Zaurancen ‘Yan Maye

0
27

khairatu.shehu

Zaurancen ‘yan maye wasu kalamai ne da ‘yan maye suke amfani da su a tsakaninsu. Sau da yawa wasu mutane masu yin sana’a ko kasuwanci ko aiki ko ma ɗalibai suna da wasu kalamai da suke amfani da su don su ɓatar da bami (mutum) daga gane manufarsu. Ba kuma mai ganewa sai su ko kuma wanda ya zauna da su ko aka gaya masa shi ne zai gane abin da suke nufi da irin waɗannan kalamai.

Su ma ‘yan maye suna da wasu kalamai da suke yi a tsakaninsu wanda kusan su kaɗai suke sanin ma’anar abubuwan da suke nufi sai kuma wanda aka yi wa bayani ya fahimta ne kawai yake iya gane manufarsu. Yawancin wannan zaurance shi ma wata alama ce ta buguwa da gushewar hankali da rashin gaskiya da aikata laifi wanda ke da alaka da illolin shaye-shaye. Ga wasu daga ciki kamar haka:

  • Za mu je dubun nahiya (wurin shan kayan maye kenan)
  • Muna cikin dubun aiki (an shawo ƙwaya kenan)
  • Mun murɗe masa kai (murfin kwalbar abin da suka sha )
  • Mun hau network (kai ya ɗauki caji kenan)
  • Mu je zubi (za a je shan ƙwaya ke nan)
  • Mun je madiri (suna cikin maye kenan)
  • Muna so mu yi slow (ana so a yi maye kenan)
  • Za mu kara wa sama hazo (za a sha wiwi ko taba)
  • Buguwa ma sai a can (wato buguwa sai a lahira)
  • Haɗin da ba duk kai ba (a haɗa ƙwayoyi da maganin mura iri daban-daban)
  • A sha komai (ma’ana ba su bar kowane abin maye ba)
  • Yaya ruwa? (ba za a sha ba ne yau?)
  • Weza (weather) ta ba da haɗin kai (yanayin gari ya yi daɗi kenan)
  • Aiki to, aiki kurum (wato in ba a sha ba a sha)
  • Akwai gem, za a fasa eriya (za a je wata matattara inda manyan gayu suke haɗ uwa don yin shaye-shaye).

Don karanta Waƙar Shan Ƙwaya ta Alhaji Dr Adamu Ɗanmaraya, Jos danna nan

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceRataye na 3: Waƙar Shan Ƙwaya ta Alhaji Dr Adamu Ɗanmaraya, Jos
Labarin na GabaTaƙaitaccen Tarihin Ibrahim Yaro Yahaya (1944–1995)
Ado Ahmad Gidan Dabino
Shahararren marubucin littattafan Hausa ne a Najeriya, sannan mai shiryawa da bayar da umarni sannan ɗan wasa ne a shirin finafinan Hausa kuma ɗan jarida. Tare da shi aka kafa wasu ƙungoyoyi na marubuta da masu shirya finafinai. Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta karrama shi da lambar yabo ta ƙasa mai taken, Member of the Order of the Niger (MON) bisa hidimta wa jama'a da yake yi a cikin ayyukansa.