Folic acid Nau’i ne na vitamin B9, kuma yana ɗaya daga cikin vitamin da aka narkar da shi a cikin ruwa (Water-Soluble Vitamins) wanda ake samu a cikin abinci da yawa, mafi mahimmanci daga cikinsu shi ne abinci mai ganye, kuma ana ƙera shi a matsayin ƙwaya.
ƙwayar Folic acid ( Folic acid tablets) wasu ƙwayoyi ne ƙanana yellow mafi yawa yana zuwa da nauyi 5 (5mg).
Ana amfani da ita wajen magance ƙarancin jajayen ƙwayoyin jini wanda rashin sinadaran iron ya kawo.
Waɗanda Ke Da Buƙatar Amfani Da Folic Acid:
- Mata masu juna biyu
- Mata masu shayarwa.
- Masu ciwon cutar hanta.
- Masu ciwon sikila.
Menene Hikimar Ba Wa Mata Masu Juna Biyu Folic Acid Ko Da Ba Su Da Matsalar Ƙarancin Jini?
Folic acid yana ɗaya daga cikin muhimman sinadaran Vitamin da mata masu juna biyu suke buƙata, saboda amfaninta a jikin su.
Ga Kaɗan Daga Cikin Amfanin Sinadaran Folic Acid A Jikin Mata masu Juna Biyu:
Sati ukun farko na ɗan tayi a ciki , shi ne lokacin da wasu a ƙwayoyin halittarsa suke haɗuwa don Samar da ginshiƙi a kan yadda wasu sassa da kuma tsare-tsaren jikinsa za su kasance, saboda haka wannan lokaci ne mafi haɗari a yadda gobensa za ta kasance ta yadda matsala a haɗuwar wasu ƙwayoyin halittar, za su sa ko da ya yi tsawon rai to zai rayu ne da matsala ta har ya mutu. To folic acid yana taimakawa wajen haɗuwar waɗannan halittun dai dai.
Domin karanta Ciwan Farfadiya (Epilepsy/Seizure) Danna nan
Birth defects: Binciken masana ya nuna sinadaran folic acid yana ba da kariya daga haihuwar yaro mai nakasa.
Folic acid deficiency: Yana kare mata masu juna biyu daga samun ƙarancin sinadaran folic acid.
Ƙarancin Sa Zai Iya Kawo Matsalar:
- Zubewar ciki
- Naƙuda kafin lokaci
- Mutuwar yaro a ciki
- Mutuwar uwa.
Heart and blood vessel disease: Binciken masana ya nuna sinadaran folic acid suna taimaka wajen daidaita sinadaran homocysteine wanda hakan zai iya ba da kariya ga cututtakan zuciya.
Cancer: Binciken masana ya nuna sinadaran folic acid yana iya rage hatsarin kamuwa da ciwon cancer.
Depression: Binciken masana ya nuna sinadaran folic acid yakan iya taimaka wajen magance matsalar damuwa.
Dementia: Haka nan akwai ƙishin-ƙishin na yana taimakawa wajen ba da kariya daga cutar ƙwaƙwalwa wanda yake saka mantuwa
Wassu Daga Cikin Amfanin Ta:
- Yana gyara fata
- Yana gyara gashi
- Yana saka cin Abinci
- Yana kare matsalolin jijiyoyi.
- Yana taimakawa kula da kyakkyawan ƙwaƙwalwar ajiya.
Idan kin yi amfani da ƙwayar folic acid yana kawo miki waɗannan alamomi maza ki dakatar da ita sannan ki je ki ga likitanki.
- Ƙaiƙayin jiki
- Ƙurajen Jiki
- Canza launin fata
- Riƙewar numfashi
Idan kina amfani da waɗannan magunguna kada ki ki sha folic acid sai kin shawarci likitan ki.
Anticonvulsants: Magungunan jijjiga kaman su fosphenytoin (Cerebyx), phenytoin (Dilantin, Phenytek), primidone (Mysoline).
Barbiturates: Magungunan da suke aiki a jijoyoyi wanda suke kai sako ga ƙwaƙwalwa.
Antimalarial: Magungunan cutar cizon sauro.
Methotrexate (Trexall): Magungunan da ake amfani da shi domin magance matsalar cancer.
Abinci Mai ɗauke Da Sinadaran Folic Acid A ciki :
- Koren ganye da kayan lambu
- Nama da Kifi
- Wake
- Hatsi
- Dawa
- Brown Shinkafa
Domin karanta bayani akan Ƙurajan Pimples Danna nan