Tsarin Iyali { Family Planning) Rubutu Na (2) (Intrauterine Device

0
112

Aci gaba da kawo maku bayani kan tsarin iyali na zamani, yau za muyi bayani akan INTRAUTERINE DEVICE wato tsinke ko zaren mahaifa.

Kamar yadda zaku iya ganin sa a hoto dake kasa, wannan abune na roba wanda kan iya zama mai nade da waya a jikin sa ko wanda babu, da ake sawa mace a cikin mahaifa domin hana ta daukar ciki.

Ya Ake Sa Shi?

Ana sashi a asibiti cikin abinda bai wuce minti 10 ba, ana sashi ta cikin al’aura zuwa mahaifa, baya bukatar yanka jiki.

Lokacin Aikin Sa

Duk da yake shima kala kala ne, amma yana kaiwa har shekara 4 yana aiki, sai dai duk lokcin da mace tayi ra’ayi ko kuma saboda wata matsala to zata iya cirewa.

Kamar ko wanne irin magani, shima yana da nasa side effect din .

A rubutu na gaba za mu yi maku bayani akan Condom da kuma murfin bakin mahaifa.

Domin karanta Bayani Akan Tsarin Abinci Ga Masu Ciwon Suga (Diabetes Mellitus) Danna nan

 

labarin da ya wuceBayani Akan Tsarin Abinci Ga Masu Ciwon Suga (Diabetes Mellitus)
Labarin na GabaKawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya