Makaɗa Abdu Kurna yana daga cikin makaɗa na ƙungiya; waɗanda suka yarje wa wasu mataimakansu su dinga zuwa taɓe na yin waƙa; wato gayaunar kiɗa.
A lokacin da Sarkin Kiɗa Abdu Kurna ya lura wazirinsa Musa Ɗanƙwairo ya laƙanci waƙar baka; sai ya ba shi faraga ya dinga fita da abokansa yawon rera waƙoƙi lokaci bayan lokaci wato sa’i da wata bukata.
Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya yi waƙoƙin noma da yawa lokacin gayauna. Daga nan ne Abdu Kurna ya ba shi izini ya dinga haɗawa da waƙoƙin masu Sarauta, musamman ma ‘ya’yan Sarakuna.
Waƙar Gayauna ta Sarauta wadda Musa Ɗanƙwairo ya fara shiryawa da aiwatarwa da rerawa da sadarwa; ita ce wadda ya yi wa Abubakar ɗan Sarkin Noma Usman na Birnin Ƙaya.
Ga wasu ɗiya na waƙar:
G/Waƙa: Ɗan Sarki a gode maka,
: Jikan Dodo Ɗangwamma.
Jagora: Ya tafi daji ba shi komawa,
: Kullum daƙe duƙe sai duƙe,
‘Y/Amshi: Gyado mai ƙoƙarin gabce,
: Ɗan Sarki a gode maka,
: Jikan Dodo Ɗangwamma.
Jagora: Mijin Ɗiya jikan Nomau,
: Gwarzon Ango karsanin Ali,
: Gungaman Iro ɗan Jatau,
: Kullum daga duqe sai duqe,
‘Y/Amshi: Gyado mai ƙoƙarin gabce,
: Ɗan Sarki a gode maka,
: Jikan Dodo Ɗangwamma.
(Waƙar Musa Ɗanƙwairo 30 ta Abubakar Birnin Ƙaya)
Domin karanta cikakken bayani akan Sauya Akalar Kiɗan Gado Zuwa Na Fada Da Na Game-Gari danna nan.
Domin karanta cikakken bayani a kan Gudumawar Waƙoƙin Baka na Situdiyo Wajen Haɓaka Tattalin Arziki danna nan.
Wannan bayanin an ciro shine daga Littafin; Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun A Aiwatarwa Da Sadar Da Waƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.