Tsaga wata alama ce wadda Hausawa da kuma wasu ƙabilu na sassa daban-daban da suke cikin Nahiyar Afrika da wasu sassa na wannan duniya suke yi da aska a fuska ko a wani ɓangare na jiki, don a bambanta wata ƙabila da wata ko mutanen wata Daula da wata ko dangi da dangi ko zuri’a da zuri’a ko don riƙon al’ada ko don magance wata cuta ko kuma don yin kwalliya.
A al’adar Hausawa tsaga ta kasu zuwa rabo uku kamar haka: Tsagar gado da tsagar magani da tsagar kwalliya. Kowace daga cikin waɗannan kashe-kashe na tsaga tana da dalilan da kan sa a yi ta, kuma kowane kaso ya sake kasuwa zuwa wasu rabe-raben.
Tsagar Gado
Tsagar gado ita ce wadda ake yi a fuska don nuna asalin mai ita ko sashin da ya fito. Ita tsagar gado tana bin gadon uba ne ba na uwa ba, watau ana yin tsagar gado ne don nuna asalin wajen uba ba na wajen uwa ba. Tsagar gado ta kasu zuwa kashi uku kamar haka: tsagar gado mai nuna asalin gari ko wurin zama misali, Katsinanci da Dauranci da Kabanci da Ƙwannanci da Gobirci da Zamfaranci da Arauci da sauransu.
Akwai kuma tsagar gado mai nuna asalin ƙabilar da mutum ya fito misali, barbarci da buzanci da sauransu. Akwai kuma tsagar gado mai nuna ma’abota wata sana’ar gargajiya misali, mahauta da manoma da sauransu. Ana kuma kiran tsagar gado da sunan askar gado. A yanzu za a yi bayani cikakke kan ire-iren tsagar gado.
Tsagar Gado Mai Nuna Asalin Gari ko Wurin Zama
Irin wannan tsaga tana nuna asalin gari ko shiyyar da mai ita ya fito a ƙasar Hausa. A da can irin wannan tsaga tana nuna daga Daular da mai ita ya fito, watau ya fito daga ƙasar Katsina ko Daura ko Kabi ko Gobir ko Zamfara da sauransu. A wancan zamanin ta hanyar tsagar gado ne ake yaƙar abokan hamayya. Ana nufin ta hanyar tsagar gado ne idan ana yaƙi tsakanin Daular Katsina da ta Gobir, Katsinawa suke gane Gobirawa, su ma Gobirawa su gane Katsinawa.
Haka kuma ta hanyar tsagar gado ne ake fahimtar masu irinta zuri’ar wane ne da yake zaune a wuri kaza. Akwai tsaga iri daban-daban a ƙasar Hausa waɗanda suke nuna mazauna wurare ko garuruwa waɗanda suka haɗa da Katsinanci a ƙasar Katsina da Maraɗi ta Jamhuriyyar Nijar, da Dauranci a ƙasar Daura ta Jihar Katsina, da Gobirci a ƙasar Gobir da Zamfaranci a ƙasar Zamfara da Kabanci a ƙasar Birnin Kabi da Arauci na Arawa mazauna Gundumar Dogon-Dutsi da kuma wasu ƙauyukan da suke cikin Gundumar Ƙwanni duk a cikin Jamhuriyyar Nijar da kuma Ƙwannanci a Gundumar Birnin Ƙwanni ta Jamhuriyyar Nijar. Yanzu za a bi ire-iren waɗannan tsaga da aka lissafa a sama domin yin cikakken bayani kan kowace da wurin da ake samun ta.
Tsagar Katsinanci
Tsagar Katsinanci tsagar gado ce wadda ake yi wa haɓen ƙasar Ƙatsina na asali ko maguzawan ƙasar Katsina, akan kira irin wannan tsaga da sunan bille ko maguzanci a ƙasar Katsina. Irin wannan tsaga gado biyu ce, gado na farko ana yin su ne a kumatu, gado na biyu bisa fuska. Akwai bambanci tsakanin yawan ‘ya’yan tsagar da ake yi wa saraki da talakawa.
Ga talakawan ƙasar Katsina ana yin tsaga shida ga kuncin dama, tsaga bakwai a kuncin hagu. Ga ‘ya’yan sarautar haɓen Katsina ana yin tsaga bakwai a kuncin dama, shida a kumcin hagu. Abin nufi anan shi ne, ta hanyar yawan tsaga a kumatu ake bambance wannan saraki ne wannan talaka ne. A halin yanzu ana samun masu irin wannan tsaga a sassan arewaci da tsakiyar Jihar Katsina a ƙananan hukumomin Katsina da Kaita da Jibiya da Mashi da Mani da Dutsi da Ɓatagarawa da Rimi da Kurfi da Dutsin-ma da Safana da Batsari da Ɗan-musa da Charanchi da Ingawa da Kusada.
Haka kuma ana samun masu irin wannan tsaga a masarautar Maraɗi ta Jamhuriyyar Nijar. Kamar yadda aka bayyana a baya masu irin wannan tsaga su ne haɓen asali na Daular Katsina, kuma su ne sarakunan haɓe na masarautar Katsina. A lokacin da Ummarun Dallaje ya kafa mulkin Fulani Dallazawa a Katsina, sai sarakunan haɓen suka yi ƙaura zuwa Maraɗi wadda da can ƙasar Katsina ce, suka kafa mulkinsu a wurin da sunan masarautar Katsina a Maraɗi.
Wannan dalili ne ya sa tun daga wancan lokaci har zuwa yanzu ake kiran Sarkin Maraɗi da sunan Sarkin Katsinan Maraɗi. A wannan sabuwar masarauta sun ci gaba da yi wa ‘ya’yansu irin wannan tsaga ta Katsinanci har zuwa wannan lokaci da muke ciki. Bayan ƙasar Katsina da ƙasar Maraɗi ta Jamhuriyyar Nijar duk wurin da aka ga mutum da tsagar Katsinanci to ƙaura ya yi daga waɗannan wuraren zuwa wannan wuri.
Tsagar Gado Mai Nuna Masu Yin Sana’o’in Gargajiya
Irin wannan tsaga tana nuna masu irinta suna yin wata sana’a daga cikin sana’o’in gargajiya na Hausawa.Ire-iren wannan tsaga akwai billen hannun dama, wanda yake nuna mai irinta zuri’arsu masu yin sana’ar fawa ne. Akwai kuma tsagar lezumanci wadda take nuna mai irinta masu sana’ar noma ne.
Tsagar Billen Hannun Dama na Mahauta
Tsagar Bille a hannun dama tsagar gado ce wadda ake yi wa mahauta a ƙasar Hausa. Ana yin bille ƙarami a ɓangaren fuska na hannun dama gefen karan hanci. Dukkan mai irin wannan tsaga zuri’arsu masu yin sana’ar fawa ne. A yanzu akwai wasu mahauta da kan yi wa ‘ya’yansu tsagar bille a hannun hagu maimakon hannun dama. Tsagar bille a hannun hagu ba ta mahauta ba ce, masu irin wannan bille asalinsu Fulani ne Sulluɓawa waɗanda a yanzu su ne sarakunan Katsina.
Daga nan ne sai wasu mahauta suka ara suka yafa, suka mayar da shi nasu bayan kuwa ba asalinsu ba ne. Wurin da aka yi bille ne, watau a dama ko a hagu yake bambanta wannan mahauci ne ko kuma Bafulatani Basulluɓe. Irin wannan tsaga ta billen hannun dama ta mahauta ana samun masu irin ta a duk sassan ƙasar Hausa.
Tsagar Lezumanci Ta Manoma
Tsagar Lezumanci tsagar gado ce wadda take nuna mai irinta asalinsu manoma ne waɗanda ba su da wata sana’a idan ba noma ba. Tsagar Lezumanci gado biyu ce kuma ta yi kama da tsagar Katsinanci, wurin da suka bambanta shi ne, tsagar Lezumanci ana yin su ne da yawa caɓa-caɓa ba kamar Katsinanci ba da ake yin nan shida nan bakwai. Masu tsagen Lezumanci ana kiransu da sunan Lezumawa.
Bincike da aka gudanar ya bayyana su Lezumawa asalinsu Zamfarawa ne, sai wani Bazamfare mai suna Jatau ya sayi ɗan uwansa Bazamfare ya sanya shi bauta, sai ya riƙa kiran shi da sunan ‘ZUMU’ watau ɗan’uwa. Sannu-sannu sai aka riƙa kiran sa ‘Lezumu’ watau aka yi ƙarin ɗafa-goshin ‘Le’. Da Jatau ya ga hankalin Lezumu da ƙoƙarinsa sai ya yarda da shi ya kuma ba shi amanar gidansa, sai ya kasance duk harkokin gidan Jatau Lezumu ne yake tafiyar da su.
Yau da kullum Lezumu yana ta yin bauta a ƙarƙashin ɗan uwansa Jatau har ya gane dukkan asirin Jatau na tsafi. Wannan ne ya ba shi damar yin amfani da wannan asiri ya rinjayi ubangidansa Jatau, ya yi masa juyin mulki, ya amshe gidan sai mai doki ya koma kuturi.
Daga nan ne aka sami zuri’arsa wadda aka riƙa kira da sunan “Lezumawa” daga sunan Lezumu da mai gidansa Jatau ya riƙa kiran sa. Saboda ƙoƙarin Lezumu da iya tsafin da ya taimaka masa har ya amshe gidan maigidansa ɗan’uwansa Jatau wanda ya yi wa bauta, ya sa ake yi wa zuri’arsa kirari kamar haka:
“Lezumawan Jatau aska ba ki amana”
“Lezumawan Jatau taba kashe mai ba ki ruwa”.
(Hira da ASKS a ranar 3-6-96).
Ma’anar kirari na farko shi ne, duk irin yadda ka saba da aska idan ka ba ta amana, to wata rana za ta ci amanar mutum domin idan ka yanka ta a jikinka za ta kama, kamar yadda duk da amanar da Jatau ya ba Lezumu, amma da ya gane asirinsa sai ya tumɓuke shi ya amshe gidan.
Kirari na biyu kuma yana nufin duk wanda ya ba taba ruwa ta sha ta girma idan ya sha ta ba daidai ba, to tana shaƙe shi ya ƙware, ƙarshe ma ta kashe shi kamar yadda Lezumu ya yi wa ɗan’uwansa Jatau wanda ya riƙe shi har ya girma amma ya amshe masa gida.
Daga lokacin da Lezumu ya amshe gida, sai ya canza tsagarsu daga tsagen Zamfaranci ya zuwa tsagen Lezumanci wanda ya ƙirƙiro wa zuri’arsa, ya kuma mayar da ita tsagarsu ta gado. Irin wannan tsaga ta Lezumanci da Katsinanci a Jihar Katsina ana kiran su da “Hatimin-Noma”. Wannan kuwa ya faru ne saboda shaharar masu irin wannan tsaga a sana’ar noma da kuma ƙwarewarsu wajen yin tsafe-tsafen da suka shafi sana’ar noma.
A yanzu Lezumawa shahararrun manoma ne kuma matsafa a duk wurin da suke. Ana samun zuri’ar Lezumawa a ƙananan hukumomin Safana da Ɗan-musa da Dutsin-ma da Matazu da Musawa da Batsari da Kankiya da kuma wasu sassan na Jihar Zamfara. A saboda wannan tarihi nasu ya sa a yanzu idan wani biki ya same su sukan gayyaci dukkan danginsu daga ko’ina domin a taru wajen yin bikin (Hira da Sarkin Noma Babban- Kada, Shugaban zuri’ar Lezumawa na Jihar Katsina. A Lezumawar Babban-Kada Safana, a Ranar 11-6-97).
Tsagar Magani
Tsagar magani ana yin ta ne domin a fitar da jini daga jikin mutum saboda a sami sauƙi ko a warke daga wani ciwo wanda yake cikin jiki. Ana kuma yin ta don a fitar da mataccen jinin da yake cikin jikin mutum. Wasu Hausawa suna da ra’ayin mataccen jini a cikin jikin mutum kan yi sanadiyyar kamuwa da cututtuka iri daban-daban. Fitar da shi ko rage shi kan sa a sami sauƙi ko a warke daga ciwon. Akwai tsagar magani iri daban-daban da ake yi wa Hausawa, waɗanda suka haɗa da ƙaho da tsagar ɓalli-ɓalli da tsagar fitar- ruwa da tsagar maganin jiri da tsagar maganin kanne da tsagar ciki ga jarirai da tsagar murfi da sauransu.
Ƙaho
Ƙaho tsagar magani ce wadda wanzamai kan yi wa mai buƙata. Ana samun ƙaho na sa ko na saniya a gyara shi. Ana kafa ƙahon a bayan mabuƙacin ko a wurin da lalura take. Daga nan sai wanzamin ya yi ta tsotsa ƙahon da yake kafe a wurin da ake buƙatar yin sa. Zai yi ta yin haka har sai ƙahon ya kame sosai sannan ya liƙe ‘yar-ƙofar ƙahon da jijiyar da yake taunawa a cikin bakinsa.
Yin haka ne zai sa ƙahon ya liƙe wurin da aka kafa shi. Bayan kamar minti goma zuwa sha biyar sai a cire ƙahon saboda a wannan lokacin mataccen jinin ko cutar da ake son fitarwa ta taru daidai wurin da aka kafa ƙahon. Daga nan sai a sanya askar tsaga a tsaga wurin da aka fitar da ƙahon, ana yin tsage daga tara zuwa goma sha biyar. Daga nan sai a sake mayar da ƙahon wurin da aka cire shi.
Bayan kamar minti goma sha biyar sai a sake cire shi, a wannan lokaci mataccen jini ko cutar ta taru cikin ƙahon, sai a zuba a ramin da aka tona kafin a fara yin ƙahon. Haka za a sake yi kamar sau biyu ko uku, yin haka ya danganta da ƙarfin wanda za a yi wa ƙahon. Daga nan sai a zuba ƙasa a rufe ramin da aka zuba jinin. Shi ke nan an gama ƙaho sai wanda aka yi wa ya saka suturarsa idan ga baya aka yi masa.
Ana yin ƙaho daga ɗaya zuwa huɗu, amma kafin a kafa wa mutum ƙaho fiye da ɗaya dole sai wanzamin ya tabbatar wannan mutum yana iya ɗaukar fiye da ɗaya. Idan jinin mutum ba shi da yawa, to idan aka yi masa ƙaho fiye da ɗaya ana iya ƙwararsa, maimakon abin ya zama na magani sai ya zama cuta. Wasu wanzamai kan shafa magani a wurin da suka yi ƙaho, wasu kuwa ba sa shafa wani magani matuƙar mataccen jini ya fita buƙata ta biya.
Yana da muhimmamnci a nan a bayyana ire-iren cututtukan da kan sa a yi ƙaho.Yawan mutuwar jiki da kasala abubuwa ne waɗanda Hausawa suka ɗauka mataccen jini ne yake kawo su. Haka kuma idan mutum ya buge a wani ɓangare na jikinsa har jini ya taru a wurin kuma bai fita ba, ko ya yi targaɗe a wani wuri kuma wurin ya yi kumburi. Bayan an gyara sai a yi masa ƙaho a wurin don a fitar da jinin da ya taru.
Haka kuma idan murfin ƙahon zuciyar mutum ya faɗa dole sai an yi amfani da ƙaho a jawo shi.Dukkan waɗannan matsalolin rashin lafiya da aka yi bayaninsu, wasu Hausawa sun ɗauka idan aka yi ƙaho za a sami sauƙi ko a warke daga ciwon.
Tsagar Kwalliya
Tsagar kwalliya ko jarfa ko shasshawa tana nufin ire-iren tsagen da mata kan sa wanzamai su yi masu a fuska ko a wani ɓangare na jiki domin ado ko kwalliya.Ita tsagar kwalliya an fi yi wa mata ita, domin da wuya a ga namiji ya ba da fuskarsa ko wani ɓangare na jikinsa ga wanzami don a yi masa tsagar kwalliya.
Ire-iren waɗannan tsage sun haɗa da kalangai da takutuha da kwaluluwa da matakin-soro da ‘yar ƙirji da alluna da me-ka-ce maigida da ‘yarbaka da garɗin-gero da kwanciya-da-masoyi. Akwai kuma tsagen kwalliya waɗanda zamani ya kawo, ire-irensu sun haɗa da alamomin siyasa kamar fartanya mai nuna alamar jam’iyyar N.P.C. da tauraruwa mai nuna alamar jam’iyyar NEPU. Wasu kuma sukan sanya a tsaga masu hoton agogo ko sunan masoyi ga hannuwansu.
A binciken da aka gudanar a sassan ƙasar Hausa an fahimci mafi yawancin ire-iren waɗannan tsage na kwalliya ana amfani da alamomi iri-ɗaya. Kuma ana kiransu da suna ɗaya, ɗan bambancin da akan samu bai taka kara ya karya ba.
Lokacin Yin Tsagar Kwalliya
A al’adance an fi yin tsagar kwalliya da kaka domin kuwa a wannan lokaci an kawar da amfanin gona, kuma sanyi ya fara sauka yadda idan an yi tsagar za ta yi saurin warkewa. Wannan kuma ya faru ne saboda Hausawa suna da ra’ayin a wannan lokaci jiki ya fi saurin tohuwa. A irin wannan lokaci ne wanzamai masu yin tsagar kwalliya ko jarfa suke barin gidajensu domin tafiya yawon jarfa, watau yin tsagar kwalliya a garuruwa da ƙauyukan ƙasar Hausa.
Wani lokaci kuma da ake yin tsagar kwalliya shi ne watan takutuha. Idan wanzaman jarfa za su sauka a wani gari mafi yawanci sun fi sauka a ranar kasuwar garin don kowa ya san an yi baƙin wanzamai ‘yan jarfa. Kowane daga cikin ‘yan tawagar kan sami gidan da yake da budurwa ya saukar mata. Dukkan yawan kwanakin da za su yi a garin, a gidan da suka sauka ake ba su masauki da abinci har sai sun tashi daga wannan gari.
A duk wurin da suka je suna tafiya da makaɗa da maroƙa waɗanda suke rera waƙoƙin yabo da na kushe ga ‘yan matan da suka yi masu kyakkyawar sauka da waɗanda ba su yi masu ba. Makaɗan wanzamai ana kiran su da ‘yan kurya ko makaɗan kurya.
Ire-Iren Tsagar Kwalliya
A lokacin da za a yi wa budurwa ko yarinya tsagar kwalliya, sai abokiyarta ta ɗauko turmi don wadda za a yi wa tsagar ta zauna ta jingina da wannan turmi. Daga nan sai wannan abiya ta zauna kusa da ita ta dafa kafaɗunta. Ana yin haka ne domin wadda za a yi wa tsagar kar ta nuna kasala. Ita abiyar wadda za a yi wa tsagar ce take gaya wa wanzamin irin tsagar da za a yi wa wannan abiya.
Wasu kuma samarinsu ne kan zaɓa masu irin tsagar da za a yi masu. Daga nan ne sai wanzamin ya fara tsaga, ana yin tsagar ana kiɗa da waƙa, maroƙa kuma suna shelar a kawo kari. A wannan lokaci ne samari za su yi ta ƙoƙarin gwada bajinta ta hanyar bayar da kari.Su ma ‘yan’uwa da abokan arziki ba a barin su a baya, sai su ma su yi ta ba da nasu karin. Abubuwan da akan bayar na kari sun haɗa da kuɗi da sutura da dabbobi.
Dukkan abubuwan da aka samu na kari wanzaman ne da makaɗansu da yaransu da maroƙansu suke rarrabawa. Bayan abubuwan da aka samu na kari sai kuma iyayen yarinyar da aka yi wa tsagar su ba da tasu sallamar ga wanzaman.Idan aka sauka gidansu yarinyar da take da dangi da yawa wadda a lokacin da aka fara yi mata tsaga an sami kari sosai, akan ɗauki kwanaki da yawa a wannan gida don ci gaba da yi mata tsaga, kamar misalin kwana biyu zuwa bakwai.
A mafi yawancin lokaci a saboda kiɗa da waƙa da ake yi a lokacin jarfa waɗanda a cikin waƙar akwai yabo da kuma bayar da ƙarfin gwiwa ga budurwar da ake yi wa tsagar, yakan sa ‘yan mata nuna juriya da daurewa. Wasu kuma gudun kar a yi masu zambo kan sa su daurewa a lokacin da ake yi masu tsaga. Wannan kan sa har a gama yi masu tsagar ba sa nuna wata alama ta kasala ko raggwanci ko su yi kuka. Haka za a yi ta yi daga wannan gida zuwa wancan gidan inda ‘yan mata suke a garin da suka sauka don yi masu tsaga.
Bayan sun gama a wannan gari sai kuma su ƙara gaba zuwa wani garin.Wanzaman jarfa kan ɗauki lokaci mai tsawo kafin su sake dawowa a garin da suka yi tsaga. A wani lokaci sukan ɗauki misalin shekara biyu zuwa uku ba su dawo a wannan gari ba, sai kuwa idan an bukaci su dawo.Wannan wata alama ce ta nuna kawaici da godiya bisa ga abubuwan da aka yi masu.
Kalangai
Kalangai tsaga ce wadda ake yi a fuska daidai saitin kunnuwa. Irin wannan tsaga ƙarama ce marar tsawo ƙwarai, tsawonta bai wuce daidai kunnuwa ba, wasu ana yi masu kalangu ɗaya-ɗaya wasu kuwa ana yi masu kalangai biyu-biyu a kowane ɓangare na fuska, wannan ya danganta da sha’awar wadda za a yi wa tsagar.
Abin kula a nan shi ne, wasu samari kansa wanzami ya yi masu tsagar kalangu ɗaya-ɗaya a kowace fuska domin sha’awa, ko kuma su ma ‘yan matansu kan bukace su da a yi masu kalangu ɗaya-ɗaya a kowace fuska.
Akwai kuma waɗanda ake yi wa tsagar kalangu ɗaya-ɗaya a fuska a matsayin tsagar gado. Misali, Fulani Dallazawa zuriyar Malam Ummarun Dallaje (wanda ya yi jihadin jaddada addinin Musulunci a ƙasar Katsina kuma Sarkin Katsina na farko daga zuri’ar Fulani) ana yi wa mazansu da matansu tsagar kalangu ɗaya-ɗaya a fuska a matsayin tsagar gado.
Tsagar ‘Yar Baka
Tsagar ‘yar baka tsaga ce ta kwalliya wadda ake yi wa ‘yan mata a kumatu ta haɗe da wutsiyar baki. Wannan tsaga gado ɗaya ce kuma ana yin ta caɓa-caɓa a kumatu. Wasu kan kira irin wannan tsaga da sunan cika baki. Wannan kuwa ya faru ne saboda yadda ake yin ta caɓa-caɓa ga kumatu. An fi yi wa ‘yan mata masu kaurin kumatu irin wannan tsaga don a ƙara rage kaurin kumatun.
Wannan bayani an ciro shi ne daga kundin bincike mai taken: SANA’AR WANZANCI DA SAUYE-SAUYEN ZAMANI JIYA DA YAU wanda BASHIR ALIYU SAFANA SALLAU WANDA AKA GABATAR A TSANGAYAR FASAHA DA ADDININ MUSULUNCI SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA JAMI’AR BAYERO, KANO, DOMIN CIKA WANI ƁANGARE NA SAMUN DIGIRI NA UKU (Ph.D) A FANNIN HAUSA
MAYU 2009/JUMADA ULA 1430
Edita@rumasau-kallamu