Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abinci, namu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake yin hallaka ƙwabo ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……
Hallaka kwabo nau’in alawa ce da ake yi da gyaɗa wadda za a iya ajiyewa domin ba wa yara.
Abubuwan Buƙata
- Gyada mai kyau
- Sugar
- Lemon tsami (a matse ruwan)
Yadda ake haɗawa
- A daddaka gyaɗa, amma ba sosai ba
- Cikin tukunya mai tsafta a zuba ruwa, sugar da lemon tsami, a bar shi ya dahu na mintuna 18-20
- A zuba gyaɗa, a ci gaba da juyawa sai ya yi brown sosai
- A shafa mai a farantin silver sai a juye wannan hallaka kwabo a kai, a baza shi sosai
- Sai a yayyanka shi zuwa desired shapes
Domin koyon Yadda Ake Biskit din Gyaɗa (groundnut cookies) danna nan