Allah (SWT) ya fifita Manzonsa da kyan halitta, fiye da sauran bayinsa. Annabi Muhammad (S.AW) mutum ne madaidaicin halitta. Ba dogo ba, ba kuma gajere ba. Watau shi matsakaici ne.
Annabi Muhammad (S.A.W) fari ne mai surkawa da jaja-jaja. Watau ba fari gau ba. Allah ya halicce shi da fuska mai haske. Yadda fuskarsa take a tsakanin mutane, kai ka ce farin wata ne, irin yadda yake haskaka sauran halittu na duniya. Yana da yalwar goshi da karan hanci. Yana da gashin ido da na gira, masu duhu. Yana da tsagar baki mai ɗan tsayi, ba tsukakkiya ba. Haka nan yankan tsagar idanunsa su ma suna da ɗan tsayi.
Ƙwayar idanunsa fara ce tas, baƙin kuma baƙi suɗuk. Wuyansa yana da ɗan tsayi. Yana da wushirya a tsakanin haƙoransa na gaba. Gashin kan Annabi Muhammad (S.AW) baƙi ne wuluk, kuma mai tsayi. Wani lokacin, Idan ya bar shi, yakan kai iya kunnuwansa, daga bayansa.
Kuma yakan zuba a kan kafaɗunsa. Yana da gemanya mai duhu. Kuma yana barinta ta yi tsayi. A ƙarshen rayuwarsa ya yi furfura a kansa da gemanyarsa, wadda bata fi ƙidaya ba.
Annabi Muhammad (S.A.W) yana da faɗin ƙirji. Watau akwai faɗi a tsakanin kafaɗunsa. Cikinsa ba shi da tudu. Yana da gaɓoɓi watau ƙasusuwansa suna da girma. Akwai gashi daga tsakiyar ƙirjinsa zuwa cibiyarsa.
Akwai hatimin annabta a gefan kafaɗarsa ta hagu, daga baya. Yana da tsayin hannaye madaidaita. Tafukan hannayensa suna da ɗan tudu da taushi. Ba a ƙarmashe suke ba. Haka nan kasangalalinsa da tafukan ƙafafuwansa. Amma ba shi da nama a agararsa. Watau agararsa a motse take. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi.
Daga Is’haƙa ya ce:, na ji Barra’u yana cewa: “Manzon Allah (S.A.W) ya kasance ya fi kowa kyan halitta. Ba kuma gajere ba”. (muslim ne ya rawaito)
Daga Aliyu bin Abi Ɗalibin (RA), ya ce: “Annabi Muhammad (S.A.W) fari ne, mai cizawa da jaja-jaja” (Albani ne ya ruwaito a cikin Aljami’us Sahihu).
Daga Abdur Rahman ɗan Abdullahi ɗan Ka’bu (ya ce. “Abdullahi ɗan Ka’bu ya ce: “Na ji Ka’bu ɗan Maliku yana bayani game da (abin da ya faru sanda Allah ya karɓi tubansu na rashin zuwa masallaci), ya ce: Na yi sallama ga manzon Allah (S.A.W) alhali fuskarsa tana ƙyalƙyali saboda farin ciki ya kasance idan ya yi farin ciki sai fuskarsa ta yi haske, kai ka ce wani yanki ne na farin wata. Mun kasance muna gane haka game da shi “(Bukhari ne ya ruwaito).
Galibi ana sIffata fuskar Annabi Muhammad (S.A.W) da farin wata, saboda haske da walwala da fuskarsa takan yi (musamman) a yayin da yake cikin farin ciki. Wannan yana nufin cewa, kamar yadda farin wata yake a duniya, to haka Annabi yake a cikin mutane.
Amma a wannan Hadisin na Ka’abu bin Malik ya ware wani kashi ne na wata, domin yin ishara da goshin Annabi Muhammad (S.A.W), inda hasken ya fi bayyana, a sanda yake cikin farin ciki. Shi yasa ya keɓance shi da wani yanki na wata.
Daga Abu Is’hak ya ce: An tambayi Barra’u (RA), shin fuskar Annabi Muhammad (S.A.W) kamar (hasken) takobi take? Sai ya ce: “A’a”, kamar (hasken) wata take” (Bukhari ne ya ruwaito)
Daga Jabir ɗan Samuratu, ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya kasance mai faɗin baki, mai tsayin yankan idanu, Mai siraren maƙyangyama…” (Muslim ne ya ruwaito).