Ƙiyamul Laili (Tahajjud)

0
1175

Kiyamul Laili ko Tahajjud ita ce sallar nafila a cikin dare, bayan an farka daga barci a cikin dararen shekara, ba lallai sai a Ramadan ba.

FALALAR TAHAJJUDI

1) Allah Ta’ala ya ce: “Kuma bayin Allah su ne waɗanda suke tafiya cikin nutsuwa a bayan ƙasa, in wawaye sun yi musu magana sai su ce: “Aminci ya tabbata a gare ku” (Wato Allah ya ba ku haƙuri). Su ne waɗanda suke kwana suna sujjada, su na tsayawa ga Ubangijinsu” (Suratul Furƙan: 63 – 64).

2) Allaha (S.W.T) ya ce: “Haƙiƙa masu tsoron Allah suna cikin Aljannanta da ƙoramu. Suna masu karɓar abin da Ubangijinsu ya ba su, haƙiƙa sun kansance masu kyautatawa kafin wannan. Sun kasance suna yin barci kaɗan a cikin dare, kuma a lokacin sahur suna istigfari”.

3) Manzon Allah (S.A.W.)ya ce: “Ya ku mutane ku yaɗa Sallama, ku ciyar da abinci, ku sadar da zumunci, ku rinƙa sallah da daddare a lokacin da mutane suke barci, za ku shiga Aljanna cikin aminci”. (Tirmizi 1855, Ibn Majah 1334 Ahmad 751).
Ana iya yin ƙiyamul laili a farkon dare ko a tsakiyar dare ko a ƙarshen dare, ƙarshen daren shi ne mafificin lokaci.

wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Falalar Kiyamul Laili Da Amfaninta Ga Musulmi wanda shehu mansur dala ya wallafa domin karanta cikakken littafin danna koren rubutun nan.

labarin da ya wuceKar Harshe Ya Gushe Ba Tare Da Ambaton Ubangiji Maɗaukaki Ba.
Labarin na GabaSiffar Jikin Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam)