kyakkyawar matarsa amma ƙarshe farjin ne kurum ta ciki bayan scan za ka samu ba ta da mahaifa, ko ga mahaifa amma ba ovaries, ko kuma ga farji ta waje ras amma ba zai shigu ba. Duk ba abubuwa ba ne masu daɗi domin ba yadda za kai su haihu. Mai dama-dama ita ce me ovaries. Don akan iya cirar ƙwan a dasa a mahaifar wata macen ta haife mata. Duk da mu Musulmai hakan ya haramta garemu.
Don haka kafin ka cewa babyn nan Yes akwai tarin abubuwan nazarta, ba iya Genotype ba ne, kasancewa mace na haila wannan ka kore wasu abubuwan da dama. Amma hakan bai kore matsalar. Haka abin yake ga wanda kan zo da ƙorafin rashin haihuwa sai bayan gwaji a gano mace ba ta cika ba a halitta ta ciki. Irin wannan yanayi na mace shi muke kira da GYNAETRESIA ko MÜLLERIAN AGENESIS.
SHI YASA NAKE JAN HANKALINMU
Lallai Yan-uwa mata ku dena watsi da magungunan FOLIC ACID da ake bai wa mata a watanni ciki na farko komi rashin daɗin warin su a daure a sha, daga cikin aikinsa shi ne ba da kariya daga irin wannan matsalolin dama sauran larurori da kan shafi jarirai.
Domin karanta Mata Ku Ba Ni Kunnenku danna nan
Edita; Rumasa’u M. Kallamu