Potato Balls abinci ne wanda a Hausance ake kiran sa da Ƙwallon dankali, wanda ake yin sa da dankalin Turawa. Yana da matuƙar daɗi musamman ma idan a karin kumallo za a ci shi.
Abubuwan da ake buƙata
- Dankalin Turawa (irish)
- Taruhu
- Albasa
- Kayan Ɗanɗano
- Man gyaɗa
- Ƙwai
- Fulawa
Yadda ake haɗawa
- Farko za a dafa dankali, har ya dahu sai a bari ya huce sannan a yi mashing ɗin shi, a kwashe.
- A daka taruhu da albasa a zuba, a saka spices da seasoning.
- A saka lawashi, sai a juya ko’ina ya haɗe. A dinga ɗiban wannan mixture ana yinsa kamar ƙwallo a hannun ana ajiyewa.
- Sannan a barbaɗa masa fulawa. Za a kaɗa ƙwai, a sa masa gishiri, a ɗaura tukunya, a zuba mai.
- Idan ya yi zafi, a na ɗauko wannan haɗin da aka mulmula kamar ball, a sa cikin mai, ana soyawa.
A ci daɗi lafiya.
Domin sanin yadda ake cabbege sauce danna nan