Abubuwan haɗawa
- Albasa
- Koren tattasai
- Taruhu
- Tattasai
- Kayan ƙamshi
- Maggi
- Kwakwamba (cucumber)
- Butter ko man gyaɗa
Yadda ake haɗawa
- Ki ɗauko albasa ki gyara, ki yanka ta ƙanana, sai ki wanke ki tsane shi a matsami. A ajiye a gefe, a ɗauko koren tattasai ki yanka, shi ma ajiye a gefe. A ɗauko taruhu, ki yanka ƙanana, a ajiye a gefe.
- Ki ɗaura non stick pan a kan wuta, ki sa butter, ki yanka albasarki, ki soya sama-sama; Sai ki ɗauko taruhu, ki sa ki soya sama-sama shi ma, sai ki ɗauko kayan ƙamshi ki sa, maggi (iya ɗanɗanon da zai miki). Sai ki ɗauko yankakken albasa (dama kin yanka ta da ɗan dama) ki sa.
- A nan, sai ki sa ruwan ɗumi kamar cokali 4 (tbsp) ki rufe na ɗan wani lokaci, har sai ruwan ya ragu.
Sannan ki ɗauko koren tattasai da cucumber ki sa ki rufe, na ɗan wani lokaci har sai ruwan ya shanye sai ki sauke ki zuba a plate.
Ku karanta Yadda Ake Vegetable Macaroni