Barkan mu da kasancewa a fannin girke girkenmu na WikiHausa, za mu koyi yadda ake Fanke (puff-puff) tare da ni Hafsat Shettima.
Abubuwan haɗawa
- Fulawa kofi 1
- Sugar 1/3 kofi
- Salt pinch
- Yeast chokali 1 teaspoon
- Mai (na suya)
Yadda ake haɗawa
-
- A cikin roba mai zurfi, a zuba flour da yeast da sugar da ruwan ɗumi, ki kwaɓa ya kwaɓu sosai, ya yi ruwa-ruwa amma ba sosai ba, sai a rufe a wuri mai ɗumi.
- Ya sami kamar awa 1, idan ya yi, za ki ga ya tashi, sai ki ƙara buga shi.
- Sai a ɗora kasko a wuta, a sa mai ya yi zafi. sai a rinƙa ɗiban ƙullin da chokali ana sawa a cikin mai.
- A soyawa kuwa, ya yi jar suya.
Domin koyan Yadda ake bread-egg toast a sauƙake danna koren rubutun nan.