Yadda Ake Amfani Da Status Saver Na Whatsapp

0
533

Yadda Ake Horon Masu Yi Maka Flashing A Waya.

Mafi yawancin mutane suna yawan tambaya ta cewar sun ga abu a status na wani ya sanya a whatsapp, kuma suna da buƙata, amma ba yadda za su yi, gashi kuma suna so, har a wasu lokuta sukan nemi da wanda ya sanya wannan status da ya turo masu amma ya ƙi , to ta wannan Manhaja (Application) za ka iya amfani da shi wajen ɗaukar dukkanin wani nau’in abu da wani ya sanya a status na shi ba tare da ka buƙaci ya turo maka ba.

Yadda masarrafin yake kuwa shi ne, ka shiga kasuwar hada-hadar masarrafai ta duniya wato Google Play Store ka nemi Status Saver, sai ka sauke shi a kan wayarka, sai ka sanya shi, ma’ana ka yi Installing na shi, da zarar ka yi, sai ka buɗe shi, zai ba ka dama ganin ɓangare guda biyu, na farko images, ma’ana hotuna da kuma Videos wato hoto mai motsi, anan ne za ka ga wajen images ya buɗe maka hotuna daban-daban, duk wanda kake da buƙatar ɗauka sai ka danne kan hoton, zai ba ka alamar memory card daga sama inda da zarar ka danna kansa shi kenan, sai ka je ka duba Gallery naka, za ka ga hoton a ciki, haka kuma wannan hanyar ake amfani da ita wajen ɗaukar video ma, idan kuma za ka ɗauke su ne duka, sai ka riƙa hawa kan hoton ko video kana zaɓa da zarar ka gama sai ka zaɓi memory card, zai nuna maka sun zauna a kai.

Sannan idan ba so kake ka ajiye ba, akwai inda zai ba ka damar ka yi sharing a duk inda kake so, domin tura wa wani ko da kuwa kai ba ka ajiye shi a kan waya ko computer naka ba. Haka kuma akwai inda zai ba ka damar ka zaɓe su duka ta hanayar zaɓen guda ɗaya, sai wannan alamar ta fito, da zarar ka danna zai nuna ka zaɓe su duka, sai ka ajiye. Idan kuma gogewa za a yi, akwai alamar gogewa sai ka danna kan alamar zai zama ka goge hotunan ko video duka daga kan STATUS SAVER ɗin .

Yadda Ake Amfani Da Shi A Taƙaice

1. Ka zabi irin nau’in status da kake son ɗaukar hoto ko bidiyo.
2. Sai ka dannan kan alamar saving domin ajewa.
3. Da zarar ka aje, sai ka je cikin gallery ka duba.
4. Za ka iya ajiye duka hotunan ko bidiyon ta hanyar zaɓar hotunan duka.

Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Komfiyuta (Computer) danna nan.

labarin da ya wuceHukunce-Hukuncen Jinin Cuta
Labarin na GabaYadda Ake Amfani Da Kafar Sadarwa Ta Whatsapp
Engr. Suleiman Musa Abdullahi
Dalibi daga Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria Wanda na karancin bangaren addinin musulunci da koyar dashi a matakin farko, sannan na canja zuwa ga karatun fasahar sadarwar zamani Inda na halarci kasashe daban-daban India,Ghana, Africa ta kudu da Uganda domin samun horo da ha66aka karewa ta a bangarororin fasahar sadarwar da dangogin ta, ciki harda bada tsaro ga bayanai da binciken kwafkwaf da Na'ura domin bincikar masu laifi don samun hujjar gabatarwa a gaban kotu.