MENE NE KISHI? 

0
34

Kishi shi ne, sosuwar zuciya da ɓacin ran da suke jawo fushi, a dalilin tarayyar da wani ya yi da wani, a kan abin da wanin ya keɓanta da son sa, ko mallakar sa. 

Mene ne Asalin kishi? 

Asalin kishi shi ne ƙyama da ƙiyayyar munanan abubuwa. 

Mene ne Abin da Yake Jawo Kishi? 

So da ƙaunar wanda aka yi kishi domin sa shi ne ke jawo kishi. 

Mene ne Matsayin Kishi? 

Kishi wata maɗaukakiyar halayya ce, kuma wata kyakkyawar sifa ce da ta dace da a siffatu da ita. 

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

Gaske ne kishi na da Fage-fage? 

Na’am, gaske ne, kishi yana da fage-fage, da ake yin sa da aiwatar da shi a cikinsu, ga jerinsu kamar haka: 

  1. Kishi a fagen tsare addinin Allah da dokokinsa. An karɓo hadisi daga Aisha (Radiyallahu An ha) ta ce: “Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bai taɓa dukan wani abu ko wata mata ko wani hadimi da hannunsa ba, sai dai a yaƙi saboda Allah, don ɗaukaka addinin Allah, kuma ba a taɓa munana masa ba ya ɗau fansa, sai dai fa in an keta hurumin wata dokar Allah ne, sai ya ɗau fansa saboda Allah Maɗaukaki”. 
  2. Kishi a fagen tsare mutuncin kai. 
  3. Kishi a fagen tsare darajar iyalai kamar mai gida ya sa tsaron da iyalansa ba za su samu damar yin shiga ta rashin mutunci ba, ko kuma yin barkwanci da maza.

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

KISHI IRI NAWA NE? 

Kishi Iri biyu ne: 

  1. Kishin Allah ga bayinsa. 
  2. Kishin bayi a tsakaninsu. 
YAYA KISHIN ALLAH YAKE? 

Kishin Allah shi ne, fushin da Allah yake yi da muminin bawan da ya saɓa masa, da kuma ƙyamar da yake yi wa mummunan aikin da bawa ya aikata. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan 

labarin da ya wuceDamakwaraɗiyya A Tsakanin Dabbobi
Labarin na GabaMenene Bambanci Tsakanin Kishin Allah Da Na Bayinsa?