Ɓacewar Ashanar Hannu Ta Tazarar Haihuwa

0
183

Abu ne mai yiwuwa ashanar hannu wacce ake soka ta a cikin tsokar damtsen mace domin yin tazarar haihuwa (contraceptive implant), ta ɓace ta yadda idan aka zo cire ta, a kasa ganinta. Ana kiran wannan yanayin “implant migration” ko “deep insertion” a likitance.

Abubuwan da suke haddasa ɓacewar ashanar hannun su ne:

  1. Soka Ta A Can Cikin Tsokar Hannu (Deep Insertion): Idan ma’aikacin lafiya ya yi kuskuren soka ashanar hannun a can cikin tsokar damtsen mace, maimakon a kasan fatar hannunta, to , hakan zai iya haifar da ɓacewar ta, har a kasa ganinta a lokacin da aka zo cirewa.   
  1. Matsawa Daga Wurin Da Aka Soka Ta (Migration): Tsinken ashanar hannu zai iya motsawa zuwa wani ɓangaren tsokar hannun mace ko kuma wani ɓangaren jikinta daban. Abinda yake sanya motsawar shi ne yawan motsa hannun (frequent movement), ko, bugewa (trauma), ko takurewar tsokar (muscle contraction).
  1. Sauye-Sauyen Ƙibar Jiki (Weight Changes): Idan mace ta ƙara ƙibar jiki , ko kuma ta rame sosai bayan an sanya mata ashanar hannu, to, wannan sauyin jikin zai iya haifar da motsawar ashanar daga asalin gurin da aka soka ta. 
  1. Rashin Soka Ashanar Yadda Ya Kamata (Improper Insertion Technique): Idan ma’aikacin lafiya wanda ya yi aikin soka ashanar bai soka ta yadda ya kamata ba saboda rashin ƙwarewa ko kuma kuskuren sokawar, to, mai yiwuwa ne ashanar ta motsa daga wurin da aka soka ta.

Idan ashanar hannu ta motsa daga wurin da aka soka ta har aka kasa gane inda take a lokacin da za a cire ta, to, hanyoyin da za a iya bi wajen gano ta su ne: 

  1. Mammatsa tsokar hannun (Physical Examination): Ma’aikaciyar lafiya za ta mammatsa tsokar hannun a daidai wurin da soka ta da kuma tsokar kewayen wurin, har a gano ta.
  1. Ɗaukar Hoton Wurin (Imaging Techniques): Idan aka kasa gano ashanar hannun ta hanyar mammatsa tsokar hannun, to, mataki na gaba shi ne a yi hoton ultrasound scan na hannun. Wannan dabarar ta fi yin tasirin gano ɓataccen tsinken ashanar hannu, domin za a ganta ƙiriƙiri. Sa’annan wannan dabarar ba ta ƙunshi yanka jikin mace ba (noninvasive technique) wajen nemo ashanar.
  1. Yin Aikin Tiyata (Surgical Removal): Da zarar an gano wurin da ashanar hannun take, to, za a iya yin aikin tiyatar yanka wurin domin a cire ta. Yawanci akan yi allurar kashe raɗaɗi (anesthesia) idan za a yi aikin tiyatar.

Ana buƙatar idan mace ta sanya tsinken robar ashanar hannu ta tazarar haihuwa, to, ta riƙa shafa wurin lokaci-lokaci domin tabbatar da cewa ashanar ba ta motsa daga wurin da take ba. Idan kuma ta ji alamun cewa ashanar ta motsa, to, sai ta sanar da ma’aikatan lafiya domin ɗaukar matakin da ya dace cikin gaugawa.

Don karanta Contraceptive Implants : Ana Kiranta Ashanar Fata Da Hausa Wannan Wata Hanya Ce Da Ake Dasa Wani Roba Ƙarami A Hanun Mace

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceHani Akan Yin Gulma
Labarin na GabaWaƙar Ilimi