Yadda Ciwon Baki Yake (Mouth ulcers)

0
3

“Mouth ulcers” Ɗaya ne daga cikin ciwukan baki da a turance akan kirasa da canker sore (shankaso), Ƙaramin ciwo ne na kwailewar fata dake faruwa a cikin baki musamman a jikin leɓe ta ciki daga sama ko ƙasa, ko gefen leɓen daga hagu ko dama, wani lokacin kuma a ƙasan harshe. Yana da matuƙar zafi, zugi da raɗadi.

Asali yana farawa ne daga ƙanƙanin kumburi kafin ya kwaile ko a ga yayi ja, inda daga nan sai fari-fari da ja inda nan take yakan iya fara zafi sosai, musamman idan aka ci abinci mai zafi, yaji, zaƙi ko mai ɗaci.

Galibi girmansa ba ya wuce girman ƙwayar dawa ko ɗan abinda ba-a-rasa ba. Duk da yana hana sukuni amma lokuta da yawa yana warkewa da kansa cikin sati 1 zuwa 2.

ME KE HADDASA SHI

Wani lokacin akan rasa dalilinsa kai tsaye, amma a wasu garkuwar jikinsu ce ke cin kanta da kanta wato Autoimmune stomatitis wanda shi ke jawowa,  wanda za a ga har jini yake ya ƙi ya warke, ko ya warke bayan magani sai ya kuma dawowa, a ɗau shekaru ana fama, tunda Autoimmune ba shi da magani zuwa yanzu. Amma masu wancan nau’in ba su da yawa amma suna shan azaba.

Sai a sauran mutane;

1. Taune leɓe ko rauni a baki na daga abinda ke jawo shi, wanda wannan kuwa na nufin ko da ta hanyar taune leɓen ko harshe yayin cin abinci ko a mutane masu sanye da Braces na haƙora.

2. Sannan rayuwa cikin matsatsi, wahala da damuwa wato dai “stress” kowanne iri ciki har da na lokacin Haila a Mata wato “stress during menstruation” na jawo irin wannan sore ɗin saboda motsawar Hormones daga normal zuwa Higher concentrations.

3. Ƙarancin sinadaran bitamins da minirals musamman nau’in bitamin B12, iron, forlate da zinc, duk suna sanya mutum cikin hatsarin samun canker sore.

4. Ciye-ciye ko mu’amala da abubuwan da jikin mutum ba ya so wato Allergic wanda wannan hatta a makilin akwai wanda bakinsa baya son wani nau’i na ingredients dinsa, ko abinci irin su; Ayaba, lemon ɓawo, chocolate, coffee, strawberries, gyaɗa, da cheese.

5. Rashin samun isasshen bacci tare da gajiya wannan ma na ta’azzara matsalar.

6. Sannan wani lokacin hakan na iya zama dalilin wani ciwo da ake da shi a jika ko dalilin wani magani da mutum ke sha, kamar magungunan chemotherapy a masu cutar Cancer, HIV, Magungunan tarin T.B, magungunan cutar farfaɗiya ko Sara (epilepsy seizures)

7. Hakazalika shan taba sigari, wiwi ko SHISHA duk kan iya haddasa wannan yanayin, ko shan abu me zafi da ƙarancin tsaftar baki.

MAGANIN MATSALAR

1- Kamar yadda nace galibi yana warkewa da kansa, amma za ku iya: Riƙa wanke baki da ruwan gishiri sau 3 ko 4 a yini a riƙa kurkurawa ana wankewa musamman kafin kwanciya bacci.

2- Shafa maganin rage zugi; irin su benzocaine gel ko alpa-xylocaine gel, ko magungunan shafawa da ke kashe ƙwayoyin cuta irin su BONJELA GEL ko wanke baki da CHLORHEXIDINE MOUTH WASH maimakon ruwan gishirin. Duk ana Saida su a manyan pharmacy store.

3- Sai kiyaye cin abinci mai yaji, mai zafi ko mai zaƙi sosai.

4- Sai kuma a riƙa shan ruwa sosai.

IDAN DUK BAYAN WANNAN AKA GA YA CIGABA:

Ta hanyar ganin yana ƙara a girma sosai, ko yana ciwo matuƙa wataƙila har da jini, ko bai warke cikin sati biyu ba, ko yana yawan dawowa bayan ya warke. To yana da kyau a zo a ga likita ko likitan haƙori don a duba ko akwai wata matsala ta cikin jiki da ke jawo hakan walau ƙarancin waɗancan vitamins ɗin, Autoimmune ko wasu cuttukan na ciki domin ulcer ma iya jawowa idan duodenal ce tunda jiki ba ya amfana da iron ɗin da ake samu idan akwai ta. Da fatan an ilmantu.

Karanta Zubar Da Ruwa A Farko Da Kuma Ƙarshen Juna Biyu

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceZikiri In An Zauna A Wani Majalisi