Ya Ake Sanin Kai?

0
93

Kamar yadda na sha faɗa a rubuce-rubuce na, mutum haɗin gambiza ne na ƙwayar halittarsa, tarbiyyar da ya samu daga gida, iliminsa, abokanansa, wurin da ya tashi da gogewarsa a rayuwa.

Su waɗannan abubuwan su suke sa wa mutum ƙauna ko ƙin wani abu, su suke taimakawa mutum wajen yanke shawara, su suke taimakon mutum kan zaɓinsa da ayyukansa, su suke haskawa mutum abubuwan da zai iya yi cikin sauƙi da waɗanda sai ya wahala.

Wanda yake son ya san kansa yana da kyau ya fara daga ƙwayar halittarsa, domin ita take zuwa da duk wasu halayensa da ya gada a wurin iyayensa da kakanninsa. Don haka ni ma zan fara da shi, ina mai cirowa daga litattafan masana a wannan fanin.

❖ Ka San Yanayinka Na Halitta

Shi yanayin mutum shi ne halayen da aka haife shi da su, waɗanda ya gada daga iyaye da kakanninsa. Kafin ya shiga duniya ya koyi wasu dabarun. Tim Lahaye (marubucin littafin why you act the way you do) ya kasafta mutane zuwa gida huɗu (4).

Bibbiyu, biyun farko su ne mutane masu surutu da hayaniya (extroverts) sauran biyun kuma su ne shiru-shiru waɗanda ba su cika shiga mutane ba (introverts). Zan kawo dukkanin kashi huɗun haɗi da rauni da ƙarfin kowanne, ina mai cirowa daga wannan littafin.

SANGUINE

A ɓangaren masu surutu akwai waɗanda ake kira “Sanguine”, waɗannan su ne irin mutane masu yoyon magana ɗin nan, ba sa iya riƙe bakinsu, duk inda suka shiga dole sai an san suna wurin, akwai su da haba-haba da mutane, ga su kuma ba wuyar sabo, ga saurin ƙulla abota. Ba su san jimami ba, kuma komai suna iya mayar da shi raha, sun yarda da tatsuniyar dawwama cikin farin ciki a rayuwa.

Ƙarfinsu: suna da saurin sabo, sun iya ba da labari, ba sa gajiya da surutu, suna rayuwa a yanzu (tuna baya ba ya damunsu balle fargabar gaba), suna da nuna tausayawa da alhini kan abu marar daɗi na wani, suna nuna shauƙi kan komai, ga su da raha da kuma shiga cikin ayyukan sa kai dumu-dumu, saurin ƙulla abota, da fara magana in kun haɗu.

Rauninsu: ba sa iya tursasa kansu su yi abin da ya dace, in ka ba su aiki da wuya ka ga sakamako yadda ya kamata, yanayinsu yana saurin canjawa daga walwala zuwa tausayawa, in ka shiga wani hali sai sun fi ka nuna jimami don haka ma ana iya zargin ko na ƙarya ne in ba a fahimce su da kyau ba, ba su da tsari, sun fi sauran nau’in mutanen girman kai, kuma cikin sauƙi suke samun kansu cikin yaudara, ƙarya da cutar mutane don su ɓoye rauninsu, sannan suna da ƙarawa komai gishiri (kambaba abubuwa).

CHOLERIC

Nau’i na biyu cikin masu surutu su ne “Choleric”, shi choleric bai kai Sanguine surutu ba, shi ma yana da saurin sabo da jama’a, shi ma’aikaci ne, yana da zummar cimmawa ko azama, yana zama jagora, yanke abin da zai yi ba ya masa wahala, haka ma yanke wa waninsa, yana wadatuwa da kansa, yana da buruka kuma yana tsara yadda zai cimma su.

Ƙarfinsa: ƙarfin gwiwa, wadatuwa da kai, hangen nesa, duk abin da ya sa a gaba ana ganin ci gaba (progress), yanke shawara ba ya ba shi wahala, jagora ne, akwai shi da naci, ba ya jira, in ma ba ku yi ba zai yi da kansa.

Rauninsa: ba ya nuna ƙawa zuci/motsin rai (emotion) dan haka bai cika nuna tausayi ba, yana ganin komai zai iya yi da kansa ko ba taimako, yana danne na ƙasa da shi da musu kama-karya, ya iya ƙeta, bai cika yafiya ba, yana da saurin fusata dan haka ma yake yawan faɗa da mutane, kuma ya iya cin fuska da baƙar magana, tunzura mutum ma yakan iya sa shi nishaɗi.

MELONCHOLY

Nau’i na gaba wanda shi ne na farko cikin mutane shiru-shiru shi ne meloncholy, waɗannan su ne irin mutane ma su basira ɗin nan, wanda kowa yake mamakin baiwarsu, akwai su da lissafi, sadaukar da kai, da son ganin komai ya cika ɗari bisa ɗari 100%. Ba su da saurin ƙulla abota amma in suka ƙulla abota da kai ba za su ci amanarka ba, yanayinsu yana saurin canzawa dan haka sun fi duk sauran saurin shiga damuwa.

Duk da ba su da surutu amma in suka samu wuri za ka rantse ba su ba ne (ko da kuwa a gaban kyamara ne ko wurin wani taro). Akwai su da tattali da rowa, in an ɓata musu
rai suna da fushi amma ba kamar choleric ba, su a zuci za su cigaba da tafarfasa dan haka suna iya ɗaukar fansa ma.

Ƙarfinsu: ‘ƴan baiwa ne, akwai su da basira, suna da lissafi, suna son ƙyaleƙyale, suna iya tursasa kansu su yi abin da ya dace, suna da zurfin tunani da tsari, ba su cika son hayaniya ba, kaɗaici yana ba su damar zurfafa tunani, ba su cika yin raha ba saboda komai gaske ne a wurinsu(da muhimmanci suke ɗaukarsa), suna da baiwar ƙirƙira da bincike, duk aikin da suka sa a gaba sai sun ga ƙarshensa, sun fi sadaukar da kansu kan abin da mutane za su amfana ko da su suna cutuwa.

Rauninsu: saboda zurfin tunaninsu cikas suke fara hangowa game da komai da za su yi, caccanzawar yanayinsu ya sa suna saurin shiga da kuma daɗewa a damuwa, saboda suna son yin komai ɗari bisa ɗari (100%) ya sa ba a cika burge su ba, su da kansu ma suna barin ayyukan da suka ga ba za su cika yadda suke so ba, ba sa shiga mutane, suna kallon rayuwa a yadda ya kamata a rayu ba a yadda take a zahiri ba, basirarsu ta sa suna da saurin zargi da munanan tunani kan abubuwa, suna da saurin kushe abu
tare da caccakar abin da bai kai mizani ba a ma’auninsu.

PLEGMATIC

Kaso na ƙarshe su ne plegmatic, su waɗannan shiru-shirunsu har ya fi na meloncholy domin ba wani shauƙi da za su samu kan su a ciki da zai sa su zama ma su surutu. Da wuya ka ga sun yi fushi ko an ɓata musu rai, suna da mugun sauƙin kai don haka sun fi sauran daɗin zama, suna da kakaci amma ba su cika dariya ba ko da sun yi kakacin, ba sa wuce iya abin da aka sa su, ba su cika son ɗaukar nauyin komai ba, sun fi jiran rayuwa ta zo ta same su.

Ƙarfinsu: nutsuwa da rashin hayaniya, suna da sauƙin kai da daɗin sha’ani, za ka iya dogara da su, sun iya sasanta mutane, suna da tsari, akwai su da kakaci, suna kallon rayuwa a zahiri, ba sa yin abu ba tare da tunani da kuma kyakkyawan tsari ba, ba sa fara aiki da kansu amma in dai an sa su sai sun kammala shi, suna da son tsafta, ba su cika shiga sha’anin mulki ba, amma duk lokacin da aka zaƙulo su aka ba su mulki, suna yin mulki da ƙwarewa ta ban mamaki.

Rauninsu: ba sa iya zaburar da kansu, suna da ganda, suna da son kansu, akwai su da rowa da tsoro, suna da yawan damuwa da zullumi kan abubuwa (gujewa ɗaukar nauyi yana farautarsu), ba sa iya saurin yanke mai za su yi balle su yanke wa wani, kullum cikin ƙoƙarin kare kansu suke daga cutuwa ko asara dan haka da wuya su ɗauki kasada, suna da turjiya da tawaye, za ka iya musu bayanin mai kake son su maka, su yi kamar sun yarda amma da sun juya baya su yi a yadda suke so.

Tim Lahaye bai tsaya a iya kasa mutane gida huɗu ba, ya ƙara bayani da cewa kowanne mutum haɗin gambiza ne na kashi biyu cikin huɗun, kowa ya haɗa ɓangare biyu amma ɓangare ɗaya yana iya fin rinjaye, akan samu ma su haɗa uku amma su suka fi ƙaranci, dan haka yace mutane za su iya kasuwa gida goma sha biyu (12).

A taƙaice dai kai tsaye mutum ba zai iya gane wanne yafi rinjaye a tattare da shi ba, amma daga bayanan da suka gabata zai fuskanci inda ya fi karkata in ya zauna ya nazarci rayuwarsa. Abu na gaba da zan ƙara shi ne, su waɗannan ɗabi’u na halitta koyaushe suna tare da mutum har ƙarshen rayuwarsa domin gadonsu ya yi, amma
iliminsa, tarbiyyarsa, imaninsa da aƙidunsa su suke mayar da shi mutum.

Dan haka yana daga cikin amfanin gane ƙarfi da rauni na halitta mutum zai san ina zai karkata a rayuwa, sannan zai san waɗanne halayya ne zai zama a ankare da su dan kar su dinga ɓata masa hulɗa da jama’a. Misali, sanguine dole ya yi aiki a kan rashin iya sauraren mutane, ya koyi kama bakinsa ya ji suma me za su ce, choleric dole ya koyi dena yin ƙarfaƙarfa da danne na ƙasa da shi, saboda wannan zai sa su daina ganinsa da
ƙima.

Meloncholy dole ya koyawa kansa kyakkyawan tunani kan abubuwa, in ba haka ba basirar ta sa ba za ta masa amfani ba, phlegmatic sai ya koyi zaburar da kansa ko zama wurin da za a dinga yawan zaburar da shi in ba haka ba zai tsinana komai ba a rayuwarsa. Wannan raba mutane da Tim Lahaye ya yi ba lallai ya zama cif-da cif ɗari
bisa ɗari (100%) ba amma a cikin duk rabe-raben da ake yi ana ganin cewa wannan na san ya fi tattara kowa da kowa.

Manzon Allah tsira da aminci su tabbata gare shi ya ce “ Allah ya halicci Annabi Adamu daga wata damƙa da ya yi daga ƙasa (a wurare mabambanta), don haka ‘ƴan’adam an halicce su a gwargwadon haɗe-haɗen ƙasar. Sai ya zamto a cikin mutane akwai ja, akwai fari, akwai baƙi akwai kuma tsaka-tsakin dukkaninsu, akwai mai kyan hali, akwai mai munin hali, akwai mai sauƙin lamari, akwai mai wahalar sha’ani” (Abu dawud da Tirmizi, kuma sun ce hadisi ne kyakkayawa).

Akwai wani jan hankali, ko da ka ga halin wani da ka sani kada ka yi gangancin faɗa masa ko da kuwa abokinka ne, domin in ya ga raunin irin wannan mutumin ba zai yafe maka, kuma da wahala ka iya gamsar da shi cewa ba iya bayanin ba kenan, dan haka gara ka bar shi ya gano da kansa in yana da buƙata, sai a kula.

❖ Ta Ya Zan Gano Kaina Daga Wannan Rabe-raben?

Kusan komai da muke yi ya dogara ne da irin tunanin da muke yi, shi kuma tunani ba komai ba ne face tambaya da amsa, tambaya ce kake yi wa kanka a zuci kuma kake amsa ta da kanka a matsayin tunani, don haka yana da kyau ka dinga yi wa kanka tambayoyi ma su kyau.

Da farko abin da za ka fara tambayar kanka shi ne, ina cikin ma su surutu ko ba na ciki? Idan ka san kana da yawan zuba a ko ina to kana cikin ma su surutu kenan dan haka za ka zama kana tsakanin Sanguine da Chloric. Daga nan sai ka sake tambayar kanka wanne irin surutu ne da ni? Ina hana sauran mutane magana saboda surutuna ko kuwa ina ɗan sararawa su ma su yi? Ina da tausayi in ana ba da labari ko wani ya shiga wani hali ko kuwa ba ruwa na? ina da son girma da nuna iko ko kuwa?

Idan amsarka ta zama e a tambayoyi biyun farko, ta zama a a, a tambaya ta uku akwai yiwuwar ka zama sanguine, saɓanin haka kuma choleric. Idan dukka e ne ko dukka a a kuma wataƙila kai gamayyar biyun ne. Idan kuwa ɓangaren shiru-shiru kake za ka iya farawa da tambayar kanka ko kana son komai ya zama ɗari-bisa-ɗari? Ka iya lissafi? Kana da zurfin ciki da kawaici? Kana nuna halin ko in kula a kan komai?

Tambayoyi biyun farko ɗabi’un Melancholy ne, biyun ƙarshe na Phlegmatic, idan e ne amsarka a kashin farko a a a kashi na biyu ka zama Melancholy kenan, saɓanin haka kuwa Phlegmatic. A lura, kamar yadda na faɗa a baya, za ka iya samu amsoshinka duk su zama e ko duk a a, wannan alama ce da ke nuna duk ka haɗa bangarori biyun.

Ta yiwu kuma ka ga wasu halayenka sun faɗo a gidan ma su surutu, wasu kuma a gidan marasa surutu, in haka ta faru sai ka sake duba sauran abubuwan da suka gabata a bayanin rauni da ƙarfi dan ka ga inda kafi karkata. Bayan ka gano gidan da ka faɗa a wannan kashe-kashen sai kuma ka amsa waɗannan tambayoyin da za su zo a babi na gaba.

Wanan bayanin an ciro shi ne daga littafi mai taken Ka San Kanka wanda AHMAD SANI ya wallafa.

Karanta Amfanin Sanin Kai

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceAmfanin Sanin Kai
Labarin na GabaYadda Za Ka Tambayi Kanka Da Kanka
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.