KAYAN HAƊI
- Nama
- Kori
- Tafarnuwa
- Sinadarin ɗanɗano
- Gishiri
- Albasa
- Ba’adonise
- Thyme
- Ganyan Ayayo
Yadda za a haɗa
Da farko a tafasa nama da albasa da thyme, idan ya tafasa kuma ya dahu sai a yanka ayayo ƙanana a daka shi a zuba sinadarin ɗandano da gishiri a kan romon da aka tafasa.
Sai a ɓare tafarnuwa a daka da ba’adonise a soya, a zuba a cikin miyar ayayon ana zubawa sai a rufe a kashe wutar, kar a bar shi ya yi kauri, kar kuma ya yi ruwa. A ci da biredin Larabawa ko shinkafa ko abin da kike so.