Yunƙurin Hausantar Da Kimiyya Da Fasaha

0
23

Haƙiƙa ilimin kimiyya da fasaha baiwa ce ta Ubangiji da ya keɓanci wasu daga cikin bayinsa da ita, wanda su kuma su ke da haƙƙin sanar da wanda Ubangiji ya so. Amma kuma amfaninsa da tasirinsa da yin aiki da shi ya shafi kowa da komai.

Don haka ba sai mutum ya karanci ilimin kimiyya da fasaha a makaranta ya cancanta ya san shi ko ya yi aiki da shi ba. Ma fi sauƙin sanar da ilimin kimiyya da fasaha ga al’uma shi ne samar da shi da koyar da shi cikin yarensu, ta yadda zai yi sauƙin fahimta gare su da kuma al’umomi masu zuwa bayansu.

Wannan zai kau da ƙalubalen gwagwarmayar koyon harshen turanci ko faransanci da sauran harsunan da ke ɗauke da wannan ilimi na kimiyya da fasaha kafin saninsa. Wannan manufa ta dace da ƙudirin UNESCO na Ƙarnin Harsunan Uwa na Duniya, wato International Decade of Indigenous Languages (IDIL2022-2032), da kuma shirin hukumar bincike da bunƙasa harkokin ilimi ta Nigeria, wato NERDC na Language Development Services.

A wani ɓangare kuma, samar da ilimin kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa zai taimaka wajen haɓaka ci gaban al’uma da ƙasa baki ɗaya kamar yadda ya tabbata a sauran ƙasashen da suka ci gaba kamar su China da Germany, ta hanyar koyar da ilimin kimiyya da fasaha a harshen uwa da suke yi a ƙasashensu.

A Nigeria, tuni a na ta yunƙurin samar da ilimin kimiyya da fasaha a harshen Hausa ta fannoni daban-daban tare da kiraye-kirayen samar da dokar da za ta bayar da damar koyar da darussan Kimiyya da Fasaha cikin harsunan ƙasa a Nigeria a matakin gwamnatin tarayya da jihohi. Haƙiƙa zai fi sauƙi a horar da malaman da za su koyar da yara ilimin Kimiyya da Fasaha cikin Hausa fiye da koya wa ɗalibai harshen turanci sannan su koyi wannan ilimi.

Haƙiƙa harshen Hausa yana da nagarta da bunƙasa a nahiyar Afrika da wasu sassa na duniya, ta yadda za a iya samar da dukkan fannonin ilimi a cikinsa, duba da yadda ya shahara a duniya wajen yin amfani da shi a kafafen yaɗa labarai masu yawa a faɗin duniya. Bugu da ƙari Allah ya albarkaci al’umar Hausawa da ƙwararru a dukkan ɓangarori na ilimin kimiyya da fasaha ta yadda babu fannin ilimin da ba za a iya samar da shi cikin harsen Hausa ba a yanzu.

Don haka ya zamo ƙalubale ga Hausawa masana ilimin kimiyya da fasaha su ƙara ba da himma a kan samar da wanna ilimi cikin harshen Hausa. A shekarun baya, masana da dama sun wallafa littattafai da ƙasidu a wasu fannonin kimiyya da fasaha a cikin harshen Hausa. Misali, Malam Abubakar Imam da wani Bature mai suna Rupert East sun wallafa littafin “Ikon Allah” mai ɗauke da labaran halittu iri-iri na Duniya.

Farfesa Hambali Junju ya rubuta littafin ‘Garkuwar Hausa da tafarkin ci gaba’ mai ɗauke da fassarar wasu kalmomi da suka shafi kimiyya da fasaha cikin Hausa. Farfesa Muhammad Kabir ya rubuta littafin ‘Aikin Likita’, yayin da marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa ya rubuta littafin ‘Kimiyyar Sararin Samaniya’.

A wannan zamani kuma, Jami’o’in Nigeria da na wajen Nigeria sun fara samar da fassarar littattafan kimiyya da fasaha kamar Lissafi, Physics, Chemistry, Biology, Kimiyyar Computer cikin Hausa. A wani ɓangare kuma ɗaiɗaikin mutane suna rubuce-rubucen littattafai da ƙasidu, kai har da waƙoƙi da su ka shafi kimiyya da fasaha a cikin Hausa.

Misali, na wallafa littafin “Wani Abu a Kan Matar Sarki” a kan Ilimin ‘Yan Halittu, wato microbes, da littafin “Zaton Wuta a Maƙera” a kan cutar yoyon fitsari da yadda za a magance aukuwarta. Na kuma wallafa tare da rera waƙoƙi a kan cimaka (nutrition) da cutar Korona a cikin harshen Hausa.

Har wa yau akwai wasu masana da su ke koyar da darussan Kimiyya da Fasaha a shafukan sa da zumunta na Facebook da YouTube da dai sauransu. Akwai kuma cibiya mai zaman kanta ta Engausa Global Tech Hub da ta himmatu wajen koya wa matasa fasahar ƙere-ƙere da sana’o’i na zamani a cikin harshen Hausa.

To amma akwai buƙatar ƙara zaburar da masana su samar da ingantattun rubuce-rubuce, musammam littattafai da sauran kayayyakin koyo da koyarwa cikin harshen Hausa, wadanda su ne muhimman kayan aikin ɗabbaƙa dokar koyar da darussan kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa.

Tuni mun assasa wata Gidauniyar Bunƙasa Kimiyya da Fasaha cikin Hausa mai zaman kanta da manufofi kamar haka:
1. Gamayyar ƙwararru a fagen kimiyya da fasaha da kuma masana harshe Hausa don samar da ingantaccen ilimin kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa, don ƙarin yaɗuwarsa da tasirinsa ga ci gaban al’umma.
2. Alaƙanta al’adu da fasahar Hausawa da kimiyya da fasahar zamani, don bunƙasa tasirinsu ga ci gaban al’umma.
3. Wallafa ƙasidu da mujallu da muhimman labarai da suka shafi ilimin kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa domin ilmintarwa da wayar da kan al’umma bisa abubuwan da suka shafi kimiyya da fasahar zamani.
4. Ba da gudunmawa da samar da manhajoji na koyo da koyarwa da bincike kan fannoni daban-daban na kimiyya da fasaha a cikin harshen Hausa, domin samar da ƙwararrun masana kimiyya daga tushe a al’umar Hausawa.
5. Amfani da kafafen sadarwa na zamani, don tabbatar da tsarin koyo da koyar da kimiyya da fasaha cikin al’umar Hausawa.
6. Samar da mahanga / shawarwari don nusarwa ga mahukunta da masu ruwa da tsaki a kan kafa dokoki da ƙudure-ƙudure bisa aiwatar da ilimin kimiyya da fasaha a harshen Hausa a dukkan matakan ilimi.

A yayin da masana cikin Jami’o’i da sauran manyan makarantu su ke aikin samar da ilimin Kimiyya da fasaha cikin Hausa, wannan cibiya za ta zamanto magama mai tattaro dukkan masu ruwa da tsaki kamar gwamnati, masarautu, shuwagabannin addini, mawadata, ƙungiyoyin marubuta da bunƙasa al’adu, ‘yan jarida, ƙungiyoyin ci gaban al’uma da dai sauransu, wajen samarwa da yaɗa ingantaccen ilimin Kimiyya da Fasaha da kuma amfaninsa ga ci gaban al’uma.

Abin tambaya da jan hankali a nan shi ne, yaushe za a fara koyar da ɗalibai ilimin kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa a ƙasar Hausa? Ta ina za a fara? Kuma waye zai fara? Idan ba mu taka rawar kiɗan mu ba, to fa wasu za su taka mana.

Bisa wannan ne muka assasa Sarkinfada College of Health Science and Technology. Daga cikin ƙudirorin wannan makaranta, baya ga horar da ƙwararru kan kimiyya da fasahar kiwon lafiya, akwai tsarin gudanar da bitoci cikin harsunan turanci da Hausa domin kawar da shamakin kuma tarnaƙin da koyon harshen turanci ka iya kawo wa bisa sauƙin fahimtar ilimin kimiyya da fasaha ga ɗalibai.

Wannan tsari zai haɓaka fahimtar ilimin kimiyya da fasaha ga ɗaliban makarantun
sakandare da na gaba da sakandare, ya kuma da daƙile kaso yawan daliban da sukan faɗi a sakamakon jarrabawar fita daga sakandare a cikin al’umar Hausawa. Har wa yau akwai tsarin ilimin manya bisa kimiyya da fasaha don waɗanda ba su samu damar koyo a makarantu ba, su hau tafarkin kimiyya da fasaha cikin sauƙi.

Burin mu shi ne kasancewar duk ɗalibin da ya halarci waɗannan bitoci ya zamo ya samu nagartacciyar fahimtar ilimin kimiyya da fasaha cikin harsunan Hausa da Turanci, domin samun nasarori a jarrabawar fita daga sakandare da kuma sharar fagen bisa fannonin da su ke sha’awar ƙwarewa nan gaba.

Mu na kuma burin wannan tsari ya taimaka wajen cimma manufofin Ƙarnin Harsunan Uwa na Duniya na UNESCO, wato UNESCO’s International Decade of Indigenous Languages (IDIL2022-2032) da kuma kuma shirin hukumar bincike da bunƙasa harkokin ilimi ta Nigeria, wato NERDC na Language Development Service

Domin karanta waƙar yaƙin korona danna nan

Farfesa Faruk Sarkinfada 26/08/24

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceShin Sauro Yana Yaɗa Cutar HIV/AIDS?
Labarin na GabaSauro Yana Gani Ne Da Iskar Da Muke Fitarwa (Co2)