Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe tare da ni Hafsat Shettimah. A yau zamu koyar da yadda ake yin groundnut, sweet potato pie, ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……
Ko kun san dankalin Hausa na ɗauke da sinadarin vitamin B,C,E da vitamin K wanda yake yaƙi da kwayoyin cuta a jikinmu.
Abubuwan Buƙata
Yadda za a haɗa pie yadda za a yi Fillings
fulawa kofi 2 Dankalin Hausa guda ɗaya.
Baking powder babban cokali ɗaya Gyaɗa ½ kofi
Man gyada Albasa
Gishiri ½ ƙaramin cokali Attaruhu 2 matsaƙaita
Ƙwai guda ƙaya (na shafawa kafin gashi) Tafarnuwa 1
Man suya Sinadarin ɗanɗano guda1
Thyme ½ rabin ƙaramin cokali
Fulawa 2 cokali babba iyu
Kori curry½ ƙaramin cokali
Yadda ake haɗawa
A cikin tukunya a zuba gyaɗa a dafa ta dahu da kyau, idan ta dahu sai a saka dankali, idan ya dahu, sai a tace su, a ajiye a gefe
Cikin tukunya mara zurfi a zuba mai chokali biyu, a zuba albasa, a ɗan ba ta tsoro, sai a zuba attarahu tare da tafarnuwa da sinadarin ɗanddano, thyme da kori(curry) a juya na minti 1-2
A zuba dankali da gyaɗa a ɗan juya
A cikin ƙaramin kofi, a haɗa fulawa da ruwa ,sai a zuba cikin wannan haɗin dankali da gyaɗa dake wuta, sai a bar shi ya ɗan hade na minti biyu kafin a kashe wuta.
Yadda zamu haɗa pie ɗinmu
A murza fulawa da man gyaɗa sosai, sai a zuba ruwa da gishiri a murza, ya murzu da kyau, sai rufe shi na minti 5-7 domin ya haɗe da kyau
Bayan wannan mintuna, sai a sake murza shi, sannan a yi rolling a sami meat pie cutter, in babu a sami ɗan roba ko kofi mai ɗan girma, sai a ringa yanka fulawa da shi circle-circle
A zuba wanna hadin gyaɗa da dankali a tsakiya, sai a shafa ruwan fulawa a gefe sannan rufe, a danna cokali mai yatsu
A shafawa pie din ruwan ƙwai
A gasa na minti 30 ko sama ko kuma idan ya yi ruwan ƙasa wato golden brown.