Barkanmu da sake kasancewa acikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tareda bayani akan lafiyarsu cikin harshen hausa a saukake tare dani Hafsat Shettimah. A yau zamu koyar da yadda ake yin lemun gyada, shinkafa da dankalin hausa (groundnut, rice, sweet potato shake) ku biyoni a sannu domin mu koya tare……
Ko kun san:- Gyaɗa na da sinadarin minerals kamar su copper, manganese, potassium, calcium, iron, magnesium, zinc da kuma selenium wanda suke ƙara ƙarfin ƙashi da haƙori.
Abubuwan Buƙata
-
Shinkafa ½ rabin kofi
-
Gyaɗa ½ rabin kofi
-
Dankalin hausa
-
Gyaɗa soyayyiya
-
Siga
-
Madara
Yadda ake haɗawa
-
A wanke shinkafa a jiƙata sai tayi laushi
-
A fere dankalin hausa a yayyanka
-
A soya gyaɗa a busar da ita
-
Sai a hade gyaɗa, dankali da kuma jikakkiyar shinkafa a markada a tace da abun tata
-
A raba ruwan gyaɗa biyu da a ɗora a wuta har sai yayi kauri (kamar kunun gyaɗa). Sai a sauke a hade da ragowar ruwan gyaɗar a saka madara da siga. Za’a iya ƙara ruwa dai dai ƙaurin da ake so.
-
Za’a iya tace shi da rariya idan yayi gudaje saisaka a fridge yayi sanyi.
-
Asha lafiya