Sabulun wanki shi ne sabulun da ake wanke tufafi, domin cire dauɗa da warin da yake a jikin tufafi. Yadda ake sabulun wanki ya haɗa da:
Abubuwan Da Ake Buƙata
Sinadiran Haɗawa Adadi
- Caustic soda (Na OH) 1 kg
- Palm Kernel Oil ( P.K.O ) 6 ltrs
- Soda ash ( light ) 0.25 kg
- Silicate 0.25 kg
- Sodium sulphate 3 kg
- Kala(colour) Daidai Misali
- Ruwa 4.5 ltrs
- Sinadarin Ƙamshi Daidai Misali
- Sinadarin Saka Kumfa 250
Yadda Ake Haɗawa:
- A narkar da 1kg na caustic-soda a cikin 4.5ltrs na ruwa, nauyinsa ya kasance ya kai 1275kg/m3. A bar haɗin ya yi kwana uku domin ya narke da kyau. A tabbatar ya yi wannan kwanakin domin samun nagartarsa, kuma domin gujewa samun matsala a fata, ko a kan kaya.
- A zuba soda-ash ɗin a cikin wannan caustic-soda ɗin da aka dama aka bar shi ya yi kwanaki, sannan a yi ta motsa damun har sai ya yi yadda ake buƙata, wato ya damu da kyau.
- A ɗauko wannan launin (colour), shi ma a zuba a cikin haɗin, a ci gaba da damawa.
- A ɗauko duka (P.K.O) wato palm kennel oil a juye a cikin haɗin a juya ko na ce damawa ba tare da an mayar da hannu baya ba, kar ayi gaba ai baya nake nufi.
- A ɗakko sinadarin saka kumfa, tare da silicate a zuba su a ciki a cigaba da motsawa.
- A ɗakko sinadarin ƙamshi (wato turare) a zuba a cikin haɗin. Sannan a zuba shi a cikin gwangwanayen sabulan, sai a bar shi na tsawan awa ashirin da huɗu(kwana ɗaya) domin ya haɗe jikinsa,don ya yi ƙarfi.
- Bayan awa ashirin da huɗu ɗin nan kuma, sai a yi tambari a kai, a yi masa fasali irin yadda ake so, sannan a yi fakejin su. Daga nan kuma sabulu ya kammala.
Gargaɗi:
- A saka a rai cewa akwai sabulai kaloli kuma iri daban-daban a kasuwanni, amma haɗin nan da za a yi, zai zama haɗi ne da za a iya shiga kowace irin gasa ba tare da fargaba a rai ba.
- Wajen wannan haɗin a tabbata an yi amfani da turaren haɗin sabulu mai ƙamshi domin jan hankalin masu saya. Turare mai daɗi sirri ne sosai, wajen ɗaukar hankalin masu saye.
- A yi Amfani da kala mai kyau wajen haɗin, domin samun ingantaccen sabulu. bayan an kammala haɗin. Yin hakan zai taimaka wajen samun nasara a cikin abin da aka haɗa.
Domin karata yadda ake sabulun wanka dannan koren rubutun nan.