Ɗabi’un Makaranta da Halayensu Cikin Zamantakewar Tsangaya

0
502

Ɗabi’un makaranta Alƙur’ani da irin halayyarsu ko kuma yanayin tunaninsu game da rayuwa (world-veiw) wani fage ne mai faɗi da muhimmanci wajen sanin haƙiƙanin tsarin zamantakewar tsangaya da irin wayewa ko gogewa da almajirai ke samu don faɗawa gwagwarmayar rayuwa.

Bugu da ƙari kuma, abu ne mai ƙayatar da mai karatu, tare da ƙara masa son nazari kan tsarin tsangaya. Tunanin makaranta ya ginu ne bisa tushen ganin girman masu ɗauke da Alƙur’ani. Don haka, duk wanda ba shi da karatu, ba sa sha’awarsa. Al’adar Barebari ta nuna isa da rashin nuna gazawa, ta yi tasiri mai yawa ga tunani ko halayyar gardawa.

Akwai wasu ɗabi’u ko ta’adoji da makaranta a tsangaya suka yi tarayya, cikinsu tun daga kan ƙananan almajirai har zuwa kan gardawa da manyan alarammomi. Irin waɗannan ɗabi’u sun haɗa da zumunci da son juna da biyayya ga na gaba da ƙanƙan-da-kai da barkwanci da sauransu. Wasu ɗabi’un kuwa, an fi danganta su ga gardawa, misali son burgewa da ban dariya da taƙadaranci da son gayu da tsafta da dai makamantansu.

A wasu lokuta kuwa, za mu ga cewa ɗabi’un wasu makarantan sawa’un gardawa ne ko alarammomi ne sun dogara ne kan irin ɗabi’ar makaranci a karan kansa. ma’ana za a iya samun alaramma dattijo wanda bai bar halayya da ɗabi’un gardanta ba. Ɗabi’u irin su tsafta da son ado kuwa an fi danganta su ga gardawa, koda yake da yawa wasu dattijan cikin manyan alarammomi, za ka same su ba a raba su da tsafta da yawan son ado.

Mai yiwuwa mai karatu ba zai samu cikakken hoton rayuwa ko yanayin zamantakewar makaranta a tsangaya ba; har sai mun gutsuro wani abu daga hikayoyi da labarai da suka shafi waɗannan bayin Allah. Wasu labaran na nuna jarunta da juriya da zumunci da tattalli; wasu kuma suna nuna hazaƙa da kishin zuci da son burgewa da sauran su, don haka sai mun haɗu a sashe na huɗu cikin wannan ɗan littafi don mu ga waɗansu ‘yan misalai.

Abu ne mai matuƙar muhimmanci mu san cewa, makaranta musamman gardawa mutane ne masu naci da azama ko himma kan duk abin da suka sa a gaba ta yadda wahala ko wani tsanani na rayuwa ba ya hana su zarcewa, matuƙar dai akwai wannan buƙata tasu, misali da yawa za ka samu gari ana rashin abinci ko rashin wadataccen ruwa, amma sai ka iske ɗaruruwan gardawa maƙil a wannan gari, musamman in sun sami labaran cewa tsangayar na tashen tara makaranta ko akwai wani mashahurin malami, to kuwa su sun samu mashekari.

Gardawa masu himma, ba su cika son a san su a gari ba, domin hakan zai jawo musu yawaitar abokai, daga bisani kuma, hakan ta riƙa kawowa shagaltuwarsu da karatu cikas, wannan ya sa duk inda gardi ya fara samun irin wannan, to kuwa za ka wayi gari babu shi a wannan tsangaya, wannan ya sa ake yi masu kirari da “Gardi na inna mai ‘yan kaya a kwana da ku, ba a wayi gari da ku ba”.

Kasancewar galiban gardawa na cikin shekarun samartaka, wannan yasa suke da son a dama da su a duk wani abu da zamani ya kawo, kuma samari ke yayin sa. Misali da yawa za ka samu gardi mai almajirai a ƙarƙashinsa idan zai je kaɗar-raɓa, to sai ya shirya almajiransa, ya tura su zuwa garin da za su sauka, daga baya kuma sai ka gan shi ya bi su cikin wata irin shiga ta ‘yan birni da jaka mai tsada da gogaggen takalmi da gilashi ta yadda wani ba zai raina shi ba.

Wannan ya sa da yawan su na koyon boko, ba tare da sun je makaranta ba.

Gardawa sun shahara da neman na kai da iya tsimi da tanadi, don haka ma za ka same su da gwaninta wajen iya ɗinkin hula; yankan farce da makamantan sana’o’in da ba za su hana su karatu ba. Saboda yawan ƙanƙan da kai, kuwa zai yi wuya ka ji an kira makaranci da alaramma face ka ji ya ce, “Almajiri dai”.

Makaranta a yayin darasu kan nutsu su tara hankalinsu, don su nuna gyaran baƙi, kamme ko camme; kara ko kurne ko kuma gyaran wasali a allon ɗan uwansu. Wannan ya sa duk wanda ya sanya allonsa a gaban alaramma; kuma ya ɗauke ba tare da wani ya sa hannu a allon ba, to wannan ya yi babbar bajinta. Makarancin da ya sanya allo gaban alaramma, tun daga Baƙara har Nasi, ba tare da an ci gyaransa, ko da da ɗugon wani harafi ba; to akan ce wane ya sha fari.

Gardawa cikin makaranta ba sa ganin kowa da wata baiwa matuƙar ba mahaddaci ba ne.

Wannan ya sa da yawa suna da wata inkiya, alal misali, idan guda ya yi baƙo; to ragowar za su yi ta hidima da girmama wannan baƙo don tsananin kara. Domin su gano matsayin baƙon kuwa, don kada su ba shi matsayin da ba nasa ba; sai guda ya tattara turɓaya a ƙasa a fakaice, kamar yana wasa da ita. Da zarar gardin da ya sauki baƙon ya ga haka, to zai ɗau haske. Don haka sai ya cigaba da tattara wannan ƙasa yana ƙara mata tsini, ma’ana dai hakan take baƙon makaranci ne. Amma idan ba makaranci ba ne, to shi mai masaukin baƙon zai baje wannan ƙasa a fakaice, har sai ya ƙarar da ita; ma’ana dai Malam Baƙo ba kowa ba ne. Daga nan ne suke cewa wane “curinbaje” ne ko “bajencuri” ne.

Makaranta a tsangaya sun ginu bisa haɗin kai don gudanar da al’amuran tsangaya.

Wannan yasa kowanen su suke zuwa jeji don saro itacen hurawa a gargari. Irin wannan hidima ita ake kira mako. A waɗansu lokuta kuwa, za ka ga an tara wannan itace tamkar wata dalar gyaɗa. A lokacin da wutar gargari ke ci ganga-ganga, makaranta kan kewaye ta suna karatu suna gwali; ma’ana suna iza ta suna ƙara itace. Da yawa gardawa kan sallamawa wanda ya fisu naci. Irin waɗannan masu naci, za ka same su ko yaushe suna kwami; ko da kuwa an tashi daga karatu, kowa ya fashe an gaji. To su ba sa sarewa, Gardi mai irin wannan naci shi ake kira Buna..

Wani abu mai ban sha’awa game da makaratan musamman ma gardawa cikin tsangaya; shi ne irin duk fasahar da suke da ita wajen karatu da sana’o’i; da kuma sarrafa duk wani abu da ke kusa da su don ya zama mai amfani gare su. Mu ɗauki yadda suke yin gado mai hawa biyu ko uku da kara da itatuwa, ko kuma mu dubi irin ƙwarewar da suke da ita wajen ɗinkin hula; ko kuma launukan da suke haɗawa don yin zayyana a allunansu. Ko kuma tsayawar hannunsu wajen rubutu ko fitar da bayala bisa takardar Alƙur’ani.

A wajen gini kuwa, za mu ga yadda suke haɗa kiskalinsu. Har ma na tattauna da wani alaramma a Ƙaramar Hukumar Tudun Wada cikin Jihar Kano; wanda ya gina wani katafaren gini mai benaye da tagogi masu ado da fasalin gine-ginen ƙasashen Larabawa; ko Rumawa, abin dai gwanin ban sha’awa da mamaki.

Wannan alaramman ya bayyana min cewa ya yi wannan gini ne da hannunsa; kuma duk aune-aunen da ya yi, da zubin ganin ya yi shi ne daga tunaninsa da ƙirƙirarsa; ba tare da ya kwaikwayo daga wani waje ba, ko kuma wani ya gaya masa ba.

Domin karanta cikakken bayani a kan Asalin Yawon Bundi Ko Ƙaura Wurin Makaranta danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Asalin Sunan Kakan Manzon Allah(S.A.W) danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceAzuzuwa Da Kashe-kashen Makaranta A Tsangaya
Labarin na GabaLokaci Da Yanayin Sadarwa A Waƙar Baka