A baitukan yau na tsaya, Na fara zancen shiriya, Na tsara baiti ku biya, Na sanya zancen anbiya, Ku bi ni sala-sala.
- Na gode Allah a gaba,
- Salati sallam na zuba,
- Gurin Nabiyyi mai haiba,
- A gun Sa ba a giba,
- Sai dai ka koyo sallah.
- ———————-
- Ka gode Allah ɗan’uwa,
- Ya yo ka mai kyan ƙwalwa,
- Ya ba ka ilmu da yawa,
- Ya ba ka hikmar baiwa,
- Waninka ko sai ƙ
- ————————–
- Ka daina kallon kowa,
- Ni’im suna nan da yawa,
- Fa Rabbi ne mai kai wa,
- Gare ka dukkan bawa,
- Ka gode wannan falala.
- ————————-
- A yau na gane jama’a,
- Suna da kyawun ɗa’a,
- Fahimta ce ke bara’a,
- Ta kauce tsarin ɗa’a,
- Hakan ko babbar illa.
- ————————-
- Ka gane komai ka faɗa,
- Idan kana son hulɗa,
- Ana ɗaga shi a yaɗa,
- A ɓata zancen a haɗa,
- Domin a kushe falala.
- ———————-
- Idan ka ce an ƙi ka,
- Ka ƙara kallon kanka,
- Ka seta ƙalbin naka,
- Sannan ka kalli waninka,
- Akwai dalilai ƙanana
- ————————
- Ga shawara zan ba ka,
- Ka gyara harshen naka,
- Ka bar batun an ƙi ka,
- Da ni da kai mui harka,
- Haza ɗabi’armu Allah.
- —————————
- Ku duba zancen nan dai,
- Da kyau da kallon daidai,
- Ina ganin nai daidai,
- Ban kauce zancen sai dai,
- Ɗanbarno zo kai lela.
domin samun karanta cikakkiyar waƙar danna koren rubutu