Ma’anar Gara Da Rabe-Rabenta

0
11

Wata kyauta ce, wacce iyayen amarya ko mai jego suke kai wa ‘yarsu, don amfanin yau da kullum. Wato wasu kayayyaki ne, wanda iyaye mata suke kai wa ‘yarsu bayan an watse daga biki, ko kuma idan mace ta haihu, sai a kai mata kayan da za ta sanyawa jariri kafin ranar suna, shi ne ake kira “kayan agwaja”, idan kuma bayan suna ne, to ana kiransu da suna “kayan gara ne”.

Rabe-raben Gara 

Bisa ga al’adar Bahaushe, yana da gara iri bakwai, kuma kowacce da dalilin yin ta. Misalin;

1. Garar amarya:   Dalilin yin aure.

2. Uwa ta waiga:   Bayan an kai garar farko ta aure.

3. Garar kayan salla: Dalilin bikin salla.

4. Garar haihuwa: Dalilin haihuwar mace (ita kuma wannan ta kasu gida biyu, akwai wacce ake kai ta kafin a yi suna da kuma wacce ake kai ta bayan an yi kwanaki arba’in da haihuwa).

5. Garar yaye: Dalilin yaye abin da aka haifa.

6. Garar Kaciya: Dalilin yi wa yaro kaciya, wanda mafi yawanci kakanni suke yankawa ɗan-kaciya kaji, don rage masa raɗaɗin kaciya.

7. Ka-fi-mai-kora: Dalilin yi wa mace kishiya.

Danna nan don karanta Aure a ƙasar Hausa

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceNi’imar Da Allah Ya Yi Wa Mutane Ba Tare Da Sun Fahimta Ba
Labarin na GabaRabe-Raben Auren Hausawa