Jinin Haila (Jinin Al’ada)

0
3082

Jinin haila (jinin al’ada) wani jini ne na al’ada, wanda yake fita daga gaban (al’aurar) mace a kowane wata. Shi wannan jini, ba cuta ko alamar cuta ba ne. Alama ce da take nuna cewa, mace za ta iya ɗaukar ciki (juna biyu). Ma’ana dai, duk macen da take jinin haila, to tana cikin shekarun da mace take ɗaukar ciki.

Idan lafiya ƙalau ne, ana fara jinin al’ada ne daga shekaru 10 zuwa shekaru 16. Ɗaukewar jinin al’ada ya bambanta tsakanin mata. Wasu suna dainawa a shekaru 43 wasu kuma suna wuce shekaru 50. Idan jinin al’ada ya zo, yakan iya yin kwanaki 2 zuwa kwanaki 7 yana zuba, sannan kuma yana zuwa ne duk bayan kwanaki 21 zuwa 35, ba lallai sai wata-wata ba. Amma dai, yawancin mata sun fi yin jinin al’ada ne duk bayan kwanaki 28.

  • Dalilin yin jinin al’ada

A kowane wata, mahaifa tana yin wasu shirye-shirye domin ɗaukar juna biyu. Wannan shirye-shiryen yana farawa ne da zarar mace ta kai shekarun fara jinin al’ada. Mahaifa tana daina wannan shirye-shiryen bayan mace ta kai shekarun daina jinin al’ada. A lokacin wannan shirye-shiryen (kowane wata), ƙwai yana fitowa tun yana ƙarami har ya kai girman da zai iya haɗuwa da ruwan maniyyin namiji, domin samar da ɗa.

Har ila yau, a kowane wata cikin mahaifa yana haɓaka, kuma yana yin kauri a lokacin wannan shirye-shirye. Duk wannan canje-canjen da yake faruwa a cikin mahaifar mace, yana faruwa ne domin tsammanin samun ciki. Idan mahaifa ta gama wannan shirye-shiryen kuma, ba a samu juna biyu ba, to sai cikin mahaifar ya kwakkwaɓo ya fara zubar da jini. Wannan jinin shi ake kira da jinin al’ada.

Da zarar jinin ya fara zuba, mahaifa za ta fara wani sabon shiri domin tsammanin ɗaukar ciki. Idan kuma aka yi sa’a, mace ta samu juna biyu, to mahaifa ba za ta sake yin irin wannan shirye-shiryen ba, har sai bayan haihuwa ko kuma cikin ya zube. Wannan dalilin ne ya sa duk macen da take da juna biyu ba ta yin jinin al’ada.

  • Yanayin Jinin al’ada

Jinin al’ada ya sha bambam tsakanin mata. Ba lallai yanayin jinin al’adar mace da wata macen ya zama iri ɗaya ba. Kwanakin da kika saba yi da adadin jinin da kike zubarwa, ba lallai sai ya yi daidai da na wata macen ba. Kowace mace tana da nata yanayin.

A lokacin da jinin al’ada zai zuba, ko kuma yake zuba, akwai canjin yanayi da yakan iya faruwa a jikin mace. Wannan canjin yanayi shi ake kira da ‘premenstrual syndrome’. Alamomin Premenstrual syndrome sun haɗa da ciwon mara, ciwon nono, saurin fushi, damuwa, gajiya da sauransu. Ba kowane lokaci ake jin waɗannan alamomin ba, kuma ba a buƙatar a sha magani saboda premenstrual syndrome sai dai idan abin ya yi tsanani sosai.

  • Lalurorin jini al’ada
  1. Zubar jinin al’ada da yawa
  2. Zubar jinin al’ada ɗan kaɗan
  3. Daɗewa/ƙara kwanakin zubar jini
  4. Raguwar kwanakin zubar jinin
  5. Dena zuba/ɗaukewar jinin.
  6. Saurin zagayowar al’ada
  7. Ciwon mara lokacin al’ada da sauransu.
Idan mace ta samu ɗaya daga cikin waɗannan lalurori, to ta garzaya asibiti domin neman shawarar likita.

  • Ciwon mara lokacin al’ada

Ciwon mara lokacin al’ada yana ɗaya daga cikin ‘premenstrual syndrome’ da aka yi bayani a baya. Galibi, ciwon ba mai tsanani ba ne, amma yakan iya zama mai tsanani a wurin wasu matan. Kuma ko an sha magani ko ba a sha magani ba, ciwon zai yi sauƙi.

Don haka, ba lallai sai an sha magani ba, sai dai idan ciwon ya yi tsanani sosai. Mafi yawancin mata suna daina wannan ciwon bayan ‘ƴan wasu shekaru.

  • Kammalawa

Jinin al’ada, alama ce da take nuna cewa mace za ta iya ɗaukar ciki. Yakan iya zuwa da wasu lalurori. Idan mace ta ga ɗaya daga cikin waɗannan lalurori, to ta je asibiti domin neman shawara

Domin kararanta yadda ake da mai gida lokacin al’ada  ko mene ne Jinin haila ko Dalilin yin jinin haila danna koren rubutun nan

labarin da ya wuceYadda Ake Miyar Alaiyahu Domin Ƙarin Lafiya
Labarin na GabaDalilin Yin Jinin Al’ada (Haila)
Dr. Adamu Bala
Sunana Dr Adam Bala Husaini, likita da yake aiki a sashin lafiyar iyali (Family Medicine), a asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad Specialist Hospital, Kano Nigeria. Kuma shugaban sashin lafiya na wikiHausa