Yadda Zaku Gyara Zamantakewar ku Ta Aure

0
77

1.Kyakkyawan yanayi

Bincike ya nuna ma’auratan da suke sabunta yanayin rayuwarsu tayau da gobe sunfi samun zaman lafiya.Misali zuwa sabbin gurare, cin abinci na musamman ko fita kallon wani abun tsorone ko na nishaɗi tare. Motsa jiki ko wasanni tare Ziyartar wani guri da Basu taɓa zuwa ba 

2.Shafar juna

Ku kasance Kuna iya kusantar junanku a Koda yaushe bawai Sai lokacin kwanciya ba. Kina iya shafar wuyan mijinki idan Yana Miki girki. Ko shafar gashin kansa a lokacin da kuke zaune Kuna kallo. Riƙe hannun juna idan Kuna tafiya tare. Sumbantar kuncinsa a bazata. Ko shafar bayansa a lokacin da yake wani yanayi Mara daɗi.

Domin karanta Yadda Za Ki San Kanki Kafin Ki Yi Aure Danna nan

3.Tattaunawa Gameda kwanciyar aure

Yana da kyau Kuna canza yanayin salon kwanciyarku ko tattaunawa gameda abunda yake saku Jin daɗin kwanciyar ko wani Abu dayake so kina Masa da zaisa yaji daɗi misali: Chanza salon kwanciya ko kuje ɗakin hotel

Idan Kuna da yara ku bada su inda za a kula dasu don ku samu isasshen lokaci

  • Yiwa juna tausa.
  • Sabunta kayan bacci.
  • Samun ingantacciyar kwanciya da gamsuwa bawai yawan kwanciyarba
  • Sumbantar mijinki Tana da tasiri kwarai wajen ƙada danƙon ƙauna tsakaninku
  • kuma Yana sawa ki janyo hankalinsa gareki.kiyi ƙoƙari kina sumbantar mijinki ko da na tsawon sakan 10 ne a rana.

Domin karanta Abubuwa Da Ya Kamata Mace Ta Kiyaye Lokacin Al’ada Danna nan 

labarin da ya wuceYadda Zaki Sa Mijinki Ya Qara Sonki
Labarin na GabaYadda ake Jollof Rice
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.