Yanayin Harshen Waƙar Baka

0
365

Mazubi na harshen waƙar baka yana ɗauke da ƙwayoyin sauti da gaɓoɓi da kalmomi da kuma jumloli; waɗanda suke ba makaɗa damar su iya aiwatarwa da sadarwa cikin rerawa a sauƙaƙe.

A zubi na waƙoƙin baka, daɗa a wajen makaɗa masu shiri na baka ko masu shiri na ƙire ko haye ko masu shiri na rubuce; suna shirya kalmomi ne da kansu ko wasu su shirya musu, sannan su saka amo na murya da na kiɗa, su kuma rera.

Waƙar Baka

Shirya Kalmomi

Shiri na Baka Shiri na Ƙire/Haye Shiri na Rubuce

Kalmomi Kalmomi Kalmomi na kai
na kai na kai
Satar waƙar Kalmomi na wani
Satar Waƙa

Idan aka lura, dangane da harshe a zubin waƙar baka, makaɗa da mawaƙa suna tasirantuwa bisa wasu matakai na ginawa da shirya waƙa da suka haɗa da:

3.1 Shirya Kalmomi

Kamar yadda aka nuna a baya, waƙoƙin baka ana shirya su ta gaɓoɓin kalmomi bisa zaɓi na makaɗi. Kalmomi a harshe su suke yi wa makaɗi tsani ya saƙa saƙonni, manya da ƙanana, a waƙa.

3.2 Daidaita Murya da Amon Kiɗa

Makaɗi ko mawaƙi yana daidaitawa ne a tsakanin amon muryarsa, wadda take tafiya a saje da gaɓoɓi da kalmomi na zubinsa; da kuma amon kiɗa wanda yake wanzuwa daga kayan kiɗa waɗanda yake amfani da su. A lokacin da wannan yanayi ya daidaitu, sai rauji na waƙa ya wanzu; wanda yakan zama gajere ko dogo ko matsakaici, gwargwadon yanayin kalmoni da kuma amon kiɗan da aka ɗauka.

3.3 Daidaita Tunani a Saɗaru

A waƙar baka akan daidaita tunani da ma’ana, babba ko ƙarama ta waƙa ta gurabun kalmomin waƙa waɗanda ake rerawa ta hanyar tsayin rauji a saɗaru. Dole ne tunanin waƙa ya dinga tafiya tare da zubin kalmomi a saɗaru na waƙa.

3.4 Kaucewa Dokokin Nahawu

Harshen waƙa, musamman yadda wani bi yakan ƙunshi tarin kalmomi, sannan da yanayin rauji da rerawa; yakan wadatu da tsarinsa ne har ya dinga bauɗe wa wasu dokokin nahawu.

Shi harshen waƙa yakan sanya masana nahawun harshe da jujjuyawar kalmomi da karin harshe da sauransu; su yi ta ƙoƙarin gwada ɗora kalmomi da jumloli na waƙa a kan daidaitaccen tsarin nahawu. A wajen waƙar baka ƙirƙirowa da baddala kalmomi ko tsarin jumla da sauransu wata hanya ce ta kamalar harshen waƙa.

3.5 Jefa Dabarun jan Hankali

Wasu daga cikin hikimomi na harshe wanda ake shirya waƙa da shi, sukan yi naso a waƙa. Makaɗi yakan yi amfani da dabaru na yi wa zubin waƙarsa kwalliya ya daɗa armasa waƙar; ya ƙara mata nagarta cikin dausayin harshe. Dabarun nan na jan hankali sukan iya sanya harshen waƙa ya ƙara tsada; ya zama mai nauyin fahimta, mai jefa sarƙadodo a wajen warware ma’ana.

Akwai dabarun jan hankali da yawa waɗanda makaɗa da mawaƙa suke jejjefawa a waƙoƙinsu da suke bambanta a daraja da nauyi na kowace waƙa; ko kuwa a mabambantan waƙoƙi na makaɗi ko mawaƙi ɗaya.

Domin karanta cikakken bayani a kan Makaɗi a Sarrafa Harshen Waƙa danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Waiwaye Kan Harshen Makaɗi A Zubin Waƙar Baka wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceMu Yi Alhairi, Mu Guji Rowa
Labarin na GabaTarihin Magabata da Haihuwar Ɗanƙwairo
Prof. Sa’idu Muhammad Gusau
FARFESA SA'IDU MUHAMMAD GUSAU, An haife shi a Gusau jihar Sakkwato, (Maris 24, 1952). Ya yi karatun firamare na Islamiyya daga 1965-1969, ya je kwalejin sarkin Musulmi Abubakar daga Junairu 1970 zuwa Yuni 1973. Ya yi Diploma, Digiri Na farko (B.A), na biyu (M.A) da Digiri na uku (Ph.D) duk a jami'ar Bayero, Kano.