Saboda irin himmar makaranta a tsarin tsangaya, alarammomi kan lazimtawa almajiransu yin karatu a wasu lokutan daban-daban bayan karatun safiya da maraice kamar haka:
Tashe:-
Akan tashi almajirai cikin dare jim kaɗan bayan fara barci da niyyar cigaba da kwami ko kuma tilawa. Wannan shi ne tashe ko jadare. Yanayin karatu a tsangaya kuwa kan ɗauki siffofi da dama musamman ma don ƙarfafa juna misali:-
Musaffa:- Makarantan da suka tara tilawa kan haɗu a wasu lokuta musamman da dare su yi ta karatu a yanayin karɓa-karɓa ma’ana ana zagaya da’ira da tilawar sumuni-sumuni ko rubu’i-rubu’i. Da haka har a sauke ko kuma zuwa wurin da ya sauwaƙa. Da yawa makaranta kan kwana suna zuba tilawa a yanayi irin na musaffa ko tuƙuri.
Ranakun Al’hamis da Juma’a su ne ranakun hutu a tsangaya. Wannan kuwa ya samo asali ne tun farkon Musulunci a lokacin da Sayyadina Umar ya yi tafiya ƙasar Sham kuma ya Jima Bai dawo ba. Wannan ya sa mutanen Madina cikin damuwa. Ko da labarin isowarsa ya iske su, sai kowa ya fito zuwa tarbo shi. Wannan ya sa yara ‘yan makarantar allo ba su yi karatu ba yini guda.
A ranar Juma’a kuwa Amirul Muminina ya iso. Don haka aka ba su hutu kuma ya Zama hutun makarantunmu na Alƙur’ani.
Domin karanta cikakken bayani akan Azuzuwa Da Kashe-Kashen Makaranta A Tsangaya danna nan.
Domin karanta cikakken bayani akan Ma’anar Tsangaya danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.