Yadda Ake Tarbiyyar Yara

0
2202

Yadda ake tarbiyyar yara shi ne, aikata dukkan abin da ake koya musu. Wato iyaye su dinga aikata irin ayyuka da suke umartar su da su aikata.

Ya kamata iyaye su zama kyakkyawan misali, abin koyi ga ‘ya’yansu.
Haka ma ya zama wajibi ga iyaye su san ilmin yadda za su tarbiyyanci yaransu.
Ba da tarbiyya ta zama dole, wanda duk bai yi wa ‘ya’yansa ba. Zai amsa tambaya a gobe ƙiyama.
Duba Allah Maɗaukaki Yana cewa :
“Ya ku waɗanda kuka ba da gaskiya, ku tsare kanku da iyalanku daga wuta “.
( Tahrim:6)
Annabi ( SAW) ya ce :“Kowannenku makiyayi ne, kuma Kowannenku abin tambaya ne ga abin da ya kiwata. “
( Bukhari da Muslim)

Haƙƙoƙin ‘ya’ya a kan iyaye su ne:
So da ƙauna, da kula da lafiyarsu, da wadata su da sutura , ba su ilmi , da
koya musu halayen kirki, da ɗora su a kan
sana’a.

MATAKAI NA TARBIYYAR YARA :

1 – ZAƁAR UWA TAGARI :
Uwa ita ce komai a tarbiyya yara. Uba ya dage ya samar wa ‘ya’yansa wa tagari.
2 – ZAƁAR MAKARANTA :
Ya zama wajibi a tantance da irin makarantu da suke kula da tarbiyya ta addini Musulunci. Ba wai zallar karatun boko ba. Me suke koyarwa? A duba su Wane ne malaman?
3 – ZAƁO UNGUWA : Zaɓo unguwa da ake zaman Lafiya. Kuma mafi yawan mutanen unguwar, su zama suna da ƙoƙarin tarbiyya.
4 – ADDU’AR IYAYE : Iyaye su zama masu yawan sa wa ‘ya’yansu albarka. Addu’ar iyaye karɓaɓɓiyya ce a kan ‘ya’yansu.
5- SADUWA : Kulawa da ladubban haɗa shimfida .Yin addu’a kafin shimfida a koyaushe.

Manzon Allah (SAW) ya ce : “Hakika da ɗayanku zai yi nufin ya tara da iyalinsa ya ce, da sunan Allah, Ya Allah! Ka nisantar da Shaiɗan daga gare mu, kuma ka nisantar da Shaidan daga abin da ka azurta mu. To, haƙiƙa, idan aka ƙaddara yaro a cikin wannan saduwa, Shaiɗan ba zai cutar da shi ba, har abada “.
( Bukhari).

6 – CIKI : Irin yadda uwa take yi na da tasiri ga yaro da za ta haifa. Yana da muhimmanci ta ɗabi’antu da yawaita karatun Qur’ani, da Ambaton Allah. Cin lafiyyen abinci da barin kallace-kallace, da waƙe-waƙe. Domin ƙarin bayani a kan yadda za ki gane kina da ciki (juna biyu) danna koren rubtun
7 – SUNA : Wajibi ne ga iyaye su zaɓar wa yaro suna kyakkyawa. Kamar sunan Annabawa ko sahhabai. Domin yaro ya sami albarkar mai sunan.
A karshe dai iyaye su gane babu wani gata da za su yi wa ɗansu, sama da kafa shi a kan kyakkyawar tarbiyya.
Za ka yi iya ƙoƙarinka, sai ka fawwala Allah lamarinka, ka roƙe shi ya shirya ma yara.
Allah Shi ne mafi sani.
Duba yadda tarbiyyar Hausawa take a zamanin da.
Litattafai da aka duba

Ya ake Tarbiyya A Musulunci.

labarin da ya wuceNa Sha Ruwa Bayan Tayar Da Iƙama A Kan Kuskure, Ya Hukuncin Azumina?
Labarin na GabaYadda Ake Gyaran Jiki Ya Yi Laushi Kuma Ya Yi Kyau
Amin Yusuf Gwamna
Sunana Amina Yusuf Gwamna Shugaba Kungiya Mace ta Musamman da ke kokari inganta rayuwar Mata da kanana Yara. Marubuciya litattafai hausa. Kuma Shugaba Makarantu Abu-Nusaiba Da ke Ring road, kano.