Babban abin da ya fara ragargaza Afrika kamar yadda muka faɗa shi ne cinikin bayi. An yi rubuce-rubuce da yawa a kan cinikin bayi da yadda abin ya canja da yanayinsa, da su waye suka yi. Wane irin tsarin cinikin aka yi kafin Turawa su zo su kawo nasu tsarin, saɓanin abin da mutanen Afrika suka saba da shi.
A tarihin Afrika kamar na sauran nahiyoyi akwai bayi a tsarin zamantakewa. Bayi ana amfanin da su a harkokin gida a matsayin ma’aikata. Kafin zuwan baƙin Larabawa da Turawa, ba a ɗiban bayi ana cinikinsu zuwa ƙasashen wata nahiyar.
Turawa su ne suka mai da Afrika nahiyar ɗiban bayi kamar dabbobi ko kayan gona. Abin da Turawa suka yi shi ne, sun mayar da cinikin bayi babbar sana’ar samun kuɗi a rayuwar mutanen Afrika.
Bayi a ƙasashen Afrika da na Musulmi suna haɗewa da sauran mutanen ƙasar ko garin da ake so, ta hanyar ‘yantar da kansu idan suka yi na misali tsahon shekaru. Kuma ‘ya’yansu mata ana mayar da su ƙwara-ƙwarai har su haifi ‘ya’ya wanda za su zama ‘ya’ya ba bayi ba.
Wasu daga cikinsu su zama manya mutane a masarautu. Wasu ƙasashen Afrika su na da irin wannan tsarin, yadda an rawaito cewa a Ife akwai wani Oni da yake Bawa ne a da, saboda haka wannan babu shi a tsarin bautar da Turawa suka kawo.
Turawan Portugal yadda suka zo da bautar su, kawai ɗiban mutane ake yi a je a bautar da su kamar dabbobi su yi aiki. Wannan shi ne tsarin da su Portugal suka kawo wa Afrika. Wannan sabon abu ne babu shi, ba a san shi ba, su Portugal su suka fara yin wannan. Sun samu ci gaba na yanayin gane duniya da su Vasko da Gama suka fara tafiye-tafiye.
A dalilin haka suka fahimci cewa akwai damar ɗiban bayi a kai su wata ƙasar su yi aiki don ɗiban dukiya ko yin noma. Turawan Portugal sun yi tsari irin na Rumawa, na kafa ƙasashe (wato colonies da turanci). A wannan tsari ana ɗiban mutane a kai su ƙasar su zauna din-din-din suna aikin noma da na haƙo ma’adanai. Sun kafa ƙasar Brazil da irin wannan tsari, suna ɗiban bayi daga Afrika suna kai wa can. Wannan ƙasar ta Brazil ta fi kowacce a nahiyar Amerika ta kudu.
Turawan da aka tabbatar sun fara yin cinikin bayi a matsayin sana’ar samun kuɗi su ne Turawan Portugal, an yi shekaru 450 ana wannan mummunan ciniki. Turawan Portugal sun ajiye bayanai akan yadda suka yi wannan cinikayya a ma’aikatun (archives) tarihin su. Wannan bayanan na tun farkon zuwansu Afrika ne a shekarar 1472.
Samun wannan ya sa masani Dr. A.F.C. Ryder ya yi rubutu masu mahimanci. Ryder (1959: 294-321) ya fassara bayani daga harshen Portguese zuwa Turanci na tafiyar wani jirgin ruwa a shekarar 1522 wanda ya ɗauko bayi daga kogin Forcados a Niger Delta.
Ryder ya rubuta littafi, a ciki ya duba matsayin abubuwan da aka ajiye a ƙasar Portugal daga shekara 1522. Wannan ya ba da damar cewa a yi dogon bincike a ga yadda irin tsarin bautar su yake, kuma kamar yadda muka sani, bautar su ta bambanta da irin tsarin bautar da ake yi a Afrika.
Su Turawa daban ne, sun shigo da wani tsari daban, kuma ba yadda za a yi a ce su bayin nan an mayar da su mutane a cikin wannan al’ummomi, saɓanin yadda yake a ƙasashen Afrika da ƙasashen musulmi, abin da ake nufi waɗannan ƙasashen Afrika da ƙasashen musulmi, ta yadda idan mutum bawa ne yana da damar da zai daina bautar nan ya shiga har ya zama wani abu, kamar yadda aka gani cewa, mata idan mutum yana da baiwa zai iya aurenta kamar yadda aka gani a shari’a zai iya mayar da ita ƙwarƙwara kuma.
Sun ɗebi mutanen ƙasarsu sun kai, a Afrika nan kusa da Najeriya, ya zo ya samu wani waje ana ce masa Satomi D’Principle, nan ma ya dinga ɗiban mutane yana kawo su, har ma ya yi wani abin da ba a taɓa yi ba a tarihin ɗan Adam shi ne ya fara yin sa. Ya ɗebo mutane waɗanda suke sun yi laifuffuka ya zo ya ajiye su.
Ya ɗebo Yahudawa waɗanda aka fara yin rigima da su a can aka fara kakkashe su, sai ya ɗebo wajen dubu biyu ya kawo su Satomi, yake ɗebo mata daga wurin da ya zama Najeriya ta yanzu wato Kudancin Najeriya, sai a haɗa su da waɗannan fararen fata Yahudawa sun hayayyafa.
Wasu Yahudawan da yawa sun mutu, amma ɗari shida sun kai labari, to haka ya kafa wannan ƙasa, shi wannan Sarki na Portugal na wannan lokaci ya yi wannan ne domin ya samu mutanen da za su ci gaba da yi masa cinikayya ta bayi a nan Afrika, saboda idan waɗannan mutane suka zo suka haɗu da mutanen Najeriya waɗanda suke da asalin su ‘yan ƙasa ne to rashin lafiyar su zai ragu.
Wannan sabuwar dabara ce shi wannan King Jour II ya kawo ta wanda ya yi zamani a 1515, ya ɗebi waɗannan mutane ya kawo su. An samu wannan cikakken labari da wani mutuminsu ya rubuta shi, shi kuma wannan Sarkin dai ya yi amfani da wannan mutane duk ga bayanin su (record) ɗin. Wannan abin da ya fara shi ne ya ba su damar su kafa wannan ƙasa ta Satomi N’Principle a wannan wurin da suke can a tekun Atlantic.
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu