Idan mutum na fama da atini yakan rasa samun sukuni, sannan a kodayaushe ya kan ji kamar kashi ya matse shi sosai tare da jin kamar zai yi shi a wando, amma kuma yana zuwa banɗaki sai ya ji ya kasa yin kashin ko ya yi ɗan kaɗan!!
Idan ya kasance kana fama da wannan matsalar ko ka taɓa yin ta a baya, daure ka karanta wannan gajeren rubutun domin sanin abin da ke kawo maka wannan matsala.
ABUBUWAN DA KE KAWO ATINI:
- Kumburin magudanar Kashi (rectal inflammation): Rectal inflammation kan sa mutum atini sosai, bayan atini waɗansu daga cikin Alamominsa sun ƙunshi kashin jini da majina.
2. Basir (Haemorrhoids): Basir Yana daga cikin abinda kan sa mutum atini sosai, musamman kafin ya yi tsiro, wani sa’in Kuma yakan sa mutum kashi mai tauri (constipation), kashin jini da sauransu.
3. Infectious dysentery ko ɓacewar ciki: A lokacin da cikin mutum ya ɓaci bayan cin wani abu, mutum zai ta atini sosai sannan ya kasa sukuni a waje ɗaya.
- Kansar magudanar kashi (Rectal tumour): Duk mutumin da ke fama da rectal cancer kan zo da kashin jini, kashi mai tauri(constipation) bayan atini.
- Pelvic Inflammatory diseases (sanyin Mata): Alamomin PID sun haɗa da ciwon mara, ƙaiƙayin gaba tare da fitar da wani irin ruwa mai wari daga gaban mace (vaginal discharge,) haɗe da zazzaɓi wani sa’in. Wani lokacin yakan haɗu da sanyin mafitsara, hakan zai sa ki yawan fitsari da rana ko yawan tashi da daddare (sau uku zuwa huɗu) domin yin fitsari, zafi yayin fitsari (dysuria), ganin jini a fitsari (haematuria) da sauransu.
- Kansar babban hanji (Tumour of descending colon): Alamominta sun ƙunshi atini, gudawa ko kashi mai tauri bayan rama da waɗansu alamomi na cutar kansa.
- Ulcerative colitis: Ulcerative colitis na daya daga cikin cututtukan da kansa kumburin Hanji. A lokacin da hanji ya kumbura mutum zai ta fama da atini da gudawa mai ɗauke da majina da jini wani sa’in.
ME YA KAMATA MUTUM YA YI?
Duk mutumin da ke fama da wannan ya kamata dai ya je asibiti domin masana abun su yi cikakken bincike a kan abin da ke janyo masa wannan matsalar. Binciken da masana za su iya yi maka a asibiti: likita zai iya saka yin waɗannan binkicen:
- Proctoscopy or sigmoidoscopy
2. Ko rectal biopsy a lokacin da likita ke zargin kansar magudanar kashi
3. Coloniscopy with biopsy and Barium enema a lokacin da likita ke zargin alamomin colon cancer
4.High vaginal swab (HVS), Abdominal Ultrasound Scan (USS) a lokacin da likita ke zargin sanyin Mara wato PID.
MAGANIN DA LIKITA ZAI MAKA A ASIBITI:
Maganin da likita zai maka ya danganta da abin da bincikensa ya gano:
- Idan yakasance Infectious dysentery ne, likita zai ba ka Analgesia domin rage raɗaɗi, zai iya saka maka ruwa (iv fluids) tare Antibiotics Wanda ya danganta me abun da test ɗin stool mcs ya nuna.
- Idan Rectal inflammation ne likita zai iya ɗora ka a kan magunguna kamar steroid suppositories ko 5-ASA enemas, sannan zai iya ƙara makaa ruwa (fluids IV ) idan ka kasance ka yi amai sosai, likita zai ba ka antibiotics saboda infection.
- Idan mutun na fama da PID ne toh likita zai iya ba ka waɗannan magungunan kamar analgesia domin rage raɗaɗin zafin. Ruwa (fluids IV) a lokacin da ya ga jikinka na buƙata empirical antibiotics.
- Haemorrhoids (Basir) likita zai ba ka magunguna sannan zai ce ka dinga yin Sits bath (wato Zama cikin ruwan gishiri) ko kuma idan ya yi tsauri sosai ya yi maka aikin da ake kira Haemorrhoidectomy.
- Idan ya kasance Rectal tumors ne ko colonic tumors toh likita zai iya buƙatar yi maka aiki ko ɗora a kan magungunan kansa. (cytotoxic drugs) ko ya yi maka radiation therapy.
Daga Cikin bayanan da na yi za a ga na ɗan yi bayani a kan magani na yi hakkan ne kasancewar akwai ɗalibai ‘yan uwana. Allah Ubangiji ya ba mu Lapia da zaman lapia Amin ya rabb
Danna nan don karanta Yadda Zubar Jini Yake Bayan Haihuwa
Edita@rumasau-kallamu










